LAHANI

2 0 0
                                    

🔱⚜ *LAHANI..!*🔱⚜
      🔱⚜🔱⚜🔱
           🔱⚜🔱
                ⚜

*♟ŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍🏻*
  _{Onward Together}_

*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA.*

*Dedicated to*
*Zainab Chubad'o*

_Special gift to bro Hassan Atk da Hussaini Atk_.

_Bismillahir rahamanir rahim._

*PAGE 8*

Su Zainab suna tsaye jugum har saida sukaga b'acewar mototinsu Laweezi Ninja sannan suka rankaya suka iso bakin motarsu, Labbo driver ya bud'e mata k'ofar motar yana mata sannu dak'yar take iya amsawa saboda duk ta galabaita da tsayuwa, sannan ya koma mazauninsa ya tadda motar suka bar wurin da sauri domin kada su sake dawowa su riskesu anan.
Labbo driver tuk'i yakeyi yana jin d'ar d'ar azuciyarsa saboda bayason asamu mishkila ko wani tsaikon dazai kawo masa matsala arayuwa, yayinda Zainab tayi kishingid'e saman kujera tana lumshe idanunta saboda duk gab'ob'in jikinta ciwo sukeyi mata, hankalin Labbo driver bai kwanta har saida yaga sun iso bakin get d'in gidan an wangale musu suka kutsa kai parking lot.
To alokacin ne ya saki nannauyar ajiyar zuciya mai nuni da hankalinsa ya kwanta, Zainab ta bud'e k'ofar motar ta fito agajiye tana yamutsa fuskarta direct hanyar parlour ta tunkara da sassarfa, shi kuma Labbo driver saida ya kintsa kansa sannan ya ciro k'atanyar ledarta aboot yakai mata abakin aparlour ya ajiye tareda juyowa ya koma wurin baba maigadi suka fara tab'a firarrakin duniya.

Dak'yar Zainab ta iso room d'in Aunty Maijiddah ta isketa kishingid'e saman pillow tana hutawa yayinda acan parlour su Jawaheer ne zaune suna kallon cartoon, to ganin Labbo driver ya ajiye k'atanyar leda yasa Jawaheer itada Mahafuz sukayi kama kama suka kaita cikin d'akin Zainab saboda sun san nata ne, basu b'ata lokaci ba suna ajiyewa suka fito a room d'inta domin kada ta riskesu ciki tayi musu d'an banzan duka!.

A d'akin Aunty Maijiddah kuma tana ganin Zainab ta dawo ta fad'ad'a fuskarta da murmushi cikeda tsananin k'aunarta da tausayawa tace"Zeey har kin dawo..?".
"eh Aunty na dawo..".Zainab ta fad'a bayan ta zauna gab da ita.
"amma naga kamar kin dad'e sosai asuper market ko kun samu go slow ne...!?".
"mi ya tsayar dake kika jima awaje...!?".
Zainab ta langwab'e kanta cikin matuk'ar gajiya da tsantsar Laweezi tace"Aunty bamu samu tsaikon mototi ba Laweezi ne ya tareni agaban super market...!".
Aunty Maijiddah ta dubeta afirgice tanata maimaita sunan Laweezi akanta wani irin mugun d'aci ne ya gauraye jinin jikinta akid'ime tace"Laweezi Laweezi kuma waye ya sanar masa kinje can...!?".

"nima ban sani ba..!".

"baki sani ba...?".

"eh Aunty".

Aunty Maijiddah ta girgiza kanta kamar k'adangarwa tace"wannan hatsabibin yaro bazai tab'a daina bibiyarki ba Zeey...!".
"shawarar dazan baki shine ki rage yawan fita idan ba haka komai zai iya faruwa dake...!".
"haba Aunty kulli zan shiga kuma..!?".
"eh mana shi zaki shiga idan baso kikeyi ya k'ara cutar dake ba...!".

"kinji ma abinda ya fad'a...!".

"sai kin fad'a Zeey".

"wai cewa yayi in zamo cikin shiri saboda akowane lokaci zan aiko yaransa suzo d'aukata su maidani gidansa...!".

"ya maidake gidansa ya tab'a ganin anyi haka yarinya bata so..!".
"to bazata sab'u ba wai bindiga aruwa wannan karon bazan tab'a lamuntar ya k'ara cutarmin dake ba...!".
"idan ya kama ankaishi kotu arabaki da wahalallen aurensa to haka za'ayi Zainab saboda na fahimci cewar rayuwarki yake farauta ba soyayyar gaskiya yakeyi miki ba....!".

Jikin Zainab ya k'ara yin sanyi azuciyarta ta dinga bugawa kallon fuskar yayarta tayi tace"Aunty kada mukaishi kotu ina matuk'ar jin tsoron tuggu da tsantsar makirci irin na Laweezi...!".
"kwata kwata babu imani da tsoron Allah azuciyarsa....!".

LAHANIWhere stories live. Discover now