LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 23*

Inna A'i tana kammala gyaran wanken ta mik'e tsaye ta zuba acikin turmi tana dakawa sannu sannu domin kada wanken ya tartse da yawa,bayan ta gama daka wanken hancinsa ya cire ta kwashe cikin k'warya takai cikin bukka ta aje saboda kada dabbobi suyi mata b'arna,zaunawa tayi tana jiran dawowar Sa'idu ta aikeshi wurin baffa Zubairu ya amso mata kayan miyan da zatayi amfani dasu,can saiga sallamar baffa Zubairu ya shigo tsakiyar filin gidan rirrik'e da ledodi biyu ahannunsa da azama Inna ta mik'e tazo ta amshi ledodin dake hannunsa cikin ladabi tareda yi masa sannu da zuwa ya amsa mata fuskarsa ayalwace take da murmushi.
atare suka iso saman tabarmar kaba suka zazzauna bayan ta ajiye ledodin har ila yau ta sake mik'ewa taje wurin randuna ta ciko masa ruwa akofi ta kawo ta dire agabansa, baffa yana tattare da gajiya ajikinsa ya d'auki ruwan yasha tareda sauke kofin abaki yana hamdala ga ubangiji azuciyarsa saida ta bashi tsawon mintuna goma alokacin ne ta lura ya d'an huta tace"baffan yara sannu da hutawa..".
baffa Zubairu ya saki nishin gajiya yace"yauwa A'i ya kad'aici da hak'uri..?".
"gashinan muna fama baffa..".
"to acigaba da hak'uri yanayin rayuwa ne wata rana sai labari..".
"tabbas haka ne..".
Baffa Zubairu ya dinga dube dube ko zai hango d'aya daga cikin 'ya'yansa Inna A'i tana lure dashi amma batace masa uffan ba ganin yak'i gaya mata abinda yake nema ne yasa tace"baffan yara wa kake nema ne...?".

baffa Zubairu yace"yaran nan ne nake nema suzo su wuce zuwa kiwon dabbobin nan naga alamar sun fara jin yunwa...".

"basa nan duk sun fita fili saidai kuma ina ganin kamar lokacin zuwansu kiwo baiyi ba akwai sauran lokaci baffa..".

"inji wa yace miki lokaci baiyi ba?Ai lokaci yayi A'i amma tunda duk kin bari sun tafi yawon banza shikenan ba komai..".

"kamar ya na bari sun fita yawon banza baffan yara sufa ba mata bane dazan turkesu su zauna cikin gida duk yadda na iya sai sun fita garka..".

"naji Indo tashi kije ki d'aukomin furata idan kin damamin..".

Inna A'i ta dafe kanta alamar ta manta tace"ohhh bari in d'auko in dama maka furar saboda tun lokacin daka fita na mance ban dama ba..".

"to sarkin mantuwa ina jiranki..".

Inna A'i ta mik'e tsaye ta fad'a cikin bukkarta babu jimawa ta fito hannunta rik'e da k'warya cikeda fura da nono kindirmo ta kawo ta dire agabanta saman tabarma,sannan ta zauna tana damar furar taji nono tsamomo acikinta bayan ta gama damawa ta zuba masa cikin k'aramin roba ta kawo ludayi ta saka.
ita kuma ta zubawa kanta cikin k'aramin kofi tareda rufe sauran furar data rage a k'warya, baffa Zubairu ya dinga cika ludayi yana shan furar sosai domin ba k'aramar yunwa ya dawo da ita ba, Inna atsanake take shan furarta harta kammala sha ta wanke kofi ta ajiye sai alokacin ne baffa Zubairu yayi gyatsa alamar cikinsa ya d'auka sannan yace mata"idan Sa'idu ya dawo yau shi kad'ai zaije kiwo kinji..".

da mamaki kwance afuskarta Inna ke kallonsa tace"saboda mi zaije shi kad'ai alhalin tareda yayansa ya saba zuwa kiwo..?".

"saboda tunda safe ina zaune arumfar kasuwa Yunusa yazo ya amshi kud'in magani ahannuna yacemin bayada lafiya, to kuma kinga tunda rashin lafiya ya kauda komai ai sai ayi masa lamuni zuwa wani lokacin suje tare..".

LAHANIWhere stories live. Discover now