Chapter 91

1.4K 87 11
                                    

Hassan

A firgice ta juyo tana dubansa don batayi expecting shigowarsa yanzu ba, daga ita sai towel daure a jikinta da alamu wanka zata shiga, ya tsaya ya tsareta da idanunsa yana kallonta, a hankali yake bin sexy body dinta da kallo tun daga sama har zuwa kasa yana jin wani irin sha'awarta na tasar masa.

Duk tabi tayi tsuru tsuru da ido kamar wacce taga dodo "ka shigo?" Ta tambayeshi muryarta na rawa.

Mikewa yayi daga jinginan da yayi jikin kofar ya soma takowa ina take yake "eh na shigo..." ya fa'da idanunsa kyam akanta, a hankali ya juyo ya dubi Faheema dake kwance tana baccinta hankalinta kwance sa'anan ya dawo da dubansa gareta yana kare mata kallo up and down "wanka zaki shiga?"

Ta gyada masa kanta, ya da'da matsowa kusa da ita "shine baki jirani muyi tare ba?" Ya fada muryarsa kasa kasa.

Cikin sauri ta da'go ta dubeshi " wankan... zamu shiga tare?"

ya da'ga mata gira da'ya " yess.."

"Tabdjin..." ta fa'da tana turo baki "ni kadai zan shiga wanka na"

Dariya ya sake yana girgiza kai "meyasa?...wai har yanzu kunyata kikeji? Ya kamata ace zuwa yanzu fa kin rage wanan kunyar"

Bata ce komai ba ta matsa zata juya masa baya yayi saurin kamo hannunta, ganin zata masa gardama ya dauketa cak sai bayi, suna shiga bayin ya sauketa a hankali sa'anan ya juyo da ita suna fuskantar juna "ki daina jin kunyata nasha fa'da miki, nida ke mun rigada mun zam da'ya yanzu, I'm yours"

Kamar da wasa taga ya soma cire wandonsa ya rage daga shi sai rigar jikinsa da boxers sa'anan ya matso yana kokarin tuge towel din dake jikinta tayi saurin rintse idanunta ta rike gam,

"Menene?"

Ta girgiza masa kanta

"Bakison naga jikinki?"

Ta da'ga masa kai tana narai narai da idanu, "toh meyesa?"

Turo baki ta kumayi "nidai....nidai ina ka rigada kayi wanka?" Ta tambayeshi tana rausayar da kai.

"Uhmm zan sake" ya ba'ta ansa.

Ta bude baki zata sake masa magana ya katseta "shh....just relax okay"

Bata sake cewa komai ba tayi shiru kamar yanda yace, bai sake bin ta kan towel din ba ganin yanda ta rike gam taki sakewa, inda yasan zai sameta ta zama weak a hannunsa ya soma bi, ya kawo fuskarsa  dab da nata suna shakar numfashin juna, a hankali ya matso da fuskarsa ya dawo dai dai saitin kunnenta yana hura mata iskan bakinsa sa'anan ya manna mata hot kiss a wajen, nan take yaji jikinta yayi reacting. Ya soma kissing ko ina a bayan kunnenta har zuwa wuyanta yana lumshe ido ya soma sumbatu "A duk lokacin da zan kasance tare dake nakan tsinci kaina cikin nutsuwa mara misaltuwa, ko fushi nake da zarar na kalli kyakyawar fuskarki sai naji fushin ya kau, you bring me peace Hibba.... and I feel lucky to have you in my life as my wife. Gabadaya ji nake bana tare da wata damuwa da zata durkushe farin cikina muddin ina tare dake" a hankali ya cigaba da ra'da mata dadadden kalamai cikin kunnenta yana kissing dinta, yaji gabadaya ta sake tayi relax a hannunsa tana sauraronsa sai faman lumshe ido takeyi, shima numfashin yake saukewa sama sama, kasa jurewa yayi ya da'go da fuskarta ya ha'de bakinsu wuri da'ya ya soma kissing lips dinta... a hankali yayi encouraging dinta ta bude masa bakinta ya samu nasaran cafko lalausar harshenta, tunda ya samu nasaran cafko lalausar harshenta bai sake sanin inda kwakwalwarsa take ba, illa sake matseta da yayi gam a kirjinsa tare da mata riko mai karfi kamar za'a kwace masa ita. Gabadaya idanunsa sun ka'da sai faman lumshe su yake.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now