Hibba
By the time dana farka naji jikina ya danyi sauki, ciwon kan ya lafa, karfin jikina ya dan dawo. Duba lokaci nayi naga azhar yayi na sauko daga kan gadon, a hankali na karasa bayi naje na gyara jikina tsap sa'anan na dauro alwalwa na fito na shimfida sallaya, a zaune nayi sallah kamar yanda na saba, ina idarwa na da'ga hannayena ina rokon Allah ina mika masa godiya game da cetona da yayi, ina rokonsa daya da'da karemu daga duk wani sharri dake shirin sake afkuwa cikin rayuwarmu dan darajan son da muke yiwa maikinsa, Hassan ma nasa shi cikin addu'a ina neman masa tsari kuma ina rokon Allah daya saka masa da duk wani alkhair ya mayar masa game da kokarin daya dinga yi a kanmu. Na jima sosai ina addu'a, har wanan tunani tunanin da mafarke mafarken da nakeyi na Kawu Abu na roki Allah daya yaye mun su, ban so ina tunawa da abunda ya sameni. Dole nayi kokari na yakice shi daga cikin rayuwata.
A hankali na mike na koma kan gado, ban gama kwanciya ba sai ga Priya ta bude kofa ta shigo, tana ganina ta karaso cikin sauri tace meyasa na sauko, nace da ita sallah nayi, ta sauke ajiyar zuciya, murmushi na sakar mata cike da jin dadin ganinta sosai muka gaisa ta soma tambayata ya jiki nace da sauki, abincin data ruko ta bude mun, noodles ne an dafata da dan ruwa ruwa cikin wata farar bowl, kwanun mai kyau a gefe kuma tea ne mai kauri cikin mug tazo ta dire mun a gabana tace naci sai ta mun allura nasha magani, nace da ita toh. Tace zata dawo in the next 10 minutes, tana fita na janyo spoon na soma cin abincin, indomin yayi mun dadi sosai don naji taste buds dina sun budu ba kamar jiya da shekaran jiya ba, ina cikin ci naji anyi sallama an turo kofar, Ammar ne ina ganinsa naji wani irin farin ciki na ansa sallamar ina masa murmushi ya karaso na soma tambayarsa ina yaje na farka ban ganshi ba, yace yaje karbo sako ne a wajen AK daga nan ya tsaya yin sallah, nace okay na nuna masa gefen gado nace yazo ya zauna muci abinci, girgiza mun kai yayi yace "ni bazan ci ba kici kayanki"
"meyasa?" Na tambayeshi ina ba'ta rai
"Bana cin abincin marasa lafiya" ya bani ansa yana kallona, dariya muka sake nidashi, ya matso da kujeransa dab dani yana tambayata ya nakeji yanzu, nace mishi da sauki ciwon kan ya lafa.
Ammar ya kasance tare dani har bayan la'asar, munyi sallah muna zaune muna hirar mun, hirar muke amma gabadaya hankalina baya jikina yana kan Hassan, ina tunanin inda yake da kuma abunda yake a wanan lokacin, ina cikin wanan tunanin naji shigowar sako cikin wayata, cikin sauri na duba naga sakonsa ne, wani irin farin ciki ne ya lulubeni na bude na soma karantawa, tambayata yake ya jikina, yana shaida mun cewa zuwa anjima zasu zo su dubani, yace yayi missing dina sosai, he can't wait to see me.
Bakina har kunne sai faman washewa nake ina karanta text dinsa har sai da Ammar dake gefena ya soma gyaran murya, da'gowa nayi ina murmushi naga yana dubana da gefen ido.
"Mr Sooraj ne?" Ya tambayeni
Na gyada masa kai
"Meyace?"
"Cewa yayi zuwa anjima zasu zo su dubani dasu AK"
Ammar yace okay, kasa rike kaina nayi nace "Ammar kasan me?"
"Mene?"
"Hassan yace yana sona"
Zaro ido Ammar yayi "da gaske?"
"Da gaske" na fa'da masa ina gyada kai cike da farin ciki.
Nan take naga shima Ammar fuskarsa ta barke da murmushi "daman na sani, ai na fa'da miki Mr Sooraj yana sonki it's just a matter of time kafun ya fito filli ya furta miki, kowa ya shaida da irin son da yake miki, I'm just glad he's the one Ya'Hibba because Mr Sooraj yanada kirki and he will never hurt you, ko na tafi nasan zuciyata bazata shiga cikin damuwa ba saboda nasan kina tare dashi"
Murmushi na sakar masa nace hakane.
"Kema na tabbata kina sonshi ko Ya'Hibba?"
Gyda masa kai nayi, shi kadai zan iya furtawa haka ba tare da naji shakka ko wani abu ba, Ammar kanina ne kuma tun tasowarmu babu abunda muke boyewa juna nidashi, ban ta'ba zama nayi hiran wani saurayi dashi ba sai akan Hassan, sosai muka saki jiki da juna yana nuna mun farin cikinshi akan son da Mr Sooraj yake mun, nima at the same time yana kokarin kwantar mun da hankali yana bani baki akan dana saki jiki nayi accepting dinshi cikin rayuwata.
