LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 50*

Itama Zainab Aunty Maijiddah ce ta maidata gidanta itace ta d'auki nauyin gyara 'yar uwarta ciki da waje saboda batason Hajara ta nuna mata wani abu arayuwa,duk da Zeey bataso komawa gidanta da kukanta da komai Ummi Aziza ta tilasta mata komawa wurin Maijiddah saboda ganin rainin wayon Zainab nason wuce gona da iri,baba Sa'idu shi ko kallo bata ishesa ba domin ya lura idan ta samu sakin fuska zata iya bijirewa umurninsa,sanin halinta ne yasa suka fita sha'aninta duk tabi ta sakawa kanta damuwa ta rame kamar ba Zeey 'yar gayu ba.
Tana komawa gidan Maijiddah ta bud'e sabon salon rashin ji domin idan Aunty Maijiddah ta bata magani zubarwa takeyi batasha musamman idan ta d'aga,idan tana kusa haka take daurewa tasha tana yamutsa fuska kamar zatayi kuka baby Jawaheer dayake tayi wayo tana mak'ale da ita akowane lokaci,yayinda Maijiddah ke d'auke da cikin wata biyar, barisster Hayatu ma idan ya dawo daga wurin aiki yakan zauna da matarsa suna fira ta fahimtar juna cikin matuk'ar shak'uwa da soyayyar gaskiya.

*************************

Su Laweezi ke zaune agardener suna shan iska k'aramin teburi cikeda kayan masarufi agabansu irinsu lemu,ayaba,kankana,tuffa,da kuma gorunan lemu iri iri masu sanyi dadai sauransu.
Hudairu ne yake shan kankana yace"Lawee auren Zainab da doctor Nazeer sai k'ara kusantowa yakeyi amma naga kamar hankalinka kwance".
Laweezi ya kurb'i lemun gora bayan ya saukar da kofi yace"kaima kasan komai ahankali ake binsa shiyasa nake bin komai atsanake domin ganin burina ya cika".

  Hudairu ya saki murmushi yace"gaskiya Laweezi kanada kaifin tunani da hangen nesa".

"ai dole inbi komai asannu Hudairu domin banason inyi garaje acikin wannan lamari".

Hudairu ya girgiza kansa alamar gamsuwa da maganarsa yace"wannan gaskiya ne".

Cigaba da firarsu sukayi suna tattaunawa akan hanyar da zasu b'ullowa al'amarin auren Zainab ta bayan k'asa batare da an fahimci mi nene k'udurinsu ba.

*************************

Hajara tana gaban dressing mirror tana kwalliya saiga mahaifiyarta hajiya Baraka ta shigo tsakiyar d'akin da sallama, acikin madubi ta hangota shiyasa ta juyo fuskarta da azama murmushi k'unshe afuskarta tace"momy kece da kanki kika shigo d'akina baki kirani awaya ba".

hajiya Baraka ta murmusa tace"uhmm ganin nayi kamar b'ata lokaci ne kiranki shiyasa nace bari inzo da kaina in kiraki".
Hajara ta waro idanunta tace"to Allah yasa dai lafiya mi nayi momyna..?".
"a'aa Hajara bakiyi komai ba kwantar da hankalinki Nazeeru ne yazo wurinki shiyasa nace bari in sanar miki".
Cikin tsantsar farin ciki Hajara ta rausayar da kanta tace"ayyah momy yanzu yana ina..?".

"yana parlourn mahaifinki yana jiranki nasa 'yar aiki takai masa kayan motsa baki saboda haka kiyi gaggawar shiryawa ki tafi ke kad'aice yake jira".

"to momy kin k'yauta matuk'a shiyasa nake k'ara sonki".
"nima ina sonki d'iyata". Kammala maganarta keda wuya hajiya Baraka ta fito daga cikin d'akin bayan ta rufo mata k'ofar.

Ahanxarce Hajara ta k'arasa kwalliyarta ta jawo hijabi kalar tufafinta ta zura jikinta yana rawa ta tunkari hanyar zuwa parlourn mahaifinta, batason ta dad'e sosai ta yadda zata b'atawa habibinta rai shiyasa take sauri tana gab da shiga cikin ta chanza salon tafiyarta.
Cikin natsuwa da sansanyar k'amshin jikinta mai narkar da zuciya ta shiga ciki da sallama abakinta, doctor Nazeer da barisster Hayatu suka amsa mata fuskarsu d'auke da fara'a wuri ta samu nesa dasu kad'an ta zauna akunyace kanta noce k'asa domin wata irin kunyarsu ta dabaibayeta tareda ratsa jini da b'argon jikinta.
Ganin yadda take wani sussune kai alamun kunya yasa yah Hayatu yaji ta burgesa domin yanason mace mai kunya arayuwa,shi kuma uban gayyar bintsire baki yayi kamar mace yana jin haushin yadda take acting like ustaziya😆.

Parlourn ya d'au shiru bakajin motsin komai saina mage can yah Hayatu ya kauda shirun yace"malama Hajara barka da yau".
"barka dai".
Nannauyar ajiyar zuciya ya saukar yace"dama dalilin dayasa muka zo wurinki domin mu tattaunawa akan wane irin design kikeson room da parlournki ya kasance?".
"kuma wane irin event's zakiyi a aurenki..?".

LAHANIWhere stories live. Discover now