LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 73*

Cikeda mad'aukakin bak'in ciki mai tarin yawa su Hudairu suka k'araso gida, zuk'atansu cike fal da tsantsar takaicin Brr Hayatu da kuma lura da sukayi cewar idan basu d'auki k'wak'k'waran mataki akan Hayatu ba nema yake ya tona musu asirin da suka dad'e suna binnewa duniya,batare da mutane sun gano ainahin abinda suke aikatawa ba cikin wani irin rad'ad'i idanun Laweezi har k'ank'ancewa sukeyi adalilin tsabar bak'in cikin ganinsu Muttak'a amatsayin masu aibantashi yace"Hudairu nine su Muttak'a da shegen tsohon nan Hakimi zasu je kotu su bada shaidar banida mutunci..!".
"To wallahi idan basu iya bakinsu ba saina d'aure dukkan danginsu domin babu wanda ya isa yace zai cimin mutunci in k'yaleshi..!".
Hudairu ya sasauta murya sosai domin ganin zuciyar Laweezi tayi sanyi yace"miye abin damuwa Lawee?Kaima kasan tsabar hassada da k'yashi ne yasa Muttak'a ya fad'i haka saboda mun daina mu'amalar komai dashi shine dalilin dayasa yakejin haushinmu..".
"Wannan tsohon banza ai kasan dalilin dayasa yayi maka haka akan ya rok'i ka bashi kud'i ka hana masa shine yaci masa rai yayi amfani da wannan damar domin ya bak'anta maka..".

Numfashin takaici Laweezi ya sauke yayinda yakejin k'irjinsa yayi masa nauyi sosai saboda azababben rad'ad'i dake gudana ajikinsa dak'yar ya had'iye d'aci azuciyarsa yace"ai kuwa sun jawa kansu bala'in da bazasu tab'a tsallake sirad'insa ba...!".
"Saboda nayi matuk'ar alk'awarin duk wanda ya nemi ya shiga gonata saina tozartasa saina d'and'ana musu azabar dasai sun gwammaci mutuwa akan rayuwa..!".
"kada kayi saurin azabtar dasu Oga Laweezi saboda idan kayi haka kotu zata iya tabbatar da zargin da akeyi maka da gaske ne..!".
"Ohh so kake in k'yalesu su ci bulus..?".
"Ba haka nake nufi ba abinda nake nufi ka bari mu fara yak'ar wannan bak'in munafukin daya shige mana a hanci sannan mu dawo akan wad'annan k'ananan k'wari..!".
Laweezi yaji rad'ad'in dake cikin zuciyarsa ya ragu sosai yace"shikenan na k'yalesu har sai mu kammala da wannan barisstern..".
"Kana burgeni abokina domin duk yadda kayi fushi idan na baka magana kana yarda..".
"Ai dole in aminta dakai saboda baya ga mahaifiyata kaine kafi kowa kusanci dani dad'ina d'aya mahaifiyata bata halarci kotu ayau ba".
Hudairu ya mak'alo hannunsa yace"kaima kasan zan iya rik'e maka sirrinka domin amana da yardar dake tsakaninmu tafi k'arfin wasa saboda haka kasa ido kayi kallo tunda sun nuna cewar su k'wararri ne awannan haraka zamu fara nuna musu mun fisu shahara awannan afanni..".
"Haka ya kamata kam but yanzu ya zamuyi da Brr Jalal?".
"Ban fahimceka mi kake nufi Lawee ..?".
"Ina nufin duk da baiyi nasara awannan zaman ba akotu zamu biyasa kud'insa ne..?".
Hudairu ya kad'a kai yana karkad'a kunne yace"zamu biyashi duk baiyi mana yadda muke so ba domin munfi k'arfin komai na rayuwa".
"Hmmm ba damuwa idan kunyi waya kace ya turomin account number d'insa..".
"Zan fad'a masa Oga".

(((()))))(((()))))(((())))(((())

Bayansu Aunty Maijiddah sun dawo daga kotu fuskokinsu d'auke da farin cikin alamun nasara, koda suka dawo har Ramatu ta kammala girka abincin dare tuwon shinkafa da miyar kub'ewa d'anya, kowanensu room d'insa ya fad'a yayo wanka sannan suka fito cikin tufafinsu masu tsada su Ramatu ne suka hango zazzaune wurin dinning table suna cin dinner,kallon k'auna suke aikawa juna murmushin jin dad'i shimfid'e afuskarsu suka k'araso suka ja kujera suka zazzauna akai, Ramatu ce ta mik'e tsaye ta fara serving d'insu sannan ta koma ta zauna.
Cin abincin suka fara yi atsanake babu mai magana acikinsu sun dad'e suna cin abinci can d'aya bayan d'aya suka fara tashi suna dawowa parlour,Ramatu ce ta k'arshen gamawa tattara plates d'in tayi wuri d'aya ta kaisu kitchen ta wawwakesu tsab ta saka akwando.
Saida ta wanke hannunta ta dawo wurin Aunty Maijiddah ta zauna yayindasu baby Jawaheer suka mak'ale ajikin mahaifinsu cikin jin dad'i.
Ramatu ta kalli b'angaren Brr Hayatu a sace sannan ta sassauta murya sosai tace"Aunty ya shari'ar yau ina fatar akwai alamun nasara..?".

LAHANIWhere stories live. Discover now