Hibba
Gabadaya daren jiya ban samu bacci ba, yanda naga rana haka naga dare, har yanzu jin abun nake kamar a mafarki, zuciyata na mun replaying abunda duk ya faru, nayi kukan har na gode Allah. Idanuna duk sun kumbura, tunda na kori Ammar nake faman kuka har asuba aka kira sallah na sauko daga kan gado na shiga bayi, da kyar a dadafe nayi alwala na fito don wani irin sara kaina kemun, har wani dishi dishi nake gani, nazo na tadda sallah, ina cikin sallah ma kuka na dinga yi, ina kaiwa Allah kukana ya kawo mun doki, idan zai jarabceni ya jarabceni daidai gwargwadon imanina, gabadaya I'm weak, zuciyata is weak, tunanina is weak gabadaya gabobin jikin is weak, I'm drained both physically, mentally and emotionally, yanzu ya zanyi? I'm still trying to make sense of duk abunda Ammar ya fa'da mun, Maganar daya kasa barin kwakwalwata shine inda Ammar ya furta kuma ya gasgata da aure tsakanina da Hassan, yanzu yana nufin all these while ina zaune karkashinsa a matsayina na matarsa? Daman duk tsawon lokacin nan ni matar Hassan ce? Bayan haka ma cikin jikina ya akayi aka sameshi, I'm still confused, don sanin kaina ne babu wani abun daya shiga tsakanina dashi, toh ta ina cikin ya bayana? How is it possible I'm pregnant? Sai yazo yayi mun wanan bayanin don bazan ta'ba yarda ba.
Ina cikin wanan tunanin naji anyi knocking an turo kofar, ko ba gaya mun ba nasan Ammar ne, ya karaso ciki yana kiran sunana nayi banza dashi naki juyowa, ina jinsa ya janyo kujera ya zauna a gefen gadon ya soma mun magana, sai dai duk maganar da yake naki tanka masa, a ynzu da nake jinsa wani irin haushinsa nakeji, ban ta'ba jin haushin Ammar kamar yanzu ba, "ya Hibba dan Allah ki juyo ki mun magana, kar kice zaki dauki dogon fushi dani, wlh I regret it. A lokacin dana aikaita hakan I was only looking out for you gani nake shi kadai ne mafita da zan iya kareki, amma yanzu na gane kuskurena, ya kamata ace na sanar dake kafun na aiwatar da komai, I'm really sorry please ki gafarceni..."
Ina sauraronsa duk maganar da yake bance masa uffan ba, har sai da priya ta shigo tayi mun abunda zatayi ta dauki blood pressure na, tana abunta ta lura da fuksata babu walwala ta tambayeni ko akwai wani abu nace da ita a'a, tayi tayi na fada mata nace mata ba komai haka ta gaji ta fice ta bamu wuri. Sai wuraren 10pm tukuna Hassan yayi sallama ya shigo, yana shigowa naga sun ha'da ido da Ammar sa'anan ya dawo da dubansa gareni, idanun mu na tsarkuwa naji gabana ya yanke ya fa'di nayi saurin kawar da idanuna, Hassan yanada wani irin kwarjini ne da duk inda ya shiga sai ya cika wajen, dukda fushi da haushin da nakeji sai danaji kwarjin nasa ya mamayeni, sanye yake cikin suit, yayi kyau sosai sai dai kallo daya zaka masa ka gano akwai damuwa a tattare dashi, fuskarsa ya nuna, bayan sun gaisa Ammar ya mike ya fice ya bar mana dakin ya rage daga ni sai shi, ina ganin Ammar ya fita na gyara kwanciyata ha'de da juya masa baya ina kallon wani bangare, shiru yayi bai ce komai ba sa'anan naga ya zagayo yazo inda nake ya tsuguna gabana yana fuskantata, mukayi face to face ya kura mun kyawawan idanunsa yana bina da kallo, kallona yakeyi with so much intensity wanda yasa zuciyata bugawa da matsanancin karfin gaske, cigaba da kallon juna mukayi dashi, deep within me ina kokarin fighting zuciyata tasan me takeyi kada ta karaya, don tun shigowarsa zuciyata ta shiga cikin hargitsi, yanzu kusancin da yazo yayi dani yasa komai na neman kunce mun, ga expensive kamshinsa daya zagaye mu nidashi, gabadaya na nemi nutsuwata na rasa, a hankali naga ya soma matso da fuskarsa dab da nawa, sai daya rage few inches tsakaninmu tukuna ya soma fadi muryarsa kasa kasa "bansan mezan ce miki ki huce wanan fushin da kikeyi dani ba, da zan iya bude zuciyata kiga yanda nake tsananin regretting actions dina dana bude miki kin gani, i never meant any harm towards you, Hibba ina ji a jikina haduwata dake cikin rayuwata bawai haka nan bane, it has a purpose wanda Allah has already ordained for it to happen, shi kadai ya tsara abunsa, haka ya kaddara zai faru tsakaninmu don haka ina rokonki da kiyi hakuri ki yafe mun, ko bazaki bani ansa ba yanzu just find it in your heart to forgive my actions, I love you soo much Hibba, ina sonki, kuma ina sonki da babyn da zaki haifa mana, I promise to love you both, i'll never abandon you, zan cigaba da baki hakuri har sai randa kika hucewa ranki...."
