Chapter 29

1K 72 0
                                    

Hibba

Lokacin danayi sallama da Ammar a jiya, har ina mishi addu'an Allah ya tsare, ban ta'ba kawowa a raina cewa something might happened to him ba, nayi mishi sallama with the hope of I'm going to see him again tomorrow... "ya Allah karka sa wani abu ya faru da kanina" na fa'da can kasan raina ina jin hawaye na taruwa mun cikin idanu har na karaso cikin parlourn  na tadda AK da Hassan tsaye wajen window suna magana kasa kasa, fuskarsu babu walwala, they looked so serious. Idanuna suka sauka kan Hassan dake sanye cikin suit fuskarsa a daure tamau kamar bai ta'ba dariya ba, he looked ready to kill, jikina ya sake daukan kyarma don I could perceive the same ruthless and threatening aura from Ak, they both looked agitated.

"Hassan..." na kira sunansa daga inda nake tsaye muryata na rawa.

Tare suka juyo suna dubana, daga gani basu so shigowata ba yanzu cikin parlourn don ya nuna a fuskarsu musamman Hassan don dubana yake da wani irin expression a fuskarasa da ban ta'ba gani ba, irin expression dake sa duk wanda ya daura idanunsa a kansa kadawa, ni kaina wani irin kyarma jikina yakeyi ganin irin kallon da yake bina dashi, amma na daure na danne zuciyata na soma takowa har inda suke, na marairace fuska ina dubansa nace "naji kuna maganar kanina...meya sameshi?"

Daga inda nake tsaye ina iya hango AK ta gefen idona shima ya juyo yana kallon Hassan yana jiran yaji ansar da zai bani.

As usual, Kai tsaye ya bani ansa bai tsyaa mun wani kwana kwana ba yace "he's missing"

Cak na tsaya ina jin yanda kirjina ya shiga bugawa kamar zai tsage ya fito tsabar tashin hankali na shiga furta kalmar "Innalillahi wa ina ilaihi raji'un", ji nake tamkar zan yanke jiki na fa'di a wajen "how is he missing, jiya da dare nayi sallama dashi taya zaku ce mun he's missing? dan Allah ku taimaka ku fada mun inda yake, su waye suka daukeshi..a ina ya zama missing?" Duk nabi na rude hawaye na zuba mun.

Saurin janyo ni Hassan yayi ya rike gam, yasa hannunsa na dama yana shafar fuskata yana kallon cikin kwayar idanuna yace "we're not sure yet, but we're looking for him, now stop worrying yourself and go back to sleep"

Kuka na fashe dashi, ina girgiza kai, taya zai ce mun na koma na kwanta bayan kanina an sace shi Allah kadai yasan halin da yake ciki! Na d'go ina dubansu "dan Allah ku taimaka ku nemo mun kanina idan wani abu ya sameshi bansan inda zansa kaina ba, ku taimaka ku nemo mun shi shi kadai ya rage mun, he's the only family I have left..." kuka nake sosai ina magana cike da dagin murya, duk nabi na birkice musu a wajen sai da Hassan ya kamo ni tukuna ya janyo ni jikinsa ya kwantar bisa fafadan kirjinsa yana kokarin rarashina "shhh it's okay... you need to calm down nothing is going to happen to him, insha Allah everything is going to be alright, zamu dawo dashi duk inda yake, I give you my word"

Jikina na ba'ari na kamo hannunsa cikin nawa ina fa'din "ka dau alkawari? Dan Allah kamun alkawari zaku dawo mun da da'anuwana cikin koshin lafiya" na karasa maganar muryata na rawa ina kallonshi cike da tsananin tashin hankali.

Murmushi ya kirkiro yana shafan gefen fuskata yace "I promise.. now be a good girl ki koma ciki, I want to discuss some things with AK"

Bance dashi komai ba na juya na koma daki cikin sauri hawaye na zuba mun, inajin yanda zuciyata ke bugawa, naje na tsuguna wajen gado na kife kaina ina wani irin kuka mai tsuma rai "Ya Allah kasa kanina yana cikin koshin lafiya duk inda yake, ya Allah kayi gagawan bayanar mun dashi, ya Allah karaka sa makiyan nan su samu galabar illatar dashi, ya illahi ya rabbi... sai faman kwararo nakeyi ina kaiwa Allah kukana. Idan wani abu ya sami Ammar I wouldn't be able to handle it, shi kadaine dan'uwan daya rage mun wanda nake bala'in so, zuciyata bazata iya juriyar rashinsa ba, without him I'm alone in this cold world.

Ina cikin wanan kukan naji kofar ta budu Hassan ya karaso inda nake ya zauna ya da'go ni yana kallon fuskata daya ba'ce da ruwan hawaye "nace ya isa ki daina kukan haka, Insha Allah zai bayana duk inda yake, we're going to look for him. I'm leaving to sort things out" ya karasa maganar yana share hawayena.

Kallonshi kawai nakeyi na kasa furta komai, ina jin yanda zuciyata ke mun wani irin lugudi, yanda yake kokarin kwantar mun da hankali har yana fa'din zai fita yaje ya nemo mun kanina, nasan it's none of his business idan yaga dama he won't even bother since I'm just his mistress, and Ammar is nothing to them ko wani abu ya sameshi it's not a bother for them, but still yana so ya taimaka mana. Wani irin sanyi na da'an ji a raina at least inada hope, ban ta'ba jin farin cikin samun Hassan cikin rayuwata ba kamar na yau, the fact that I have him to lean onto in times like this is a blessing for me.

"Will you be alright?" Naji ya tambayeni

Zira harshena nayi ina lasan lips dina na kasa daya bushe na gyada masa kai, so nake nace masa zan bisu amma nasan ba abu mai yuwa bane, bazai amince ba.
Nayi kokari na danne zuciyata, dole na daure na mike tsaye na cigaba da addu'a har suje su dawo Allah ya basu nasaran dawo mun da kanina duk inda yake.

Saukan soft lips dinsa bisa goshina naji yana kaimun kiss yace "good girl... I'll be back soon"

Mikewa yayi ya dau hanyar fita ina jin yanda zuciyata ke mun nauyi.

"Allah ya bada nasara... Allah ya bayanar dashi, kuma Allah ya tsare" na fa'da muryata na rawa.

Juyowa yayi yana dubana ya gyada mun kai ha'de da sakar mun murmushi yace Ameen sa'anan ya juya ya fita ya barni tsaye a wajen cikin tashin hankali, bayan fitan Hassan kusan 20 minutes na kasa tsaye na kasa zaune sai faman zarya nake a dakin, tunani nake ko nima na fita naje nemansa da kaina amma nasan ko naje it will be useless, ta ina zan fara? Ga gari ba kadan ba, bayi na fada cikin sauri na dauro alwala nazo na fuskanci ubangijina na cigaba da kai masa kukana.

Not edited.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now