LAHANI

1 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 12*

Bayan ya dasa aya a k'arshen labarinsa jikinsu Zainab duk ya gameda tsananin sanyi zuciyarsu ta dinga rawa alokacin ne taji wasu irin ruwan hawaye sun wanke mata fuska,da sauri ta share hawayenta afaikace saboda batason su Aunty Maijiddah su hankalta da yanayin firgici da tsantsar rud'un data shiga ciki, d'akin ne ya d'auki shiru na tsawon lokaci can Aunty Maijiddah tace"yanzu Laweezi ne ya torosu suzo su bamu hak'uri..?"."Babu shakka haka sukace min dear.."."Hmmmmmm amma Laweezin nan kwata kwata bayada kunyar baisan hanyar da kunya tabi ba shiyasa ya rab'e mata ta wuce can wani wuri..".
"shi atunaninsa zai iya yaudararmu mu yarda mubar Zeey ta koma gidansa saboda tsabar jahilci iri nasa..".
Hayatu ya girgiza kansa cikin zafin zuciya tace"barni dashi dear da sannu zan nuna masa shi k'aramin alhaki ne tareda koya masa hankali..".
"bai sanni bane shiyasa yake neman afkawa cikin gonata..!".
Aunty Maijiddah ta marairaice fuska cikin tsagwaron damuwa da tsananin tsoron Laweezi tace"k'albi kabi komai ahankali domin Laweezi yanada matuk'ar had'ari arayuwarsa mugu ne na k'arshe..!".
da sauri yah Hayatu yayi duba cikin k'wayar idanunta ya hango tsantsar tsoro da tashin hankali acikinsu hakan ne yasa yaji tausayinta ya d'arsu azuciyarsa cikin sanyin murya yace"zanbi ahankali kinji kema please ki daina sakawa kanki damuwa komai zai wuce kamar bai tab'a faruwa ba..".

"zan rage k'albi da yardar Allah".

ya juya b'angaren Zainab dake mak'ale ajikin Maijiddah ta lahe mata kamar mage numfashi yaja yace"Zainab..".
"na'am yaya Hayatu".
"kinason farin cikinmu...?".
"kinason kwanciyar hankalinmu..?".
"kinason mu samu galaba akan Laweezi...?".
Zainab ta gyad'a masa kai alamar eh mana tana so sannan tace"ina so mana yaya".
"idan har kinason farin ciki da kwanciyar hankalinmu please na rok'eki ki daure ki cire komai azuciyarki da sannu komai zai daidaita...!".
"sannan kuma ki dage da yawan addu'ar ubangiji Allah ya tona asirin koma waye yakeda sa hannu acikin mutuwar iyayenki da sannu gaskiya zata bayyana k'arya ta gushe..".
"kinsan ita gaskiya dawwamammiyar abu ce yayinda k'arya bata tab'a dawwama na tsawon lokaci batare data fito fili ba..".
Jikin Zainab ya k'ara yin sanyi azuciyarta ta dinga harbawa hawayen da suka zamo mata abokan rayuwa ne suka dinga shatata afuskarta tamkar an bud'e famfo tace"insha Allahu zan dage da yawan addu'ar ubangiji ya tona asirin ko waye ya kashe mana su Ummi..!".

"OK don't worry little sister komai yayi zafi maganinsa Allah..".
Cigaba da rarrashinta sukayi suna gaya mata maganganu masu sanyi wad'anda zasu iya gusar mata da damuwarta nan take, saboda su kansu tsantsar tausayi take basu sannan kuma al'amarin Laweezi ya fara rikita musu k'wak'walwa da hargitsa tunaninsu.

**********************
Su Hudairu suna ficewa daga gidan barisster Hayatu basu zarce ko'ina ba sai a k'ofar gidan Laweezi suna cikin mota zaune batareda sun fito ba, Hudairu ya ciro phone d'insa a aljihunsa yayi dialling nombar Laweezi tana fara ringing ya d'aga wayar yace"hello Hudairu ya akayi ne..?".
"ka fito waje gamunan abakin get d'in gidanka.".
"har kun dawo kenan..?".
"eh mana".
"ku shigo cikin gida mana Hudairu".

"kaga agajiye muke ka fito idan zaka fito in isar maka da sak'on barisster Hayatu..".

"okay am coming now..".Yana rufe bakinsa ya katse wayar tareda fitowa daga cikin parlourn direct ya nufi hanyar fita daga cikin gidansa.

LAHANIWhere stories live. Discover now