Chapter 14

1.2K 82 4
                                    

Hibba

A Cikin baccina na soma jin hanaye suna lalubata ha'de da hucin saukan numfashi bisa wuyata, a firgice na farka kafun na waigo naji ya ha'de ni da jikinsa, na soma jin hannayensa suna yawo a sansar jikina yana ta'ba wuyata, daga bisani ya juyo dani muna fuskantar juna, sanye yake cikin farar jalabiya, daga wutan dake kunne ta gefen gado, ina iya hango kyakywar fuskarsa, wani irin sanyayen kamshi ne na musamman ke tashi a jikinsa naji ya matso da fuskarsa dab da nawa, numfashin mu ya gaurayu wuri daya, ya talllafo gefen fuskata yana shafa a hankali gabadaya tunanina a hargitse yake sai faman zaro ido nakeyi zuciyata cike da fargaba, a hankali naga matso yana kallon cikin kwayar idanuna ya furta" ya jiki... how are you feeling now?"

Da kyar na iya bude baki nace mishi "da sauki" sai a lokacin abubuwan da suka faru jiya da dare suka soma dawo mun, na da'go ina dubansa shima dubana yake da wani expression da ban gane ba, "ki tashi kiyi sallah lokaci na tafiya"

Cike da mamaki nake dubansa jin abunda ya furta kamar bashi yake ta'ba jikina ba yanzu kuma yazo yana tunatar mun da sallah?

Bance dashi komai ba illa binsa da kallo da nakeyi, naga ya mike yana fa'din ki samu kiyi sallah kiyi wanka ki shirya zan kira personal doctor yazo ya dubaki anjima, shiru nayi ina dubansa daga bisani na gyada masa kai, bai sake ce dani komai ba ya juya yayi hanyar fita na tsurawa bayansa ido kirjina na wani irin bugu, ban dauke idanuna akansa ba har sai daya ba'cewa ganina na sake rintsa idanuna ina jin wani abu a jikina da ban ta'ba ji ba a game da wani da' namiji. A hankali na mike jikina duk a mace nayi hanyar bayi na kuna ruwan zafi ta pampon na fara wanke fuskata da bakina tukuna na dauro alwala na fito, da kyar na iya gabatar da sallah a sanadiyar jikina dayayi weak, ina idarwa na soma azkar har bacci ya kuma tafiya dani.

Sai wuraren karfe tara na safe na farka, motsinsa ne ma ya farkar dani naga ya shigo hannunsa rike da wasu fararen ledoji, ya dire mun a gaba, kamshi abinci ne ya gauraye mun hanci, ina kallonshi ya bude ledan ya ciro wraps din abinci da akayi wrapping da foil gwanin ban sha'awa, soyayyar kaza ce da wani sauce da ban gane ba, sai kuma chinese rice dayaji shrimp da kwai, sanye yake cikin suit dinsa as usual, zama yayi a gefena yana encouraging dina dana ci abincin, kallon abincin nayi dukda ina jin yunwa amma sai na tsinci kaina da rashin samun appetite, tunanin Ammar ya fa'do mun na da'go ina dubansa muryata na rawa nace "yau zaka kaini naga Ammar ko?"

Ajiyar zuciya ya sauke "Ammar, Ammar...Ammar, bakida wani zance sai na Ammar?"

"Dole nayi tunaninsa, kanina ne"

"I know but you have to get well first, you should worry about your health tukuna"

"Toh ai Na samu lafiya, daman zazzabi ne kawai" nayi saurin fa'da

Murmushi ya sake ha'de da shafar gefen fuskata yace "kici abinci"

A hankali na dauko spoon na debi abinci na kai bakina na soma taunawa amma naji gabadaya bakina babu da'di, na kara cokali daya biyu na ture ina ajiyar numfashi. Kallo na yayi na yan mintuna bai takura akan sai lallai naci abincin ba ya mike ya ya fice daga da'kin, a hankali na koma na kwanta.

