LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 9*

Yana kara phone d'in akunnensa ya jima yana tattaunawa da barisster Hayatu sun dad'e suna maganganu atsakaninsu sannan daga k'arshe sukayi sallama Nazeer ya katse wayar, tareda maida fuskarsa wurin momy dake zaune tana saurarensu tausayi da tsantsar haushi ne ya cika mata zuciya.
Ahankali Nazeer ya mik'e tsaye yace"momy zanje in duba jikin Zainab barisster ne ya kirani..".Momy tace"ba komai saika dawo son ka kula da kanka kaji..".
"i will momy".Rufe bakinsa keda wuya yaja k'afafunsa ya fice aparlourn kai tsaye ya tunkari parking lot.
momy kuwa mik'ewa tayi ta shige cikin d'akin baby Khairat domin kada tabarta tana k'irinniya da watsar da kayayyakinta.

**********************
Zainab tana kwance saman gado lullub'e da blanket ajikinta yayinda zazzafan zazzab'i duk ya game mata jinin jiki, alokacin ne Aunty Maijiddah take mata sannu tareda shafar gashinta can yah Hayatu ya shigo cikin tsakiyar d'akin yace"Jiddana taci abinci ne..?".
Aunty Maijiddah ta yamutse fuskarta cikin matuk'ar tausayin Zee tace"eh taci k'albi..".
Hayatu yace"abubuwan suna damuna da d'auremin kai na rasa yadda zan b'ullowa al'amarin Laweezi..!".
"amma zan tsananta bincike akansa..!".
Aunty Maijiddah tace"lamarinsa sai ahankali hubby ni duk na tsinke masa k'albi..!".
"ki daina damuwa insha Allahu *KOMAI YAYI FARKO* yanada k'arshe..!".
"da izinin ubangiji asirinsa saiya tonu...!".
"Allah yasa.. ".
"Amin".
"ka kira doctor Nazeer d'in ne hubby...!?".
"eh mana baya nesa da zuwa..".
"ki cigaba da lura da ita zan koma parlour in jirashi har ya iso..!".
"too k'albi..".Hayatu ya fito daga ciki ya koma parlour ya zauna yana jiran isowar doctor Nazeer.

  Aunty Maijiddah ta dinga share mata zufar dake tsiyaya ajikinta cikin raunin zuciya da tsantsar zullumi.

acan parlour yah Hayatu yana zaune saiga sallamar doctor Nazeer ya kutso kai tsakiyar parlourn amsa masa yayi cikeda tsananin shak'uwa, yana isowa wurinsa ya bashi hannu sukayi musabaha da juna sannan yah Hayatu yace"mu shiga ciki ka dubata Nazeer..".
"a'aaaa batada lafiya ne friend..?".
"eh zazzab'i ne yake damunta Nazeer sannan kuma ga shed'anin yaron nan ya sako agaba da barazana..".
"barisster Hayatu wai miyasa yakeson damunta ne arayuwa...?".
"mi ye tayi masa?Ko atunaninsa yanzu ana zaman aure adole ne...!".
yah Hayatu yace"shi dai ya sani idan na samu cikakken information akansa zan gurfanar dashi agaban kotu...!".
"ya kamata kam kafin yayi mata wata cutar..!".
"cuta ta nawa kuma Nazeer mutumen da yayi sanadiyyar mutuwar iyayenta ai babban mak'iyinta ne..!".

Nazeer ya gyad'a kansa alamar gamsuwa yace"zancenka gaskiya ne muje in dubata".
"to likita bokan turai..".

suna rufe bakinsu yah Hayatu ya jagorancesa har cikin tsakiyar filin d'akin alokacin ne Aunty Maijiddah ta jaye mata blanket ajiki, saida suka gaggasa da juna cikin karamci da tsantsar mutuntawa sannan doctor Nazeer ya fara yiwa Zainab gwaje-gwaje cikeda matuk'ar shauk'in so da k'aunarta, bayan ya kammala aunata ya d'auko syringe da magani ya zurara a syringe da taimakon Aunty Maijiddah ta bari akayi mata allurar zazzab'i.
saboda Zainab akwaita da shegen tsoron allura ana gama yi mata allurar ta dinga sharar kwallar zallar shagwab'a yayinda Aunty Maijiddah ta dinga rarrashinta, magunguna ya ciro a briefcase d'insa ya bata k'yauta domin sonta ya riga ya rufe masa idanuwa.
fatar samun lafiya yayi mata sannan suka rankaya suka nufi parking lot suna firarsu cikin fara'a da nishad'i aransu, ji sukeyi kamar kada su rabuda juna adalilin shak'uwa da amintakarsu, sun dad'e tsaye suna cigaba da tattaunawa sannan daga k'arshe doctor Nazeer yayi masa sallama ya fad'a motarsa ya tadda motar tareda ficewa daga cikin gidan,yah Hayatu jiki asanyaye ya juya ya koma cikin room d'in Zainaba.

LAHANIWhere stories live. Discover now