LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 57*

Zainab dake kwance saman gado tasha kuka harta k'oshi barci ya fara fisgarta harta fara nisa ciki sosai,kamar amafarki taji ana knocking door da sauri ta mik'e tsaye bayan ta zuro hijabi ajikinta ta iso bakin k'ofar parlour ta bud'e, idanunta suka fad'a cikin na shugaban bodyguards d'in dake tsaron lafiyar mijinta.
Asanyaye Zainab tace"lafiya dai..?".
"hajiya kinyi bak'uwa ne tacemin kinsan da zuwanta shine nace bari inzo in tabbatar da hakan".
Zainab tayi mamaki matuk'a amma bata nuna masa ko afuska ba cikin k'arfin hali tace"miye tace maka sunanta..?".
"Samrat".
Zainab ta saki murmushin murna tace"ohhh she is my friend allow her to come in please".
"okay hajiya kiyi hak'uri na dakatar da friend d'inki i don't know her shiyasa dana dakatar da ita awaje".
"no problem ai aikinka kakeyi saboda haka bazan ga laifinka ba".
"thank you so much hajiya".
Rufe bakinsa keda wuya ya juyo ya dawo wurin Samrat wadda harta fara gajiya da tsayuwa,yana isowa ya bata hak'uri adalilin tsayar da ita da yayi bata samu sararin yi masa magana ba direct ta nufi hanyar zuwa parlourn.
Tana iza k'ofar parlour kamar daga sama Zainab ta fad'o mata ajiki tareda k'ank'ameta cikeda tsananin shauk'in so da farin cikin ganinta arayuwa,itama Samrat murmushi kawai takeyi sun jima rungume da juna Zeey taja hannunta sukayi masauki saman cushion tace"Samrat ashe zan k'ara ganinki har na cire rabon sake had'uwa dake rayuwata..!".
"to ai gashi yanzu kin ganni".
Zainab zata mik'e Samrat ta dakatar da ita tace"yi zamanki idan abinci zaki kawomin ak'oshe nake".
Zainab ta koma ta zauna akan cushion tace"ko ruwa bazaki sha ba k'awata..?".
"Zan sha wata rana ai kefa nazo ne domin mu tafi gidan Aunty Maijiddah bikin d'anta ko bakisan yau ne ake sunan yaronta ba..?".
Rau rau da idanu Zainab tayi tace"na sani amma Laweezi ya hanani zuwa gidanta bai amince inyi alak'a daku ba..".
"kina nufin hardasu Ummi yace bazaki koma alak'a dasu ba..?".
Zainab ta gyad'a kanta alamar eh haka ne.
"Lallai wannan anyi marasa mutunci..!".
Zainab tace"amma yau ya bani izinin zuwa shopping Samrat kinga da wannan damar zanyi amfani inbi ki muje gidanta but sai mun fara zuwa shopping sannan in tilasta drivernsa ya kaimu can".
"To yi sauri kije ki d'auko handbag d'inki mu wuce kada mijinki ya dawo".
"Aiba kowane lokaci yake barci agidan nan ba".
"auuuu abin na Laweezi babba ne".
"don ma ba kiga yadda yake aikata wasu abubuwan ba". Zainab tana rufe bakinta taja k'afafunta da sauri ta fad'a d'aki domin ta d'auko handbag.

Bada dad'ewa saiga Zeey ta dawo rataye handbag a kafad'arta Samrat tana ganinta ta mik'e tsaye suka rankaya suka iso har parking lot,dayake drivern Oga Laweezi ya fad'a masa zai kai madam shopping shiyasa ya shek'o da hanzari ya bud'e musu k'ofar mota maigadi ma tuni ya wangale musu get d'in.
  Suna tafiya cikin mota suna firarsu cikin natsuwa sai kallon mototi da mashunan dake wulgawa sukeyi atiti,drivern Oga Laweezi dayake ba kasafai yakejin hausa ba shiyasa basu damu dasu fad'i abinda yake cikin ransu ba.
"Zeey gaskiyar magana kina cikin wahala ga daula ga komai amma baki samu kulawa, soyayya,da k'aunar miji ba ji yadda kikayi bak'i kika rame kamar bake ba..".
Zainab ta lece baki tace cikin jimami"to ya zanyi Samrat dukkan abinda ya sameni nina jawa kaina saboda tun farko dana amince da zab'in iyayena da yanzu ina can hankalina kwance agidan doctor Nazeer amma saina bari makahon so ya rufe mini idanu...!".
  Samrat ta dafata tace"ki daina ganinki laifin kanki ai naji labarin cewar baba Yunusa da kawu Rabilu ne sukayi shige da fice har suka aura miki Laweezi batare da saninku ba".
"kedai aurena dashi babu zato ko tsammani Ummina batada masaniya akan komai adalilin aurena da Laweezi har k'aramar hauka tayi kamar ta cire zane ta yassuwa,Aunty Maijiddah tana rarrashinta tana komai amma ko saurarenta batayi ba baba Yunusa amfani yayi da k'arfin iko akanmu ya wuce dani daga gidan iyayena...".
"Nasan duk dayake kinason Laweezi amma kinson bin umurnin iyayenki".
"naso k'awata amma su baba Yunusa sunyi amfani da ikonsu akaina sun kawoni gidan azzalumi wanda baisan darajar d'iya mace ba..!".Ta fad'a tana had'iye wani irin d'aci da mololon bak'in ciki dayake mak'ale aranta akowane lokaci.
"kiyi hak'uri komai zai wuce kamar amafarki nidai fatana ubangiji ya cireki daga cikin k'angin rayuwa".
Zainab taja gyashi cikin d'acin rai tace"hmm amin ya Allah".
Magana suka cigaba dayi har ya k'araso dasu wani irin katafaren super market driver ya parker motar abakin super market d'in,yana parkerwa su Samrat suka fito daga ciki kai tsaye suka fad'a cikin super market driver ya fito daga ciki tareda jingina bayansa akan motar Laweezi.

LAHANIWhere stories live. Discover now