Duk maganar da yake bance mishi komai ba na lumshe idanuna ina sauraronsa har ya gama ya mike, "zan wuce office yanzu idan akwai wani abu da kike bukata kiyi mun text ko ki sanar da priya ta kawo miki, zuwa anjima i'll call you to check on you, in the evening driver zai kawo Faheema tazo ta ganki, so when I'm done i'll come and pick her up"
Nan ma bance dashi komai haka ya juya ya fice daga dakin, ina jin ya fita na bude idanuna, har yanzu zuciyata bata daina bugawa ba, nayi shiru ina kokarin saita tunanina, a hankali naji hawaye sun taru mun cikin idanuna, so nake na daure na cije, I can't succumb but abun yana neman yafi karfina, ina son Hassan zuciyata tana mutuwar sonsa, no matter how much I'm trying to stay angry at him nakeji na kasa, ganinshi ma kadai da presence dinsa is enough to make my heart weak.
Da priya ta kawo mun abun kari ha'de da magungunana na karba nasha wani irin bacci mai nauyi ne ya tafi dani, kamar cikin magungunan ta ha'da mun dana bacci don ban farka ba sai wuraren karfe uku na rana, na sauko naje nayi alwala nayi sallah azahar sa'anan na dawo na hau kan gado, wayata na dauko naga 3 miss calls biyu daga Hassan, daya kuma daga wajen Hafsah harda text ta turo mun na bude na soma karantawa, tambayata take ya jiki tana bani hakuri bata samu damar shigowa da safe ta dubani ba amma zuwa anjima da yamma idan Lukman ya dawo zatayi mishi magana ya kawota, idan kuma bazasu iya zuwa yau ba gobe da safe insha Allah zan ganta, na tura mata text nace jiki da sauki babu komai Allah ya kaimu goben sai na ganta.
Zuwa karfe shida driver ya kawo mun Faheema, da gudunta da murna ta shigo tazo ta rungumeni, nan take naji duk wani damuwata ya gushe nayi concentrating akanta munata hira tana bani labarin abunda mallaminsu ya koya musu a Islamiyah, dariya naketa yi ina biye mata nace ta kawo takardunta na gani, takardun ta ciro daga yar'jakarta muka fara da Al- Lughatul Arabiya muna kara revising abunda malamin ya koya musu.
Sai wuraren karfe takwas na dare tukuna mahaifinta ya shigo tana ganinsa ta jawo hannunsa ta zaunar dashi a gefena tana faman masa surutanta, shi kuwa tunda ya shigo idanunsa na kaina, naki bari mu ha'da ido, magana ma daya mun sama sama na ansa masa kuma don Faheema tana wajen ne banso ta fahimci komai, haka suna tare dani har zuwa karfe tara duk bai samu fuska ba, shima Ammar daya shigo gaisuwar nasa sama sama na ansa, babu wanda nakewa magana a cikinsu illa Faheema, gabadayansu jikinsu yayi sanyi, haka duk sukayi suka gaji suka kyale, ganin dare nayi ya kamata yakai Faheema gida ta kwanta yasa yace mun sai da safe, yace na ajiye wayata kusa zai kirani idan ya isa, banza nayi dashi ina cigaba da rungumar Faheemata na mata sai da safe sa'anan ya jata jiki a sanyaye suka wuce.
Not edited.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...