Hibba
A firgice nake binsa da kallo, kyakyawar fuskarsa daure murtuk kamar bai taba dariya ba. cigaba da kallonsa nake a mugun firgice, tunani kala kala na mun yawo aka, badai mutumin dana gani kan hanya bane dazun? Toh meya kawoshi nan gidan? Tambayar dana shiga yiwa kaina kenan babu answer. Cika da nutsuwa da izza ya soma takowa har yazo ya tsaya gabana, wani irin kyarma jikina keyi har lokacin bugun kirjina bai saisaitaba naji yace "Hibba Abdullahi?"
Kallonsa kawai nakeyi na kasa furta koda kalma daya, a hankali naga ya kuma matsoni kamar zai shige jikina, ya sunkuya daidai saitin fuskata, saurin sunkuyar da kaina nayi zuciyata cike da matsanancin tsoro, so nake na matsa baya daga kusancin da yayi dani amma naji kafafuna sun ka'ge, a hankali naji yasa hannunsa a ha'bata ya da'go da fusakata muna kallon juna, fararen idanunsa masu matukar kyau da haske kyam a kaina, sai faman bina da kallo yake, can sai naji yace
"Look at you, yar mitsila dake, ki gaya mun a gidan uban wa zaki samo mun million da'ri na?!"
Maganarsa tamkar dafi naji har cikin kawon zuciyata, nan take kwakwalwata ta shiga cikin hargitsi, badai wanan mutumin bane yake rike da Ammar. Saurin jada baya nayi, muryata na rawa nace "Kaine kake rike da kanina Ammar?"
Shiru yayi na yan sekoni yana dubana daga bisani ya girgiza kai "kaninki dashi da abokanansa na da'ga musu hannu, sun samu nasaran cutata million dari" murmushi ya sake yana cigaba da girgiza kai "trust me sunyi ganganci da suka aikata hakan, I'm not the type of person to be messed with"
Saurin hadiye abunda naji ya tare mun makoshi nayi nace "dan Allah dan Annabi karka masa komai, ko meye zanyi duk inda kudi yake zan nemo amma karku ta'ba lafiyar kanina, shi kadai gareni".
"Shi kadai gareki? Iyayenku fa?"
Nan take naji wani iri, jin ya ambato iyayenmu nace "iyayenmu sun rasu tun muna kanana, ni kadai Ammar yakeda"
Da'ga mun gira daya yayi kamar bai yarda da abunda na fa'di ba, kamar irin ya saba jin irin wanan labarin, abun yayi mun ciwo amma nayi kokari na dane
Shiru yayi yana bina da kallo daga bisani yace "kince ko meye zaki iya yi?"
Saurin gyada masa kai nayi a raina ina fa'din ko wani aiki aka sani zanyi indai zan samu na kubutar da Ammar.
"come with me" ya fa'da, Bai jira yaji mezance ba ya juya ya soma tafiya. Jikina na ba'ri nabi bayansa. Wani office ya kaini mai bala'in girma, a hankali na soma bin ko ina da kallo, kujeru ne da wata katuwar table tsakani, sai wasu na'urori da ban san sunayensu ba, sanyin Ac ne ya karade ko ina, ga wani irin sirritacen kamshi na musamman dake tashi, irin kamshin jikinsa. Wuri ya samu ya zauna yana fuskantata, ina tsaye ina dubansa sai faman kad'uwa nake yayi mun nuni da kujera "sit down".
Zama nayi ina fuskantarsa kaina a sunkuye , daga inda yake zaune inajin yanda idanunsa ke yawo a sassan jikina, tun daga fuskata har zuwa kan kirjina, ina ganin inda idanunsa suka tsaya nayi saurin gyara hijab dina, duk nabi na takura a wajen, sosai ya zurfafa da kallona munfi minti biyar a hakan daga bisani naji yace
"So.. kince zaki iya yin komai don ayi releasing dan'uwanki, the closing date is friday this week, in zaki iya kawo mana million da'ri cash, your brother is free"
Kirjina ne ya shiga harbawa da karfin gaske, ranar juma'a? "Idan ban samu na kawo kafun lokacin bafa" na tambayeshi ina zaro ido hankalina a mugun tashe, ina yakeso na samo masa million da'ri cikin sati daya? Ko zan shekara dubu ina wanke wanke bazan ta'ba tattara masa wanan kudin ba.
