Chapter 59

1.2K 82 5
                                    

Maryam

Sauri sauri takeyi gudu gudu tana Allah Allah ta karasa gida, ta duba lokaci taga karfe tara saura, hankalinta ya kara tashi, bata so tayi dare haka, tasan Hassan ya jima da dawowa gida, wanan shegen go slow daya riskesu a kan hanyarsu ta dawowa ne ya ba'ta musu plan din komai, taso ta rigasu isowa gida.

Har ta shigo cikin estate din ta karyo kwanar da zai sadata da layinsu, unguwar shiru kasancewa gidansu ne kadai a wanan close din, wata mota ta gani anyi parking a gefen hanya, ta kurawa motar ido, this is not the first time da take ganin wanan motar kusan sati da'ya kenan. Ta dan tsorata, har ta karasa bakin gate zata danna kararawa taji an mata magana, cak ta tsaya sa! Sa'anan ta juyo a firgice.

Wani mutum ne mai dan' jiki taga yayi approaching dinta, yana sanye da kayan sanyi da face cap, daga ganinshi ba yaro bane amma bai manyanta ba sosai, it looks like yana late 40's dinsa, gaisheta ya soma yi "mallama sannu.... barka dai"

"Yauwa sannu barka" ta bashi ansa a dan' tsorace

"Dan Allah idan bazaki damu, inada dan'tambaya don ni matafiyi ne akan hanya nake,"

"Kallonshi Maryam tayi sama da kasa sa'anan tace "toh Allah yasa na sani, ina jinka"

"Anan gidan kike da zama?"

Ta gyada masa kanta

"Dan Allah akwai wace nake cigiya ne, yar'uwata ce ta gudu daga gida shekara biyar kenan bamu ganta ba muna kan nemanta, shine aka mun kwatancen nan gidan"

Maryam na jin haka ta tattaro duka hankalinta da attention dinta ta basa, "wanan yar'uwar taka ya sunanta? Kuma ya take?"

"Sunanta Hibbatullah, fara ce mara jiki, batada tsawo sosai kuma tanada yar' karamar fuska".

"Ohoo Hibba kake nema kenan, toh bata nan" ta bashi ansa ha'de da kokarin juyawa zata shige ciki ya kara dakatar da ita, "haba mallama, dan Allah ki taimaka ki tsaya ki saurareni, zan iya yin komai don na samu ganinta"

Juyowa tayi tana kallosa tayi shiru tana nazari, "meyasa ka damu kake son ganinta?"

"Kamar yanda na gaya miki, yar'uwata ce, An bani ita ne tun tana karama, ni ya kamata na aureta amma ta bijire ta gudu, dan Allah ina bukatan hadin kanki, kema kinsan aure ba abun wasa bane, ya kamata ace tana gidan mijinta yanzu".

Maryam na tsaye tana dubansa, wani tunani ne fa'do mata don haka ta dan' saki murmushi tace "toh shikenan zan taimaka maka amma bisa sharadi"

"Babu Komai mallama in har zaki taimaka mun na samu ganinta toh kin gama mun komai, zan iya yin komai duk abunda kikace"

Murmushi ta sake sakewa sa'anan tace "toh shikenan zaka iya zuwa gobe da safe?"

"Ko karfe nawane kikace nazo zan zo mallama"

Maryam tace "toh shikenan bani number wayarka, zan karasa maka bayani a waya yanzu dare yayi, duk yanda ake ciki zan sanar dakai"

Jiki na bari ya ciro wayarsa yayi saurin karban number wayarta, sa'anan ya mata godiya sosai ta juya ta shige ciki, kawu Abu cike da murna ya karasa cikin mota yayi driving ya koma inda yake kwana zuciyarsa cike da farin ciki.

Maryam na isa security suka bude mata gate ta shiga ciki, san'da ta soma yi har ta shige cikin parlourn ta soma haura sama, bata tsaya ko ina ba sai dakinta, tana isa ta sauke ajiyar zuciya tana kokarin kawowa kanta nutsuwa sa'anan ta soma tsara yanda zata aiwatar da abubuwanta.

********************

Hassan

Zaune yake akan kujera cikin parlournsa, da laptop gabansa yana hasko masa duk wani abu dake wakana cikin gidan, yayi zurfi cikin tunaninsa tunani kala kala na masa yawo aka, yana cikin wanan tunanin kawai yaga giftawar mutum ta cikin camera, hakan ya farfado dashi daga duniyar tunanin da yake ciki ya kurawa Cameran ido, Maryam ya gani tana karasow cikin gidan cikin sauri sauri gudu gudu har ta shigo cikin main Parlour na kasa, tana shigowa yaga ta soma san'da har ta idasa haurawa sama zuwa dakinta. Hassan yayi shiru yana duban screen din laptop dake gabansa, ya rasa ma me zaiyi a wanan lokacin, where is she coming from by this time? Shi daya bata umarni data jirashi suje su dawo shine har takeda guts din fita, zuciyarsa ne ya soma tafarfasa daya tuno abubuwan da take yiwa diyarsa baya nan da kuma munanan kalaman da take gaya mata, babu tantama karshen zamanta a gidan yazo kenan, bazaiyu ta cigaba da zama tana kulan masa da diyarsa da waenan bakaken hali irin nata ba, bai ta'ba regretting daukarta aiki da yayi irin na yau ba, idan ya tuno yanda Faheema ta dinga kuka tana zayane masa abubuwan da take mata sai yaji komai ya tsaya masa ya rasa meke masa dadi a zuciyarsa .

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now