LAHANI

4 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 4*

Aunty Maijiddah ta dinga shafar gadon bayanta cikin matuk'ar tausayi da rarrashinta yayinda duk wata gab'a dake jikinta tayi lak'was asanadiyyar tausayin tilon k'anwarta daya mamaye rayuwarta, ita kanta Laweezi haushi yake bata saboda ganin yadda yake neman hargitsawa Zainab rayuwa da rikita mata k'wak'walwa, huci tayi mai tattare da d'acin rai da rashin samun mafita tace"Zee kukan ya isa hakanan kinji please ki rage yawan haddasawa kanki damuwa domin banason in rasaki saboda ke kad'aice kike ragemin aduniya....!".Zainab ta dinga saukar da numfashi kad'an kad'an cikeda tsananin damuwa da tsoron Laweezi tace"dole in shiga cikin damuwa saboda Laweezi bazai tab'a barin inyi rayuwar farin ciki ba Aunty so yake ya kasheni inbar duniya...!".
"nayi nadamar aurensa nadama mara amfani domin duk abinda yayimin alhakinsu Ummi ne ke bibiyata Aunty Maijiddah....!".
"kaiconah ni Zainaba naga ta kaina! Na biyewa son zuciya da rud'in shaid'an sun kaini cikin tafkin wahala da tsantsar bak'in ciki arayuwa....".
"ina zan saka rayuwata inji sanyi ina ma ana maida hannun agogo baya dana maisuwa na gyara babban kuskuren dana tafka arayuwata...!".
"baba Ummi ku yafemin alal hak'ik'a na sanyaku cikin k'unci da tsananin bak'in ciki alokacin da kuna raye duk da kun yafemin amma har yanzu alhakin b'ata muku rai da nayi yana bibiyata...!".
"da wannan k'unci da uk'ubar rayuwar da nake fuskanta arayuwata gwamma ace na mutu in huta da takaicin rayuwa Aunty....!".
Jin yadda muryarta ta dashe take sakin sambatu kamar zararriya yasa hankalin Aunty Maijiddah ya tashi alokaci d'aya hawayen k'unci da zullumi suka shatata afuskarta tamkar an bud'e famfo dak'yar ta furta"ki daina cewa gwamma ki mutu Zeey saboda idan kika mutu banida wadda zan kalla amatsayin jinina k'anwata inji sanyi saike...!".
"hakan daya faru dake rubutaccen al'amari ne daga ubangiji sarki shine ya rubuta duk ire iren abubuwan da zasu sameki tun kafin kizo duniya...!".
"saboda haka ki daina kuka kinji Zeey d'ina...".
"k'irjina yayi mini nauyi zuciyata ciwo takeyi tamkar zata tsage akan tsantsar zafi da rad'ad'in da nake ciki....!".
Aunty Maijiddah ta jaye jikinta ana Zainab tace"sorry little sister zaki samu sauk'in abinda kikeji azuciyarki anjima zan kira doctor Nazeer yazo ya dubaki...!".
shagwab'e fuskarta tayi tace"banaso adubani...".
"saboda mi Zee...!?".
"saboda ko adubani ko kada adubani bazan tab'a warkewa daga cutar bak'in cikin da Laweezi ya k'unsamin ba har sai an gurfanar dashi agaban kotu an yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata...!".
"komai daren dad'ewa gaskiya zatayi halinta Zainab duk wanda yakeda sa hannun acikin mutuwarsu Ummi sai asirinsa ya tonu....!".
"shawarar dazan baki shine ki bari abi komai asannu k'anwata muddin aka gano ainahin wanda ya kashesu to tabbas za'a gurfanar dashi agaban kotu....!".
Zainab ta had'iye wasu busassun miyau a mak'oshinta cikin disasshiyar muryarta tace"naji zan daure in ragewa kaina damuwa...!".
"da kam yafi kafin ciwon zuciya ya kamaki...!".
Zainab ta numfasa tace"to Aunty".
"yanzu ki share hawayenki tareda gyara fuskarki Abbansu Jawaheer yana son magana dake...!".
Zainab bata sake magana ba ta mik'e tsaye zubur ta fad'a bathroom ta wanko fuskarta Aunty Maijiddah tana kallonta tazo gaban mirror tana shafa powder afuskarta, saida ta kammala gyara fuskarta ta yadda k'arya ne idan ba'a gabanki tayi kuka ba ki iya fahimtar tana cikin matsanancin hali da tsananin tashin hankali ganin ta gama ne yasa tace"na gyara fuskata Aunty..".
"ko kefa muje d'akinsa to..".Aunty Maijiddah k'arasa maganarta keda wuya taja hannun Zainab suka fito daga ciki room d'in kai tsaye suka tunkari d'akin yah Hayatu.
suna isa bakin k'ofar Aunty Maijiddah tayi sallama tareda fara shiga ciki Zainab ta biyota abaya cikeda rashin kuzari da tsantsar damuwa, wurin mijinta Aunty Maijiddah ta zauna yayinda Zainab ta zauna k'asan carpet kanta asunkuye zuciyarta sai tsananta zogi da k'una takeyi wani irin tururin d'aci ne ke ziyartar lungu da sak'o na magudanar jijiyoyinta, ganin yadda tayi shiru yasa yah Hayatu ya dinga k'are mata kallo yana nazarinta na wasu mintuna kad'an nannauyar ajiyar zuciya ya saukar ya furta cewar"Zainab".

LAHANIWhere stories live. Discover now