Hassan
Fifteen minutes kenan da tashin jirgin su Hibba suna sama, Hassan yaga ko kadan batayi gizao ba, a tunaninsa wanan ne karo na farko data fara hawa jirgi, amma ko kadan bata nuna alamun tsoro ba, no sign of flight fright, sai ma yaga tanata anashuwa abunta, ya lura da ita tunda ya sanar da ita tafiyan nan nasu na zuwa ganin kaninta ta shiga farin ciki, ta sake jiki sosai tare dashi sa'banin kwanakin da suka wuce, suna cire seat belt yaga ta mike ta koma kan cushion dake can gefe tana kallon waje ta window, yanda take abubuwa kamar karamar yarinya yana matukar bashi nishadi. Yanzu haka zaune take ta lankwasa kafa akan kujeran tana faman ciye ciye, blessing ta sake karo mata kayan maku lashe, sai faman ci take babu abunda yasha mata kai.
Sosai Hassan ya zurfafa da kallon Hibba, yana jin wani irin feelings na taso masa, ya lura tunda ta shigo cikin rayuwarsa yan kwanakin nan yana tsintar kansa cikin anashuwa most especially idan yana tare da ita, baya gajiya da kallonta. Ita kuwa ko ajikinta bata ma san yanayi ba, she's so oblivious to his attraction to her.
"Zaka ci?" ta tambayeshi daga inda take zaune acan gefe tana mika masa piece of cake.
Murmushi kawai ya sake yana girgiza mata kai, yaji wayarsa ta soma ringing. Hibba ta mayar da hankalinta kan cake, shi kuwa ya dauko wayar yana dubawa sa'anan ya kara a kunne
"Uhm.. ina jinka"
"har ka dauki hanyar zuwa Abuja kenan?" Yaji muryar Jamal ya doki kunnensa.
Ajiyar zuciya Hassan ya sauke yana mamakin yanda Jamal yasan da tafiyan nasa, tunda bai sanar da kowa ba. shi kanshi bai shiryawa tafiyar ba sai da Hibba tasa shi a gaba akan sai lallai ya kaita gun Ammar tukuna ya kira Ak ya sanar dashi zuwansa da ita. Bayan Ak babu wanda yasan da wanan tafiyan nasa, harta Hibban ma bata sani ba sai a yau.
"Eh toh, sai akayi yaya?" ya fa'da cikin wayar yana duban Hibba data zurfafa sai faman cin cake dinta takeyi tana kurban juice
"Nothing kawai na kira ne na tabbatar ko da gaske ne ka dauki yar' budurwar taka zaka kaita taga kaninta" Jamal ya fa'da yana dariya cikin wayar, Hassan ya ku'le
"Toh ina ruwanka? Matslata ce ai ba taka ba"
Dariya Jamal ya kuma sakewa, " so matsalarka ce yanzu? Na zata she's just a contract to you?"
Ajiyar zuciya Hassan ya sauke. Da farko dai ya dauketa a matsayin contract dinsa nothing more amma yanzu abubuwa sun soma canza masa yana ganinta in a different light, she's definitely not a contract to him, but a problem? Yes. Ta rigada ta zama matsalarsa yanzu wanda shi kadai zai iya magance.
Yanzu abunda yafi da'ga masa hankali shine yanda yake matukar jin dadin kasancewa tare da ita, in more ways than he can imagine, a yanzu haka sam baya son abunda zai nesanta shi da ita, bama don ya ta'ba jikinta ba, a'a, kallonta kawai yana matukar kawo masa nishadi. Shidai yasan bayan rabuwarsa da Afrah yasha damawa da mata kala kala amma iyakacinsa kenan, baya ta'ba barin wani abu ya shiga tsakaninsa dasu, he only invites them when he's bored, rayuwarsa is always on the fast lane, fast money, fast cars, fast women.
Hibba kuma on the other hand she's just different, Ita daban ce, she doesn't fit into his world and kuma matsalace gareshi, matsla kuma babba.
"Yep she's a problem" ya fa'da wa Jamal yana duban Hibba wace har ta gama ciye ciyen nata ta dauko wata handbook data samu cikin jirgin tana karantawa.
Dariya Jamal ya kuma sakewa yace "ko zamu iya sharing wanan matsalar?"
Nan take Hassan ya ba'ta fuska jin abunda jamal yace "karka kuskura Jamal, kaje can ka samu ta'ka matsalar, amma banda wanan, this particular one is off limits" ya fa'da yana hucci, yasan Jamal wasa yakeyi, amma he couldn't help it, kawai ji yayi he needs to let him know Hibba is off limits, she belongs to him alone. A da sun sha sharing yan mata tsakaninsu amma yanzu no way... ba dai Hibban'sa ba.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...