Murmushin gefen baki ya sake ya saukar da idanunsa zuwa jikina yana bina da kallo sa'anan yace "zaki samu". hade da mikewa daga inda yake zaune yazo ya zauna a gefena, har muna iya jin dumin jikin juna, sanyayen kamshin jikinsa ya karadeni, hannunsa naji yakai gefen kumatuna ya soma shafa a hankali, Wani irin zirrrr naji a jikina na mike cikin sauri kirjina na harbawa da karfin gaske, kallon juna muke, munfi minti biyu a hakan daga bisani naji yace
"Million da'ri... shekara biyar"
"mene?" Na tambayeshi jikina na ba'ri
Mikewa yayi daga inda yake zaune ya zube duka hanayensa cikin aljihu ya soma zarya "100 million, five years.... it's a contract".
Kallonshi nake cike da rashin fahimta, zuciyata na bugawa da karfin gaske "wani contract kenan?"
"The one I'm offering you" ya fada yana kare mun kallo "interested?"
Shiru nayi ina dubansa tunani kala kala na mun yawo aka, yana nufin shekara biyar, million dari, za'a sako mun kanina?
"Wani irin aiki kenan kake so na muku?"
Bai ce komai ba naga ya sake kallon jikina, nan take na da'go me yake nufi, wani irin zallan baccin rai ne naji ya ziyarceni, badai so yake na bashi jikina ba? Wani irin kallo na watsa mishi, nace "daman haka halinku yake?.. Toh bari kaji na gaya maka, ni ba irin kallan wanan matan bane, bazan ta'ba saida jikina ba, kuma ka rubuta ka ajiye, jumma'a insha Allah zanyi kokari na samo maka kudinka na kawo maka, duk inda kudi yake zan nemo". Ina gama fa'din haka na juya a fusace nayi hanyar kofa, naji taku a bayana anzo an fincikoni da karfin gaske an manna da jikin kofa, kamar zai shige jikina naji fuskarsa dab da nawa, numfashi nake fitar wa a mugun firgice ina kyafta ido, kasa yayi da idanunsa suka sauka kan lips d'ina kana ya lumshe su a hankali yakai fuskarsa daidai saitin wuyana yana shakar kamshin jikina naji ya rada mun cikin kunne "where do you think you're going?! I just gave you an offer, ki zauna kiyi nazari akai Hibba, shekara biyar, million da'ri and your brother is free. You have until friday morning". Ya karasa maganar hade da ruko kugu na ya matso ni jikinsa, lumshe ido yayi ya sunkuyar da kansa kasa ya kamo lips dina na kasa ya ciza a hankali sa'anan ya sake ya da'go yana duban fuskata.
shock nayi jin abunda yayi mun, gabadaya tunanina ya kwance mun, tunda nake ban ta'ba tsintar kaina cikin irin wanan yanayin ba, ban ta'ba jin jikina yayi reacting game da wani da' namiji ba kamar yanda nakeji a yanzu haka, nan take na soma kaduwa na kasa koda kwakwaran motsi, shi ko naga ko a jikinsa, kamar baiyi komai ba ila ma murmushin daya sakar mun dake kara kayattar da kyakywar fuskarsa
"me kike jira" naji ya tambayeni ko har kinyi deciding ne?" Ya karasa yana shafa fuskata, sai a lokacin hankali na ya dawo jikina nayi saurin girgiza masa kai ina ja da baya.
Wani irin kallo naga ya watsa mun, cikin kwayar idanunsa naga kamar yana fighting da abu yana kokarin ri'ke kansa ya rintsa idanunsa "toh idan ba so kikeyi nayi abunda zakiyi regretting ba, leave".
Ina jin ya fa'di haka na juya cikin sauri Allah yasa jakata na hannuna na soma kokarin bude kofa naji a rufe gam, a hankali na juyo muryata na rawa nace "ka danne kofar"
Kallona yayi na yan sekoni kamar yana so yace wani abu sai kuma ya fasa ya da'ga kamar baiyi niyan yin hakan ba, ina ganin ya da'ga cikin sauri na bu'de na fita a guje idanuna sun cika da ruwan hawaye, ban tsaya ko ina ba sai dana ga kaina a waje.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...