LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 54*

Sunyi tafiya mai tazara sannan suka k'araso adaidai k'ofar gidan baba Sa'idu parker mototinsu sukayi suka firfito daga ciki, sannan suka rankaya suka fad'a cikin tsakiyar filin gidan d'auke da sallama abakinsu jin muryar mijinta yasa Aunty Maijiddah ta zuro hijabi ta fito d'auke da tabarma ahannunta shimfid'a musu tayi bayan sunyi gaishe-gaishe atsakaninsu sannan ta kawo musu kayan motsa baki adire agabansu,komawa d'aki tayi ta fad'awa Ummi Aziza cewar daddyn Jawaheer yazo suna mata sallama jin ance babanta yazo yasa Jawaheer ta fita da gudu tanata washe hak'ora da farin cikin zuwan mahaifinta domin ba k'arya tayi missing d'in daddynta.
  Ummi Aziza tace mata ta koma wurinsu gatanan tafe haka Aunty Maijiddah ta juya ahankali ta koma wurinsu,nesa kad'an dasu ta zauna ta fad'a musu Ummi tana tafe Jawaheer dake manne ajikin barisster Hayatu sai k'irinniya takeyi masa yana biye mata.
Shiru ne ya gifta atsakaninsu har saida Ummi Aziza ta fito suka gaisheta ta amsa musu fuska k'unshe da fara'a da nishad'i.
Barisster Hayatu ya gyara zama yace"Ummi wurinki muka zo".
"ina jinku Hayatu".
  doctor Nazeer ya duk'ar da kai k'asa yace"akan maganar aurena da Zainab ne naga har yanzu bakicemin komai ba shiyasa nace bari inzo inji ranar da za'ayi abin".

Ummi Aziza tace"Hayatu abinda ya kawoku kenan..?".

"eh maganar data kawomu kenan Ummi".

Ummi Aziza tayi jugum cikeda rashin kuzari da mutuwar gab'ob'in jiki murya araunane cikeda tsananin damuwa da tausayin likita tace"kuyi hak'uri likita ku sani dukkanin abinda ya faru banida laifi k'addara ce dama ubangiji Allah ya rubuto acikin kundin k'addararku bazaku kasance.............". Tari ne ya sark'eta babu k'ak'k'autawa ta kasa k'arasa maganarta...

Aunty Maijiddah ce ta mik'e tsaye da gudu taje ta d'ebo ruwa tabata tasha tana jera mata sannu,su barisster Hayatu sai sannu sukeyi mata saboda sun fahimci akwai mummunan al'amarin daya auku shiyasa take fargabar sanar musu.

Saida suka ga ta dawo cikin natsuwarta idanunta suka kad'a sukayi jajir kamar barkono.

Ganin yadda ta shiga cikin matsanancin hali mai wuyar fassaruwa yasa yah Hayatu ya tausasa murya yace"Ummi sannu ki daina damar da kanki komai ya faru akan lamarin aurenmu masu iya dangana ne da amsar k'addararmu hannu bibbiyu".
"wace irin magana ce kikeson fad'a mana amma kin kasa k'arasawa ma'ana dai akwai b'oyayyen al'amarin dake faruwa..!?".
Kwalla taff cikeda taff cikin k'wayar idanunta jikinta yayi lak'was zuciyarta sai zogi takeyi mata tace"likita hak'ik'a nasan bai k'yauta maka ba kuma ban cika alk'awarin da baban Zainabu yabarmin aduniya ba,amma inason ku sani ba laifina bane sunyi amfani ikonsu da k'arfin iko akan yarinyata suka aurar da ita Laweezi..!".
"Ku fahimceni da idon basira wallahi naira biyar banci ta yaron nan ba bale kuyi tunanin sayeni yayi...!".
Jin cewar Laweezi ya auri Zainabu ta k'arfin tsiya yasa wani irin k'ololon bak'in ciki da b'acin rai yayiwa doctor Nazeer dirar mikiya azuciya! Barisster Hayatu adalilin tsabar tashin hankali idanunsa suka kad'a sukayi jajir jijiyoyin kansa suka bayyana.

Kasa furta ko kalma d'aya sukayi asanadiyyar sun shiga cikin tsantsar rud'ani da jimamin kasancewar wannan rikitaccen al'amari mai iya tarwatsa xuciya zama guda,itama kanta Aunty Maijiddah kukan zuci takeyi saboda tsananin tausayin irin halin da Nazeer zai shiga adalilin rashin Zainaba aduniyar so,tasan irin azababben so da k'aunar da yakeyiwa k'anwarta haka kuma ta hak'ik'ance rashinta sai iya haifar masa da babbar matsala arayuwa!.
Ganin shirun yayi yawa Aunty Maijiddah tace"daddyn Jawaheer kuyi magana kunyi shiru wallahi ba laifin Ummi bane baba Yunusa da kawu Rabilu sukayi k'ulle k'ullensu suka aurawa Laweezi k'anwata, dak'yar ma Ummi ta bari suka fice da ita daga cikin gidan nan har fad'a sukayi kacha-kacha atsakaninsu asanadiyyar aurenta da Laweezi da bamu so ba.." .

LAHANIWhere stories live. Discover now