Chapter 43

1K 66 4
                                    

Hibba

Shiru nayi ina tunanin duba wayar, banso na duba naga sakonsa nace mun bazai samu shigowa ba, can kasan raina nasan ina missing dinsa sosai, yau kwana nawa rabona dana daura idanuna kan kyakyawar fuskarsa, na rasa gane kan feelings dinan da kullum nake kara dilmiya ciki, kullum son Hassan kara horuwa cikin raina yake, a koda yaushe cikin tunaninsa nake, idan na farka bacci bana ganinsa, sai dai naga alamun ya shigo ya fice haka zalika da dare sai na kwanta bacci nakejin shigowarsa, wani sa'in ma baya shigowa sam. Ajiyar zuciya na sauke na cigaba da zamana don nasan idan na duba sakon kilan depression ne zai kamani.

Da wata karar sako ta sake shigowa, naji hankalina ya dan da'ga don ba sabon Hassan bane ya bar mun jerun sakoni haka ba. Na soma tunanin ko Hafsah ce, don bayan shi da ita kadai kawai muke chatting, itace ma tace na bude whatsapp don muna communicating. So from time to time muna dan magana da ita anan.

Mikewa nayi naje na dauko wayar na soma dubawa, a maimakon naga number Hafsa, sai naga sunan Faheema ya bayana cikin wayar. Mamaki ya cikani, ko dayake ba abun mamaki bane don nasha ganinta da Daddynta suna waya, wani sa'in ma harda video calls, Yarinyar tanada wayo sosai, tun ranar da Hassan ya bata waya muka gaisa tace na karba numberta, from time to time takan kirani mu gaisa, yawanci hirar mu bai wuce ta bani labarin school dinsu ba da kuma magunanta tayita tambayata yaushe zanzo na ganta, wani sa'in sai na rasa me zance don bansan makomar relationship dina da mahaifinta ba, Faheema tanada shiga rai sosai, ga hankali, wani sain muna hira da ita kamar da babba nake magana, sai na manta yar yarinya ce yar shekara shida. Yanzu haka ina tsaye, murmushi ne ya bayana a fuskata, na soma kokarin bude sakonin, voice notes na gani a jere na soma playing dinsu, cikin dan karamar muryarta mai dadin sauraro ta soma fa'da mun mun abunda aka dafa zasu ci na dinner, wasu maganar ma bana ganewa sosai saboda gwaranci, dariya na dinga sakewa jin abubuwan da take fadi, naga wasu sakoni sun sake shigowa, hotonta ne ya bayana tana loman abincin dake gabanta, taliya na hango tasha garnishing sosai da dan sauce din naman kaza, sai yoghurt dake gefenta a glass cup, murmushi take tana loman, yanda tayi posing so cute, ga dogon gashinta nan ya zuba mata har gadon bayanta. Sauran hotunan kuma na Magunanta ne, kian da Alfan suma suna cin abincin su.

Dariya naketa faman yi, Faheema kenan, gata ga kian da Alfan dinta, komai nata gwanin ban sha'awa.

Ganin dariyar da naketa faman yi ne yasa Ammar tambayata menene, na karaso ina nuna masa hoton Faheema, yayi shiru ya kura mata ido yana kallonta, "yarinyar Mr Sooraj?"

Nayi saurin gyada masa kai "tana da kyau ko?"

"Sosai ma" ya fa'da yana cigaba da kallon hoton Faheema.
Shiru nayi muna duban hotunan tare can ya da'go yana dubana yace "toh ke bazaki tura mata namu hoton abincin ba?"

Ban kawo wanan tunanina a raina ba amma da Ammar yayi suggesting sai naga hakan yayi na koma gallery na fiddo hotunan abincin dana dauka dazun na tura mata, hade da tura mata voice notes nace abincinta yayi kyau, dama ina kusa muci tare, can ta sake turo da voice notes tana fadin yaushe zanzo na dafa mata wanan kallan abincin nawa tana so, dariya muka sake daga ni har Ammar, muna cikin dariyar sai ga kiranta nan ya shigo, video call.

Ba tare da ba'ta lokaci ba nayi saurin da'gawa kyakyawar fuskarta ya bayana, "Anty Hibba.." ta kira sunana tana murmushi, kamar zata bi screen din ta fito tsabar murna. Nima ina murmushi nace "Faheeema... kin gama cin abincin naki?"

Saurin gyada mun kanta alamun eh, tace "yaushe daddy zai kawoki ki dafa mana biscuit da yakuwa" dariya na sake jin ta kira biski da biscuit.

"Ga kanina Ammar yana gaisheki, yaga hotunan abincinki yace kinyi kyau" na fada ina nuna mata Ammar ta camera

Hannu Ammar ya da'ga mata, itama ta da'ga masa hannu cike da jin kunya tace ta gode. Muka cigaba da hira da ita, ganin hiran namu bana karewa bane nida Faheema yasa Ammar ya kwashe kwanuka yakai kitchen, ya soma wanke abubuwan da muka ci abinci da, yana yi yana bi a hankali saboda rauninsa.

A hakan muka cigaba da hira da Faheema, actually ita taketa faman hiran ina sauraronta, tana bani labarin friends dinta a class da kuma abubuwan da ake koya musu a makaranta, labarin da take fada mun ciki harda abincin data ci yau da safe da kuma rana, wai Baraka ta dafa mata noodles da sausage, ita kuma bata son sausage, haka ta hakura da abincin bata ci ba . Sai kuma ta dauko mun labarin wasan da sukayi ita dasu Kian, wasan boye boye tace yau da rana sun saci hanya sun shiga dakin Hassan sunje sun kwanta sunyi baccinsu akan gadonsa.

