LAHANI

3 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 5*

Aunty Maijiddah ta lece baki cikeda tsananin damuwa yayinda a k'ark'ashin zuciyarta takejin wani irin azababben zafi da rad'ad'in ciwo yana yawo cikin jikinta da k'wak'walwarta, ji takeyi tamkar ta aza hannu saman kai ta kurma uban ihu asanadin yadda Laweezi ya zamo sanadiyyar tab'arb'arewar farin cikinsu da kuma mutuwar iyayensu!.
dak'yar ta danne damuwarta ta fad'ad'a fuskarta da murmushi tamkar babu abinda yake damunta tace"wannan zancen naka gaskiya ne noorul hayat ya kamata afara bin diddigin Laweezi domin agano mi yake aikatawa ni tun farkon ganinsa da idanuwana sukayi tozali dashi zuciyata ta tsinke gangar jikina ta nasa mini araina ba mutumen kirki bane...!".
"shiyasa tun farko banso Zainab ta aureshi ba amma dayake tanada taurin kai ta k'ek'eshe idanunta tace saishi idan bashi ba zata iya kashe kanta....!".
"hmmm gaskiya tun farko Zeey ta tafka babban kuskure arayuwarta shiyasa tun yanzu take fuskantar jarabobin rayuwa saboda abinda ta aikatawasu Ummi bata k'yauta ba...!".
"sauk'in abin ma ta rok'esu gafara kafin subar duniya da sun mutu da fushinta azuciyarsu da har abada bazata tab'a ganin cigaba ba arayuwarta...!".

Aunty Maijiddah tace"ai shine sauk'in data samu dear...!".

"haka ne gaskiyar magana..".

Cigaba da maganganunsu sukeyi cikeda matuk'ar jimami da tsantsar tausayin Zainaba wadda take fuskantar guguwar k'unci da tsantsar barazana awurin tsohon mijinta Laweezi.

**********************
Zainab kuma tana shiga cikin tsakiyar filin d'akinta ta cire tufafinta ta d'aura towel ajikinta sannan ta fad'a bathroom tayo wanka sharp sharp batare da b'ata lokaci ta d'auko doguwar rigarta bak'a ta zura ajikinta, babu kwalliya babu komai lotion kawai ta shafa afatarta sannan ta kwanta saman hamshak'in gadonta rungume da phone ak'irjinta,tunanin irin maganganun da Laweezi yakeyi mata ne masu nuni da barazana da kashedi arayuwa suka fad'o mata arai suna mata yawo cikin k'wak'walwarta da ilahirin jiki, juye juye ta dingayi akan gadon domin ta rasa mafita da hanyar da zata b'ullowa al'amarinsa saboda ta tabbatar da gaskiyar zancensa akan duk abinda ya fad'a to tabbas saiya aikatashi domin ganau take ba jiyau ba.
azamantakewar rayuwar aurensu da sukayi ashekaru uku da suka wuce ta riga ta lak'anci halayyarsa tareda karantarshi ciki da wajensa na yadda ko paper da biro aka bata zata iya rubuta halayensa tsab batare da tayi kuskure ba, saboda afarkon aurensu bata fahimci wa nene shi ba saida zaman aurensu yayi matuk'ar nisa sosai sannan da sannu sannu ta fara gano ainahin halayensa miyagu dayake b'oyewa mutane bayason asani.
tana tsaka ga tunani can taji wayarta ta fara ruri alamar ana kiranta cikeda rashin kuzari ta tashi zaune tareda k'urawa nombar da ake kiranta da ita, mamaki takeyi na yadda akullum sai an kiranta bak'uwar nombobi iri iri daban daban tunaninta maishi ko companyn MTN yake aiki ai yaci ace ya gaji da chanza layukkan waya domin chanje chanjen is too much, kamar bazata d'auka ba sai wani b'angare na zuciyarta ya bata shawarar ta d'auka wani b'angare kuma ya gargad'eta akan kada tayi receiving call ta sani ko Laweezi ne ke damunta da yawan kira.
  har ta yanke shawarar bari tayi receiving call taji ko waye yake kiranta tana dannawa kiran ya katse, siririn tsoki taja cikeda matuk'ar takaicin ko waye tace"garama da kiran ya katse koma waye ko wa cece can ta matse masa...!".

Tana rufe bakinta can wani kiran ya sake shigowa a phone d'inta still nombar d'azu ce aka koma kiranta da ita receiving call d'in nombar tayi cikin tsananin haushi ta kara akunnenta tace"wai wane irin maye ne ke damuna da yawan kira...!?".

LAHANIWhere stories live. Discover now