Chapter 17

1.2K 74 4
                                    

Hibba

Yau kwana uku kenan, Hassan bai cika mun alkawarinsa na kaini gun Ammar ba, na sa rai har na gaji, da dare kawai nake ganinsa, wanan ma sai dai yazo ya ta'ba ni son ransa ya rudar mun da tunanina dama gangar jikina tukuna ya kyaleni. Tun ina tsoro har nazo na soma dan sabawa tun da naga baida niyar having sex dani, na da'an saki jiki tunda iyakacinsa kawai wasa dani. Wanan wasan da yakeyi dani ba karamin tayar mun da hankali yakeyi ba, ko bacci bana iyayi sosai saboda shi nake gani cikin mafarki.

Sosai zuciyata ta shiga cikin damuwa ganin har yau kwana ta biyar kenan da signing contract din kuma yana ta'ba jikina son ransa amma yaki barina naje naga abunda nafi komai muradi a rayuwa. Na soma dana sanin signing contract din ba tare da mun tsayar da rana da kuma lokacin da zai kaini wajen Ammar ba, sai yanzu nake ganin wautana, na mika mishi yardata gabadaya, i've been so stupid.

Jiya da dare bayan ya gama abunda zaiyi, muna kwance na sake jefo masa tambayar yayi shiru daga bisani yace mun gobe zai kaini. Toh gashi goben yazo na shirya tun safe ina zaman jiransa har yanzu ban ganshi ba gashi ana neman la'sar. Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mun na share na mike na shiga bayi naje na dauro alwala na fito na tada sallah, ina idarwa na zauna ina lazimi, naji knocking a kofa hade da sallama aka turo kofar aka shigo, cikin sauri na waigo na ganshi ya shigo hannunsa rike da jakankuna designers kala kala, yazo ya diresu a gefen gado, kallo da'ya na masa na kau da kai, a tsanake ya tako yazo ya tsuguna gabana, sanye yake cikin black suit as usual da suke mugun fitting jikinsa, ya kamo taffin hannuna cikin lalausar nasa yana murzawa a hankali yace

"Ya dai?"

"Lfy lau" na bashi ansa still kaina a sunkuye naki da'gowa na kalleshi.

"Are you hungry?"

Shiru nayi masa dukda ina jin yunwa amma haushin abunda yake mun yasa naki ce masa komai

"Nasan you're hungry.... ga abinci nan na kawo miki kici ki shirya mu tafi"

Ina jin haka cikin sauri na da'go ina dubansa cike da rashin fahimta, da'ga mun gira da'aya yayi cike da sabo yace "ko baki shirya ganin kanin naki bane?"

Ina jin haka nayi saurin mikewa ina fa'din "na shirya"

Dariya ya da'an sake ganin yanda duk nabi na ru'de yace "kici abinci tukuna"

Zuwa yayi ya dauko wata leda ya bude mun wrap din abinci, shinkafa fried rice da yaji hanta da coleslaw da naman kaza, a gefe lemu mai sanyi ne, yana gama budewa ya matso mun dasu gabana yace dani bisimillah daga bisani ya nuna sauran jakankunan dake baje a gefe yace " ga sababin kaya idan kin gama ci sai ki canza. Godiya na masa, ya shafa gefen fuskata yace yana zuwa sa'anan ya juya ya tafi.

Yana fita ban tsya wata wata ba, jikina na bari na jawo abincin na dauki spoon na soma ci, abincin masifar dadi, sai faman loma nake ina hadawa da coleslaw da naman kanzan ina korawa da lemun mai sanyin, sai dana cinye tass tukuna na tattara na kai shara na dawo na soma bude sauran jakankunan, kayan cikin jakan farko na fito da, Abaya kala uku ne masu masifar kyau sunsha ado da duwatsu sai faman kyali sukeyi, da'ya bakar abaya ce tasha ratsin blue diamonds, daya maroon mai ditwasu farare sai kuma dayan brown itama mai rastin white flowers, sake baki nayi ina jujuya kayan a hannu, ina kallon label din, daga gani zasuyi masifar tsada don ko daga yanayin texture din zaka sani, a tsnake na ajiye su na bude dayan jakar naga wasu english wears gowns, trousers harda skirts da leggings sun kai kala goma, da'yan jakar ma na bude undies ne a ciki da bras kala kala, a hankali na bude dayar jakar naga takalama designers masu matukar kyau harda high heels, last jakar dana bude kayan makeup ne a ciki, irin tsadadun nan, shiru nayi ina bin kayan da kallo don nasan ba karamin kudi ya kashe wajen siyansu ba, sai kace lefe.

Cike da sanyi jiki na ciro Abaya maroon na shimfida gefe ha'de da sabon pant da bra da takalmi na ajiye, na fa'da bayi naje nayi wanka na dauraye jikina, na fito na goge jikina na soma shafa mai da special turarena na khumra, kamshin turaren da Hassan yake rikicewa akai jiya ma sai daya sani a gaba na gaya mishi inda na samo wanan kamshin, abun ya daure mun kai don ba wani special abu bane a wajena, tun ina karama ummanmu ta koya mun yanda ake ha'da turaruka kala kala, da kaina nake ha'da turaren shafawata haka zalika gidanmu rai da rai cikin kamshi bamu rabuwa da turare. A hankali na cigba da shafe jikina na dauko kayana na soma sawa, ina gamawa na bude kayan kwaliyan daya kawo mun na ciro powder kadai na shafa. Ni daman ba gwanar yin kwaliya bace, ban ta'ba makeup ba ban ma san yanda akeyi ba, shiyasa na shafa iya hodan, na dauki gyalen abayan na yafa, na dauko takalman nasa yayi fitting perfectly ina mamakin yanda akayi yasan size dina, komai ya zauna carass a jikina.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now