LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 36*

Lokacin da Gid'ad'o ya fahimci cewar Zainab ta fara zuwa school nan take yaji hankalinsa yayi k'ololuwar tashi tsananin tsoro ne ya d'arsu azuciyarsa domin yana gudun ayi masa k'wacen budurwa.
asanadiyyar haka yaje har wurin mahaifinsa Yunusa alokacin da suna zaune shida Inna Lantana ya russuna k'asa ya gaishesu kamar yaron kirki, amsa mashi sukayi cikin sakin fuska da tsantsar k'aunar d'ansu shiru ne ya biyo baya domin Gid'ad'o ya kasa fad'awa iyayensa abinda ke tafe dashi su kuma kallonsa kawai sukeyi suna jiran suji abinda zai fito abakinsa.

Ganin ya kasa cewa uffan yasa baba Yunusa yace"Gid'ad'o lafiya kazo kayi mana zaune k'erere..!?".

Gid'ad'o yace"baba dama wata magana ce nakeson in fad'a muku..".

"a'aaaa fad'i mana Gid'ad'o idan baka sanar mana damuwarka ba amatsayinmu na iyayenka waye kakedashi da zaka fad'awa...!?".

Gwauron numfashi Gid'ad'o ya sauke yace"dama akan maganar Zainabu ce baba na dad'e ina sonta tuntuni kafin ta mallaki hankalin kanta, shine nakeson yanzu kayiwa baba Sa'idu magana ya bani aurenta..!".
mamaki da tsantsar al'ajabi ne ya shimfid'u afuskokinsu nan da nan sukaji tsananin bak'in ciki ya gauraye jinin jikinsu.

cikin k'arfin hali da dauriya baba Yunusa ke kallonsa yace"kai yanzu Gid'ad'o ka rasa wacce kakeso da aure sai Zainabu shin ko ka manta ne tsakanina da Sa'idu babu jituwa bale soyayya..?".
"kaida nakeson ka samu aiki ka zamo hamshak'in mai kud'i ina kai ina aure yanzu tunda bakada sana'ar fari bale ta bak'i..!".
"to bari kaji tun wuri ka chanza tunani saboda burinka bazai tab'a chika ba..!".

Inna Lantana ta bintsire baki tana fuskantarsa tace"maigida hankali ne bai ishi Gid'ad'o ba idan banda yanada k'aramar k'wak'walwa da toshewar basira mi zaiyi da Zainab wadda ko cikin mata ba kowa bace illah shara..!".
"to bazan tab'a lamunta ba ka auri d'iyar mak'iyanmu...!".

Gid'ad'o yayi narai narai da fuska cikeda tsananin damuwa yace"amma In......!".

Daka masa tsawa tayi ta dakatar dashi tace"amma mi Gid'ad'o ka fita daga cikin idanuna kafin kasa zuciyata ta tunzura inyi maka mugun baki akan figigiyar yarinyar nan..!".

"Baba Inna please ku fahimceni ku bari in auri Zainab wlh ita kad'aice macen da nake burin mallaka arayuwata...!".

Lantana da baba Yunusa suka dubi fuskar juna suna mamakin k'arfin hali irin na Gid'ad'o akark'ashin zuciyar Yunusa sai fargaba da tsoron yakeji kada tarihi ya maimaita akan d'ansa, hargowa da fad'a yaji Inna Lantana tana yiwa masa "ko zaka mutu Gid'ad'o bazaka tab'a auren Zainab ba...!".
"wato kai na fahimci so kake ka gaji ubanka wurin son mata ko!To wallahi kayi kad'an kace zaka kunyatamu awurinsu bak'ak'en munafukan can...!".

Ganin abin zai kawo hatsaniya yasa baba Yunusa ya dubeshi yace"tashi ka tafi zanyi tunani akan maganarka..!".

"ya tafi kuma maigida...!?".

"eh mana barshi ya tafi Lantana zamuyi yanke shawarar data dace nida ke akan abinda yake so..!".

Inna Lantana ta karkace baki ta kallesa tace"zaka iya tafiya inda zakaje Gid'ad'o...!".

Cikeda mutuwar jiki Gid'ad'o ya tashi tsaye zuciyarsa tana suya da tafasa ya fito daga cikin d'akin iyayensa.

saida suka tabbatar daya wuce sannan baba Yunusa ya sassauta muryarsa k'asa k'asa yace"kinsan dalilin dayasa nace masa ya tafi zamuyi tunani..?".
"ban sani ba saika fad'a maigida..!".

LAHANIWhere stories live. Discover now