After about 30 minutes sai gashi nan yayi knocking ha'de da sallama ya shigo tare da wani matashin doctor yazo zai duba jikina, ban musanta ba matashin doctor ya karaso inda nake kwance yana mun tambayoyi daga bisani yace zai debi jinin amun test, bayan ya deba jinina yamun allura da zai kwantar da zazzabin yace zaije ya dawo da tests results. Tare suka fita da Hassan, ina kwance a wurin idanuna suka soma mun nauyi har bacci yayi nasaran tafiya dani.

Mafarkin Umma'na da Abbana dana soma yi ne ya farkar dani, na bude idanuna a tsorace ina ajiyar zuciya, don jin mafarkin nayi kamar da gaske, gani gasu ga Ammar....A hankali na cigaba da ajiyar numfashi ina tuno shekarun baya da suka shu'de. Lokacin da iyayenmu suke da rai, lokacin da rayuwa ke da sauki bamuda wata damuwa, iyayenta sun bamu kulawa daidai gwargwado dukda mun taso bamuda shi amma hakan bai hana su koya mana wadatan zuci, sun dora mu akan hanya sun bamu tarbiya, ban ta'ba ganin Ummanmu tasa Abba a gaba ba akan sai lallai yayi mata wani abu. Gata da hakuri da juriya, duk runtsi duk wuya tana rungume da mu, Ita da Abbanmu suna matukar son juna, yanda suke soyayyarsu yana matukar burgeni, a hankali zuciyata take hasko mun sanda ina yar' shekara gomata ina kwance bisa kafar Ummana a tsakar gida tana mun tsifa, na da'go cike da yarinta nace "Umma nima inaso nayi aure na samu wanda zai kula dani kamar yanda Abba yake kulawa dake"

Murmurshi Ummana ta sake, kamar batada wata damuwa a duniya, Umma'ta kyakyawar mace ce in and out, fara ce sol idan ka ganta tamkar bafulatana, mutane da dama suna ce ita na biyo don kamanin mu da'ya da ita, Ammar ne kadai yake dan fizgo mahaifinmu, batada damuwa sam shiyasa burina kullum bai wuce na dauki irin halayenta ba.

A hankali ta soma shafan kumatuna tace "insha Allah Hibbatullah zaki samu wanda zai kula dake, zai soki ya baki duk wata kulawa da kike bukata a duniyar, koda bayan ranmu bazaki ta'ba kukan marairaci ba"

Murmushi na sakar mata muna cigaba da tsifan mu sai ga Abba nan ya shigo rike da Ammar wanda yake dan shekara takwas, duk yayi dumu dumu da jikinsa a sanadiyar buga kwallon kafa daya je yi, Umma zata mike ta tarbe shi yayi saurin dakatar da ita yace mu cigaba da abunda mukeyi, da kanshi ya shiga ya tube jikin Ammar ya masa wanka ya canza masa kaya sa'anan suka fito sai faman kyalkyale dariya sukeyi, yazo ya zauna a gefen ummanmu yana janta da hira.

A hankali na lumshe idanuna na bude, ina tunanin dama rayuwarmu ta cigaba a hakan, hawaye masu zafi suka taru cikin idanuna, na da'go ina kallon ceiling da'kin zuciyata na mun wani irin nauyi, muna cikin farin cikinmu dare guda komai ya katse mana, bazan ta'ba mantawa da wanan mumunar ranar ba, ranar da akazo aka sanar damu mutuwar iyayenmu sun samu hatsari a hanyarsu ta zuwa Yobe. A ranar duniyar ta tsaya mana cak dani da Ammar. Allah ne kadai yasan meyasa abubuwa suka faru haka.

A hankali zuciyata ta karkata ga kyakyawan attajirin nan Hassan danayi signing contract dashi. Nan take naji jikina yayi bala'in sanyi Ina tunanin abubuwan da suka faru tsakanina dashi kwana biyun nan, duk lokacin daya kusanto ni ina addu'a ga Allah yasa ra'ayinsa akaina ya canza karya ce zai kusanceni ya raba ni da mutuncina, ga kuma irin feelings din da nake ji a game dashi tun farkon haduwar mu har yanzu na kasa saisaita zuciyata, yace mun nan da shekara biyar I'll be free nida kanina, but a ganina shekara biyar is a very long time kuma komai zai iya faruwa tsakakanin wanan lokacin.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now