Nasan nayi babban kuskure dana bar Ammar yayi tafiyan nan zuwa Lagos shi kadai. Tun ranar daya dauko mun maganar yanaso ya tafi gabadaya hankalina ya kasa kwanciya, I knew it was a big mistake.
"Kinga Ya' Hibba, Lagos garin nema ne, garin hustling ne, ana samu sosai, yawanci abokanai na da suke can suna bani labari, sunyi mun alkawari they'll find me a good one, insha Allah idan naje zan samu abun yi, na gaji da zaman banzan nan da nakeyi a gida". Ya fa'da mun a ranar da yake shirin tafiyarsa.
Kallonsa kawai nakeyi a ranar, a good one to Ammar means ko wani aiki da bazai bukaci ya kawo takardun makaranta ba tunda bashida degree, bazan musanta ba tunda nima d'in ban samu nayi karatun ba, iya secondary school level muka tsaya. Dan' aikin boyi boyi da nakeyi ina wanke wanke a restaurant shine nake da'an samu mu rufawa junan mu asiri amma it's never enough. Tun muna yara Ammar yakeda burin ya zama da'an kasuwa, da babban company mutane na aiki karkashinsa. Ni kuma burina bai wuce koyarwa ba, inaso na zama mallamar makaranta. Mun dage sosai da karatun mu amma lokaci guda komai ya katse, abubuwa suka canza muka fada cikin kunci da wahalan rayuwa.
"Idan na samu naje Lagos na samu aiki mai kyau kin huta da aikin wahalar kenan, ku'di bazai ta'ba yanke mana ba, daga nan ma ki samu ki rabu da wanan yar'iskan madam dinki da batada mutunci"
"Aikin wahala" na fada can kasan raina ina kallon waje ta window moton da nake zaune ciki. Tunda na zaune a motar na kasa dauke idanuna daga waje, tunani kala kala na mun yawo aka, inata kallon daji da garurukan da muketa faman wucewa. Allah Allah nake mu isa garin Lagos, mun dauko hanya tun jiya da safe daga Maiduguri har yanzu bamu kai ba, nayi zaman har na gaji, ga yunwa daya sani a gaba, rabona da abinci tun jiya gashi babu isashen kudi a hanuna. Motar mu ta tsaya wurin cin abinci, kowa ya sauka neman abunda zai ci amma banda ni tunda banida isashen kudi. Daga ni sai dubu biyu, kuma bansan me zanje na tarar ba shiyasa nake taka tsantsan, mutumin dake zaune kusa dani a mota yana dawowa naga ya miko mun gala, kin karba nayi nace mishi nagode saboda ina tsoro amma yayi mun yaren mu cikin harshen Babur yace mun inyi hakuri na karba. Godiya nayi mishi na karbi galan. Toh shine a cikina har yanzu.
Ina zaune, zuciyata cike da fargaba, ban ta'ba zuwa garin Lagos ba, idan na isa ma ta ina zan fara? Abunda ya yafi damuna ma shine irin mutanen da zanje na tadda, wani irin mutane Ammar yaje yake mu'amala da har ya fada cikin wanan halin? Tambayar da naketa yiwa kaina kenan na kasa samun ansa. Hawaye masu zafi suka zubo mun, meyasa na barshi yayi tafiyan nan? Meyasa ban tsawatar masa ba daya nace sai lallai ya tafi, Ammar yaro ne sosai bashida wayon da zai iya da garin Lagos, duka duka shekarunsa nawa, iyayenmu asalin yan Biu ne amma a cikin garin Maiduguri aka haife mu muka girma muka taso, gwanda ni na ta'ba zuwa wasu garukan irinsu kano da Jigawa amma Ammar bai ta'ba barin garin Maiduguri ba, duk wayonsa anan yayi. Abokanansa ne kadai suka tafi garin Lagos suketa faman rinjayansa, har shima ya yanke shawaran tafiya can. Ammar kanina ne wanda muke uwa da'ya uba da'ya, shi kadai ne ya rage mun a duniya, tunda iyayen mu suka rasu muke rike da juna, haka muka taso cikin kunci da wahalar rayuwa. Daga ni har shi babu irin wahalar da bamu sha ba, gashi na barshi ya tafi yaje ya fa'da hannun marasa imani, Allah kadai yasan me zasu masa da suka kamashi yanzu.
Na tuna ranan dana samu wanan mumunar sakon, ina zaune a daki na dawo daga aikin wanke wanke na kenan, kiranshi ya shigo mun waya, cikin sauri na da'ga don yau kwanan mu biyu kenan bamuyi waya ba, ina da'gawa naji muryarsa wani iri, nan take hankalina ya tashi, yana kokarin mun bayani naji kiran ya katse, cikin sauri na sake kokarin kiranshi, naji sa'ko ya shigo mun a waya da wata bakuwar number, nayi saurin budewa na soma karantawa kamar haka
"Kaninki Ammar has done a very unwise thing. Dashi da abokanansa sunyi amfani da kudina sunyi losing over a 100 million a ca'can da sukayi. He's under our protection yanzu, negotiation between us is prudent and we demand your presence here immediately if not something may happen to him".
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...