LAHANI

0 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*Sister Mardiya Ahmed (Amingo Queen)marubuciyar ADEEL(Mr Handsome) karamcinki da k'aunarki ga wannan novel shine yafi komai sakani cikin nishad'i da farin ciki matuk'a,tabbas ke d'in kin kasance mafi daraja da soyayya azuciyata akodayaushe,ina rok'on ubangiji Allah ya d'aukaka rubutunki asocial media yasa ki zamo fitacciya acikin marubuta*.😘

*PAGE 51*

Jin muryar Laweezi ya daki dodon kunnenta yasa ta lumshe idanu cikeda tsananin annushuwa tace"heart desire kaine ka kirani yau..?".
"Nine Angel kina mamaki ne..?".
"a'a ba mamaki nakeyi ba saboda ba yau ne ka fara kirana ba illa ganin yanzu kana gab da rasani gashi ka kasa aiwatar da komai akan haka..!".
Numfashi taji ya sauke yace"Zainaba bakida damuwa muddin akaina ne nace ki daina damuwa aurenki da lusarin namijin nan tamkar ya rushe ne..".
Zainab ta zumb'ura baki tace"ta yaya zan kwantar hankalina bayan ina gab da zamowa mallakin wani ba kai ba,ai kasan dole natsuwata ta gushe farin cikina na tarwatse asanadin zan rasa abokin rayuwata..!".
"idan ka yarda adalilin tsabar bak'in ciki da tashin hankalin da nake ciki tsakar dare baya iya yin barci..!".
Laweezi yace"duk abinda kikeji ina jin fiyeda haka Angel".
"kedai ki zuba idanu kisha kallo zakiga irin abubuwan da zasu biyowa baya..".
Zainab tace"shikenan tunda kace nabar komai ahannunka".
"eh mana kibar komai ahannuna zakiga aiki da cikawa".

Soyayya suna cigaba dayi babu k'ak'k'autawa acikin waya Laweezi ya cigaba fad'a mata daddad'an kalamai masu k'ara wutar soyayyarsa azuciyarta,itama sai mayar masa da martani takeyi cikeda tsantsar murna sosai domin maganar da sukeyi har yasa damuwar dake ranta ya kau saboda Laweezi ya k'ware wurin salon yaudara tareda iya mantar da duk wata d'iya mace damuwarta...

************************
Mama Halima tana zaune kusaga Laweezi take tambayarsa yadda ake ciki game da aurensa da Zeey, Laweezi yana sanye da guntun wando da singlet yana aiki alaptop d'insa yace"mommy mahaifinta bayada mutunci shiyasa nakeson in nuna masa iyakarsa..".
Mama Halima ta lece baki tace"hmm kasan talaka baisan mutunci ba son idan banda yanada k'ashin tsiya kamarka zaije yace yanason d'iyarsa amma ya tsaya maka taurin kai..!".
"barni dashi mommy zaya gane kurensa..!".
"ina goyon bayanka amma komai zakayi ka dinga taka-tsantsan kaji".
"na iya takona saboda akwai mak'iya akewaye dani".
"Good".

*************************
"Baban Zainabu ni banga dalilin dayasa ka b'oyewa su Maijiddah ba kosu waye sukayi maka wannan ta'addancin ba..!".
baba Sa'idu yace"Aziza dole in b'oye musu domin idan na kuskura na sanar musu rayuwar 'ya'yana zata iya shiga cikin garari,gara abin ya tsaya iya kanmu daya koma akan yaranmu".
Ummi Aziza ta karkace baki tace"ni wannan lamari yana bani matuk'ar tsoro da mamaki hankalina tashi yakeyi idan ina tunawa da akwai mai son ganin bayanmu..".
"Abin takaici da bak'in ciki Aziza yaron duk yayi amfani da kud'i ya siye dukkanin danginmu shiyasa ranar nan suka zo sukayi mana cin mutunci na k'arshe, sannan yaya Yunusa da Rabilu duk ya saya musu manyan manyan gidaje ya bud'e musu shagogi suna gudanar da sana'a bugu da k'ari kuma ya mallaka musu tsadaddun mototin hawa..".

Ummi Aziza ta girgiza kanta alamar mamaki tace"ohhhh kace shiyasa su yaya Yunusa suka gujemu domin sun samu arzik'i to ai naga arzik'in 'yarmu suke ci".
"rabudasu rud'anin duniya ne ke d'ibarsu nasan da sannu duniya zata koya musu hankali, nidai koda ace talauci zai kasheni ya zamto banida ko sisi bazan tab'a amsar kud'in yaron nan domin bansan wace irin hanyoyi yabi ya tarasu ba...".
"haka ne maigida tunda gashi ana zarginsa da rashin kirki".

LAHANIWhere stories live. Discover now