Hibba
Tunda na bude kofa naga Hassan tsaye fuskarsa a daure kuma babu Ammar zuciyata ta shiga cikin damuwa da tashin hankali, ban san me yaje suka tatauna dashi ba amma inada tabbacin duk yanda akayi Hassan bai amince masa ba, don nasan there's no way Hassan zai yarda yayi releasing dina bayan na rigada nayi signing. so nake na tambayeshi amma zuciyata cike take da fargaban abinda zai biyo baya. Yanzu haka tsaye muke cikin lift bayan mun bar apartment din AK, shiru ne ya ziyarce mu, naga yayi shiru yayi zurfi cikin tunani yana kallon wani gefe, fuskarsa a murtuke daga gani akwai abunda ke damunsa cikin zuciya, a hankali na juyo ina lekan fuskarsa mukayi ido hudu naji zuciyata ta harba da matsanancin karfin gakse, dukda fuskarsa a daure take hakan bai hana tsananin kyaun da Allah yayi masa ya bayana ba, nayi saurin kawar da kaina gefe ina hadiyen abunda naji ya tasomun ina kokarin daidaita feelings dina a hankali naji ya kamo hannuna ya soma murzwa, ganin yanda yayi shiru yana dubana kamar he's lost in thought ya sani tambayarsa
"Are you alright?"
Kallona yayi for a few seconds, kamar akwai abunda yakes so ya fa'di, sai kuma ya canza mind dinsa ya sakar mun lalausar murmushi "yes I am... me kikeso kici? Ya watso mun tambaya
"Ni bana jin yunwa"
"Ban yarda ba, you have to eat something"
Zanyi magana lift din taja ta tsaya yana rike da hannuna muka fito tare cikin tsadadiyar hall din hotel ga baki kota ina sunata shiga dafice, inda aka rubuta restaurant na hotel ya jani muka karasa ciki muka nemi wuri muka zauna yayi mana order, within two minutes aka zo aka jera mana abinci kala kala a gabanmu, tsakuran abincin na soma yi ya kura mun ido ganin yanda duk nabi nayi wani iri, ajiyar zuciya ya sauke ha'de da matsowa kusa dani ya kamo hannuna cikin nashi yana shafawa a hankali yace " Hibba...look at me"
A hankali na dago na dubeshi "Ina so ki fahimci wani abu, the most important thing here is saving your brother and no matter what an agreement is an agreement, be rest assured you and your brother are under our protection as long as you stick to your end of agreement"
Shiru nayi ina sauraronsa da rinanun idona nace "nasan I've signed the agreement amma inason Ammar ya kasance kusa dani, nafiso ina ganinshi nan ne hankalina zaifi kwanciya, please nasan this is not part of the agreement but ka taimaka ka daukar mun wanan alkawarin" na karasa maganar muryata narawa.
Kura mun ido yayi na da'an lokaci kamar yana kokarin battling da wani abu dake cikin zuciyarsa can kuma yace "you'll see him but not now, kinga halin da ake ciki yanzu it's still not safe amma once it's settled you'll see him consistently, kinji ko?"
Mamaki ne ya cikani ganin yanda yake mun magana cikin sigaer rarashi kamar bashi ba, Cike da farin ciki nayi saurin gyada masa kaina.
"Now eat your food" ya karasa yana sakar mun murmushi.
Nima murmushin na sakar masa, maganar daya mun yanzu yasa naji hankalina ya da'an kwanta, na ji sanyi a raina, cokali na dauko na soma cin abincin, at least koba komai zan dinga ganin kanina from time to time, ya dau mun alkawari. Cike da farin ciki na cigaba da cin abincina, na zage naci sosai shi kuwa ya kura mun ido yanata kallona, na lura duk sanda nake cin abinci zai bar duk abunda yakeyi ya kama kallona, as if he's just fascinated by me eating, watching me eat yana bashi nishadi, danaga kallon yayi yawa na janyo abincin na juya masa baya ina facing wani wuri na cigaba da ci.
Dariya naji ya sake, After soma minutes muka tashi da abincin dake gabanmu, tare muka fito nayi hanyar zuwa lift da zai kaini sama wajen Ammar naji ya kamo hannuna muka dauki hanyar zuwa waje
"Ina zamu kuma?" Na watso mashi tambayar
"Shopping" kawai ya bani ansa yana sakar mun murmushin gefen baki
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...