Dariya na dinga yi, ina imagining abubuwan da take fadi, sai faman surutu take cike da nishadi ni kuwa inata sauraronta ina dariya. Sai data kai aya tukuna ta dakata, nima na da'an bata labarin wasu abubuwan danayi yau tukuna muka soma sallama, har zan katse wayar naji tace "Anty Hibba kinsan wayata ta ba'ta yau?"

"Wayarki ta ba'ta? Garin ya?" Na tambayeta

"Uhmm.. da safen nan nayita nema ban gani ba, sabuwar wayar da Daddy ya siya mun, inata damuwa banson daddy yayi mun fada na batar da wayan, naje school na dawo muna wasa da su Kian a dakin Daddy saboda nayi missing Daddy sosai...muna cikin wasa naji Kian tanata faman kuka cikin wardrobe na daddy, naje na bude na ganta da wayar tanata faman lasa. Ni kuma Anty Hibba ban kai wayata cikin wardrobe din daddy ba. Bansan ya akayi wayar ta shiga wardrobe din ba. Don ko yau satar hanya mukayi muka shiga dakin saboda inata missing Daddy. Anty Maryam bata ma san mun shiga ba"

Muryarta ne ya soma karaya kamar zatayi kuka tace " ban samu nayi magana da Daddy yau ba... Anty Hibba..kuma kullum sai munyi magana da Daddy..."

"Oh kiyi hakuri Faheema kinji, don't cry please, daddy zai kiraki zuwa anjima kinji ko, karki damu"

Jan majina naji tanayi nan take naji zuciyata tayi mun wani irin nauyi na shiga rarashinta, shiru tayi ta da'an kifa kanta tana goge hawayenta muryarta na rawa tace "inason naga Daddy... ina missing Daddy, inaso ya kawo mun ke gida, kuzo tare kinji ko Anty Hibba"

Tsintar kaina nayi da rashin sanin mezan ce mata don a wanan lokacin zuciyata wani irin zugi take mun, tausayin yarinyar yana ratsa jikina, sam mahaifinta bashida lokacin kansa ballanta na nata, gashi ban ta'ba jin ta ambato mun mahaifiyarta ba,  ko ina take? Ko tana nan da rai oho, ko rabuwa sukayi ban sani ba don Har yau Hassan bai ta'ba dauko mun batunta ba, nima haka ban ta'ba kawo masa zancen ba, ga kuma Faheema data nace tana son ganina, kullum maganarta kenan, Daddynta ya kawo ni, toh yanzu idan mukaje wani matsayi Faheema zata daukeni cikin rayuwarta, ya rayuwarmu zata kaya tsakanina da Mahaifinta.

"Karki damu daddynki ya kusan dawowa  ya ganki kinji ko" na tsinci kaina da fada mata.

"Da gaske? Haka yace miki?"

Cizon lips dina na kasa nayi inq tunani nace "I'm very sure ya kusan dawowa ya ganki Faheema"

"Waye ya kusan dawowa Faheema?" Naji wata murya daga jan bangaren na tambaya.

Shiru nayi ina sauraro

"Daddy zai dawo gida" naji Faheema na fadawa wanda ya mata tambaya. Sai kuma ta juyo tana kallona cike da murna tana fadin "wayyo I'm so excited! Daddy zai dawo"

Dariya nima na sake ganin yanda taketa faman murna,

Muryan ne ya sake katsemu " Faheema kashe wayar nan kizo kiyi wanka, lokacin wankan ki yayi"

"Dan Allah Maryam minti daya bari na gama magana da Anty Hibba"

Wani irin tsawa naji Maryam ta daka mata"Ki kashe wayar nan nace! Ko sai nazo nayi seizing?!"

Ba'ta fuska Faheema tayi kamar zatayi kuka ta juyo tana dubana tace "Anty Hibba, bari na tafi sai na ganki"

Nima cike da sanyin murya nace "toh shikenan Faheema sai kin gani, ki kula da kanki kinji ko?"

Gyada mun kai tayi ha'de da da'n murmushi ta da'ga mun hannu nima na da'ga mata sa'anan ta katse kiran, nayi shiru ina nazari, sam banji dadin yanda Maryam ta yiwa Faheema ihu ba, Yarinyar ma duk ta firgita, sai naji kwata kwata Maryam din bata mun ba daman tun farkon haduwar mu jinina bai hadu' da ita ba, ajiye wayar nayi cike da sanyin jiki na mike na karasa kitchen don na duba Ammar, na sameshi har ya gama wanke kwanukan da muka ci abinci, ko ina yayi fess kamar bayi wani aiki a kitchen din ba, ya juyi yana dubana "har kin gama wayar da kawar taki?"

Na gyada masa kai ina murmushi nace "mun gama"

"Sai naga kamar tayi miki kankanta a kawance ko" Ammar ya fa'da yana dariya.

"ai abokantaka ba sai lallai wanda ka girma ba, idan jinika ya ha'du da mutum shikenan" na fa'da masa

Murmushi kawai yayi muka cigaba da hirarmu, har dare yayi sosai tukuna mukayi sallama, Ammar ya wuce.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now