Bayan kusan hour guda muna cikin hirar mu mukaji knocking a kofa aka bude, muryar Faheema na fara ji ta shigo a guje tana ihun kiran sunana, "Anty Hibba!!! Anty Hibba" tazo ta fada a jikina ta rungumeni tsam, nima rungumeta nayi cike da farin cikin ganinta ina fa'din "Oyoyo Faheemana"
Daya bayan daya suka fara shigowa, before you know it dakin ya cika da mutane, Jamal, Sadik, AK harda Lukman, Hafsah itama ta karaso cike da farin ciki tazo ta rungumeni, duk muka rungumi juna muna farin ciki, a hankali idanuna suka sauka kan Hassan muka ha'da ido dashi ya kashe mun ido daya yana murmushi, sunkuyar da kaina kasa nayi ina jin kirjina na harbawa cike da matsanancin sonsa, a hankali na dawo da dubana kan Faheema data da'go ta tsaya cak a gefena tanata faman bina da kallo, sosai ta kura wa fuskata ido tana bi da kallo, nan take na Fahimci abunda take kallo, jikina yayi sanyi duk naji wani iri, kilan ma tsoro na ba'ta da waenan raunukan dake kan fuskata.
Tana tsaye tana kallona a hankali naga ta kai yan mitsi mitsin hannunta gefen fuskata tana shafa a hankali tace "akwai ciwo ko? Sannu Anty Hibba...Allah ya kara miki lafiya. Daddy yace kinyi hatsari saboda haka bazaki iya dawowa gida ki zauna tare damu ba, shiyasa kika zauna a asibiti"
A hankali na dago ina duban Hassan, daman abunda ya fa'da mata kenan? Cewa nayi hatsari? Ajiyar zuciyar na sauke don sam bazan so tasan abunda su Kawu Abu suka mun ba, na dawo da dubana gareta ina murmushi na girgiza mata kai nace "karki damu Faheema na samu sauki yanzu, babu wani ciwo dake damuna kinji"
"Kin tabbata Anty Hibba?" Ta tambayeni muryarta na rawa, hawaye naga sun ciko cikin kyawawan idanunta sak irin na ubanta tace "ina jin tsoro Anty Hibba bana son ganinki bakida lfy, ina so naga kin warke, I want you to be fine Anty Hibba" ta karasa maganar tana mika hannayenta allamun tana so ta rungumeni, a hankali na sunkuyo na mika mata hannuna na janyota gam jikina na rungume itama ta rungumeni hawaye na zuba mata ta soma sheshekar kuka, rarashinta na soma yi nace mata ta bar kuka, gani nan ina cikin koshin lafiya babu abunda ya sameni,"babu ciwo Faheema, raunin basu mun zafi, bakiga ina magana ina murmushi ba?"
Shiru tayi tana dubana sa'anan ta gyada mun kanta hawaye na zuba mata shar shar bisa fuskarta tace "zan gayawa Daddy daga yau ya dinga kula dake da kyau saboda karki sake yin wani hatsarin"
Murmushi na sakar mata su Jamal suka sa dariya, na da'go naga Hassan shima Murmushin yake, cigaba da kokarin kwantar mata da hankali nayi, sai danaga hankalinta ya kwanta ta soma murmushi tukuna na dawo da hankali kan sauran dake tsatsaye muka soma gagaisawa suna tambayana ya jiki nace da sauki, sosai naji dadin ganinsu ina musu godiya.
Bayan mun gama gaisawa na dawo da attention dina kan Hafsah, wace duk ta tsareni itama kamar zata mun kuka tana tambayata ya jiki nace da ita da sauki, sai faman bina da kallo take cike da tausayawa, kara rungumeni tayi tace taji tsoro sosai data samu labari, Allah ya tsare ya kiyaye na gaba. Nace da ita Ameen ha'de da mata godiyan zuwan datayi da kuma kula da Faheema data dinga tace bakomai ta janyo wani dan basket data shigo tace ta dan' mun siyaya abubuwan da zan bukata nace meyasa ta wahalar da kanta tace babu komai na karba, godiya sosai nayi mata, muka shiga hira.
Su AK basu wani jima ba suka wuce, Ammar ya bisu don akwai aikin da zai taya AK zaije ya dawo, Hafsah tace zata kasance dani har zuwa anjima ta shiga rokon Lukman daya zo yayi picking dinta zuwa anjima bai ja ba yace zuwa anjima zaizo ya dauketa su wuce, sosai mukaji dadin hakan nida ita, muka cigaba da hiran mu harda Faheema tanata samu dariya. Ta da'ga can gefen dakin Hassan ne tare da brothers dinsa suna discussing kasa kasa, sai dai cikin zancen nasu na danyi picking wasu abubuwa don daga ji magana sukeyi akan mahaifinsu da kuma auren da zaiyi. Na lura duk shiga da fitan nurses cikin dakina idanunsu nakan Hassan da brothers dinsa suna kare musu kallo cike da sha'awa. Ni kaina na lura da hakan ne saboda satan kallonsa da nakeyi, muna ha'da ido dashi sai ya sakar mun murmushi ni kuma nayi saurin dauke kaina.
Not edited
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomansaHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...