Hibba
Tunda muka baro gida naketa faman kokari kawowa zuciyata nutsuwa na mantar da kaina abunda Maryam tayi amma naji na kasa, damuwa fal a cikin raina, musamman ma yanda naga take treating Faheema ya da'ga mun hankali, na daukar wa kaina alwashin zamu zauna muyi maganar da Hassan na fahimtar dashi yanda matarnan take yiwa yar'sa a bayan idonsa, a gabansa ne kadai take nunawa tana sonta, ina cikin wanan tunanin a hankali na juyo ina dubansa, tunda muka shigo bai ce komai ba ya cigaba da driving yayi zurfi cikin tunani, Faheema ce taketa kokarin jana da hira na dawo da hankalina gareta har muka karasa cinema, wani sabon Animation daya fito Raya and the last dragon ake nunawa, Faheema tana son cartoon din sosai, nima haka inason kallon cartoon tun ban kai haka ba, Hassan dai bai damu nasan kawai ya biye mana naga ya ciro wayarsa yana latsawa, Faheema ce take ta'bo shi from time to time tana nuna masa idan wani abu ya faru, a hankali nake jin saukar hannunsa cikin nawa yana shafawa from time to time, jin hannunsa cikin nawa yasa naji hankalina ya dan' kwanta, muka zauna muka kalla kamar karya kare.
Muna gama kallon muka fito daga cinema muka sake daukar hanyar zuwa La Manga Luxury Beach villa a Lagos Island, Allah Allah nake mu karasa beach din, ban ta'ba ganin ruwan teku ba, itama Faheema sai tayani murna takeyi. Within 40 minutes muka iso wajen saboda traffic da muka dan tadda a hanya, muna shiga hanyar da zai sada mu da wajen na fara baza ido ina bawa idanuna abinci, sai naji tamkar bana kasar Nigeria don wurin ya hadu fiye ga tunanina, daga gate aka fara da'gawa Hassan hannu cike da gimamwa muka karasa ciki, muna karasa shiga cikin resort din kujeru ne an shimfidasu cikin rumfuna, ga carpet grass ta ko ina sai dan pools kashi kashi dayayi surrounding wajen, driving muka cigaba dayi muna wuce wuri shakatawan har muka soma isowa kan yashi ga bishiyoyin kwakwa kwance ta ko ina da, sai a lokacin naga ruwan tekun ya bayana, baki na sake ina bin wurin da kallo, na jima ina ganin ruwan a tv, ko a hotuna amma ganinsa a zahiri ya wuce expectations dina, wani irin excitement ne naji ya ziyarci duk ilahirin jikina, ga wani irin fresh iska daketa faman busowa ai bansan sanda na kamo hannun Faheema ma ba muka fito daga cikin motar muka karasa a guje kan yashin, Hassan shima ya fito yana biye damu a baya, sai faman kyalkyalewa da dariya muke cike da farin ciki muka tsaya gab da bakin ruwan daketa faman tashi yana sauka, na ruko Faheema nace mu karasa cikin ruwan tayi saurin kankameni tana girgiza tana dariya tace "a'a Anty Hibba, tsoro nakeji"
Dariya na soma mata ganin yanda ta kankameni, Muna tsaye ruwan yazo ya riskemu, Faheema tasa kara at the same time tana kyalkyalewa da dariya, nayi saurin rukota, kafafunmu kawai ruwan ya ta'ba sa'anan yaja da baya, iskan daketa faman kadawa ne yazo ta direction dinmu from nowhere naji ya dauke gyalen dana yafa a kaina gashin kaina ya bayana, a tsorace na waigo naga iskan ya kada gyalen zuwa inda Hassan yake tsaye yana kallonmu, cikin hikkima kuwa ya cafke gyalen ba tare da ba'ta lokaci ba ya karaso cikin sauri ya tsaya gabana ya sanya mun gyalen, yana gyara mun zamansa a kaina, yana gamawa naga ya soma waige waige ko wani ya gani amma babu kowa daga mu sai wasu turawa da da'daikun bakaken fata a wajen, kowa yana minding business dinsa, sai a lokacin naga ya sauke ajiyar zuciya ya kamo hannuna cikin nasa yana kara matso dani kusa dashi, wani irin kunya ne ya lullubeni nayi saurin sunkuyar da kaina kasa, Faheema ta karaso wajensa tana fa'din zata hau lillo don akwai wajen wasan yara da aka ware kan yashin, already ma ga wasu yara a ciki sunata faman wasan su.
Bai musanta ba ya dauketa cak muka karasa wajen lillon, mai kula da yaran wajen idan suna wasa yazo ya tarbe mu, Hassan ya biya za'a shiga da Faheema ta kamo hannuna tace mu shiga tare, na girgiza mata kaina ina dariya nace yara ne kadai ake bari su shiga Faheema, ta bari idan anzo kan na manyan sai mu shiga tare, da wayo da dabbara muka samu ta shiga ita kadai, nida Hassan muka karasa cikin rumfa muka zauna, daga inda muke zaune muna iya hango Faheema tana wasa cikin yaran. Tunanin Faheema da kuma farin cikin da take ciki a yanzu yasa na tunasar wa kaina na yiwa Hassan magana akan yanda Maryam take treating dinta, shiru nayi ina nazari ina tunanin yanda zan bullo masa da maganar, a hankali nayi gyaran murya na kira sunansa, ya kafeni da sexy eyes dinsa "uhmm...what is it?"
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomansaHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...