Hajjo
Bangarensu Hajjo kuwa tunda suka gano suka tabbatar wa kansu cewa eh da gaske ne Maryam ta tafi, kuma tafiya har abada wanda bazasu kara ganinta hankalinsu ya dawo musu, sai dai jin duniyar suke kamar basu ke cikinta ba, tun a ranar da aka musu comfirming ta cika Adda ta dawo kamar wata zarariya, da kyar aka kwasheta aka fitar daga asibitin, Hajjo kuka, Adda kuka suka dawo kamar wasu ta'babu, sunyi matukar girgiza ba kadan ba, a lokacin da Maryam ta cika ba jima ba aka musu releasing gawar aka dawo da ita gida aka suturtata aka kaita makwancinta. Mallam Gidado har cikin ransa yaji mutuwar Maryam, abun ya girgiza shi sosai, ana sadakan uku ya tattara ina shi ya bar gidan basu kara sanya shi a ido ba har yanzu, komai ya lalace musu a gidan, yan layi da unguwa ma basu barsu ba, don suna ganin laifinsu ne mutuwar Maryam, duk inda suka shiga yi dasu akeyi don babu wanda bai san irin rayuwar data daukar kanta ba, shekarn jiya akayi sadakan arba'in, Addan tana kwance yau jiki yayi kyau gobe kuma yaki, Hajjo ce take samu takeyin girki tana kawo musu gida don abincin da zasu ci ma a gidan zaune yake da gindinsa. Yauma data shigo ta tadda Adda kwance hankalinta ya kara tashi "Adda ko zamuje asibiti ne, jikin nan fa yaki kuma kinki a kaiki a dubaki"
Da kyar Adda ta bude baki tace "Hajjo ki barni kawai... babu wani asibitin da zanje, in lokacina yayi Allah ya dauki raina a hakan, don hakika na cuci kaina kuma na cuce ku yayan dana haifa, ban daura ku kan hanya mai kyau ba, yanzu yau ina Maryam? son raina ya jawo mun na rasata na rasa komai, mahaifinku ma ya gudu ya barmu, rayuwa yanzu batada wani amfani garemu".
Cikin sheshekar kuka Hajjo ta soma fa'din "dan girman Allah Adda ki daina fa'din haka, rayuwa bata lalace mana ba, har yanzu munada sauran hope, kinada ni ga sauran kanina, Maryam lokacinta ne yayi addu'a kawai zamu cigaba da mata Allah yakai haske makwancinta, kiyi hakuri ki daina wanan kukan da tunanin Adda, idan na rasa ki kema bansan inda zan sa kaina ba..."
Kuka sosai Hajjo takeyi, sai datayi mai isarta tukuna, tana zaune a gidan har yamma ya gabato ta dan tayasu aiki a gidan kafun ta koma gida kar mai gida ya dawo bai tadda ta ba. Sai dai cikin wanan satin wani abun alajbi ne ya sameta, ta tashi da safe taji gabadaya jikinta na mata ciwo, abun kamar wasa har zuwa yamma ta kasa tsinana komai, haka dai tayita jan jiki har zuwa cikin dare ta tashi da ciwon kafa, tun daga kan yatsunta take jin ciwon nan har cikin kwakwalwarta, da safe kafan nan ya kumbura timm, hankalin Alhaji ya tashi nan da nan yayi rushing dinta zuwa asibiti, likitoci dai suka duba ba'aga komai can zuwa anjima kuma ciwon kafan ya lafa, kumburin ma ya sauka haka suka dawo gida, hankalin Hajjo yayi mugun mugun tashi, bokanta Ojakinwa ne ya fado mata ta kirashi tana sanar dashi gashi gashi yanda take jin jikinta, yace ta dan bashi lokaci zai kirata, can bayan 10minutes ya kuma kiranta ya shaida mata wanan ciwon da take fama dashi ba kowa bane illa kishiyarta, tayi mata barbadi kuma ta taka, shiyasa ko da aka je asibiti ba gano komai ba, hankalinta ya tashi ta tambayeshi yanzu ya za'ayi yace ta shirya tazo, akwai maganin da zai ba'ta tayi amfani dashi, idan ita kishiyar tasan wata bata san wata ba, yace zaiyi mata aikin da kafarta zata fice ta bar mata gidan.
Hajjo tace babu komai insha Allah zata shirya tazo, washe gari Hajjo ta shirya zuwa wajen Ojakinwa sai dai kash tana cikin driving kafar ta sake rike mata, gashi tana tuki on high speed, kafar ta rike sosai tama kasa taka brake, wani yaro karami akala bazai wuce shekara bakwai zuwa takwas ba yazo zai tsalaka titi a wanan lokacin bai ankara ba da gudun nan tazo ta haye kansa, har lahira ta aika dashi motar tayi daji ta bugu da bishiya, sai dai ita babu abunda ya sameta illa ciwon data ji a goshinta jini nata zuba, da kyar ta samu ta fito daga motar, yan kauyen nan suka fifito akayi caaa akanta, aka ririketa iyayen yaron sai kuka suka ce bazasu yarda ba ta kashe musu da', Hajjo tana kuka tana rokonsu amma suka ce ina, police station suka karasa da ita aka kulle. Tace ko nawa ne su fa'da zata biya, abun ya kara kona nusu rai tana kokarin ha'de rai da aka rasa da kudi, charges dai aka manna mata da overspeeding, tana kokarin musu bayani ba isashen lafiya bane da ita amma ko a jikinsu, tana nan kulle har magana yaje kunnen alhaji, daman bata sanar dashi fitanta ba, da kyar dai ya samu aka kashe wutan case din, sai daya bawa iayyen yaron makudan kudi yace suyi hakuri police ma yayi settling dinsu, da case din ya lafa ya rubuta mata takadadar saki yace ta tafi ya sallameta bazai iya cigaba da zama da ita ba tana janyo mishi bala'i all the time, tana kuka tana magiya amma ko a jikinsa, haka ta koma gida, kishiyarta kam kamar zata zuba ruwa a kasa tasha, finally tayi waje da ita.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...