Prologue

2.1K 122 9
                                    

Zaune yake kan daya daga cikin kujerun dake zube cikin VIP section na club din. Idanunshi kyam akan kyakyawar yarinyar dake tsaye da sauran yan'matan suna rawa, ido ya kura mata sosai, ko wani sashi na jikinta yana motsawa da rawan da takeyi.

Wani irin kallo ya dinga binta da shi yana jin wani irin abu na taso masa amma yayi kokari ya danne. Yarinyar ta juyo idanunsu suka tsarku cikin juna, nan take yaji yana neman loosing control.

Hannunsa yasa ya shafo lalausar sumar kansa wanda ya zame mishi jiki, yarinyar murmushi ta sakar masa sa'anan ta cigabada rawan da takeyi tare da kawayenta.

Hassan shiru yayi ya cigaba da kallonta, hannu yasa ya janyo glass cup na lemu dake gefensa akan table ya kai lips dinsa ya soma sha still idanunsa na kanta.

Allamu yayi da hannunsa, daya daga cikin bodyguards dinsa ya matso. Hassan ya soma fadin " ku kawo mun yarinyar can zuwa lounge dina within 5 minutes".

Bodyguard din yace "Okay sir".

Yana gama fadin haka ya mike ya gyara zaman suit din dake jikinsa sa'anan ya soma tafiyar nan nasa cike da kasaita. Sauran bodyguards dinshi suka mara masa baya har ya isa lounge dinshi. Suna isa kofar shiga lounge din, bodyguards din suka ja suka tsaya shi kuma ya shige ciki.

Hassan na shiga ciki ya ciro wayoyinsa guda biyu ya ajiye akan drawer dake kusa da gado, agogon hanunsa kirar rolex mai bala'in kyau da tsada ya cire ya ajiye shi gently a kan table din, daga bisani ya soma cire jacket dinsa na suit yayi hanging dinsa neatly. Komai nasa a nutse yake yinsa kuma a tsaftace.

Hannu yasa ya soma kwance tie din dake daure a wuyansa, yana cikin haka yaji an soma knocking, yasan babu mai zuwa yayi masa knocking haka sai bodyguards dinsa don haka ya bada izini a shigo.

Bodyguard din yasa hannu ya bude kofa ya shigo tare da yarinyar da Hassan ya bada umarni akawo masa.

"sir, she's here". Bodyguard din ya sanar dashi.

gyada masa kai yayi, sa'anan bodyguard din ya juya ya tafi ya basu wuri, ya rage daga shi sai yarinyar, ya kura mata kyawawan dara daran idanunsa ko kyaftawa bayayi yana kare mata kallo daga sama har zuwa kasa. Yarinyar sanye take cikin wasu kananan kaya da suka dame mata jiki, gown ce blue sai kuma black head din data daura akanta. Siririya ce sosai kuma fara, amma batada tsawo sosai. Itama tsayawa tayi tana kallonsa don tsananin kyaun da cikan zatin Hassan yayi mugun tafiya da imaninta. Tunda ta shigo cikin club din tare da kawayenta taji gabadaya hankalinta ya karkata zuwa gareshi don kwarjininsa ya mamaye gabadaya cikin club din. Ko wace mace dake cikin club din idanunta na kansa kuma kowace ta kasa dauke idanunta daga kansa.

Hassan yana tsaye daga inda yake ya cigaba da kare mata kallo daga bisani ya bude baki yace mata " have a seat".

Yarinyar batayi musu ba ta nemi wuri ta zauna. Hassan ya juya yaje ya cigaba da abunda yakeyi. Shirt dinshi ya soma cirewa sai ya rage daga shi sai black trousers, hannu yasa ya soma kokarin cire belt din wandonsa ya juyo yaga idanun yarinyar kyam akansa, sai ya fasa.

Towel dinsa ya dauko yayi hanyar bayi ya fada ciki ya kunna hot shower a kansa ya soma wanka. Sai dayayi kusan 15 minutes yana wanka daga bisani ya kashe shower din ya dauko brush dinsa ya somayi, nan ma sai daya dau lokaci.
Yarinyar dake zaune tana jiransa cikin dakin har ta soma gajiya sai gashi nan ya fito.

Bai ce mata kala ba, yaje wurin dressing mirror dinshi ya soma goge jikinsa daga bisani ya dauko body lotion mai dadin kamshi ya shafe duk ilahirin jikinsa dashi ya sake dauko turaruka ya fesa ta ko ina a jikinsa, ya karasa wajen wardrobe ya ciro sababbin kayansa. Simple wear ne riga da wando jeans ya sanya.

Yarinyar kallon mamaki kawai take binsa dashi dataga yanda yakeyin komai nasa a natse, ita kanta tasan daba din guy din ya mata ba kuma tana ganin he's loaded zata yagi rabonta ba data jima da tafiya don ita bata ga dalilin da zata zauna tana faman jiran namiji yana bata mata lokaci haka.

dauko wayansa yayi guda daya wace yake yawan amfani da ita sosai yazo ya zauna a gefen gado ya soma danawa. Bai kalleta ba yace " ya sunanki?"

"Laurat". Ta fada mishi kai tsaye.

"Laurat.....". Taji ya maimaita sunan nata sai kuma yayi shiru bai sake cewa komai ba ya cigaba da latse wayansa.

Laurat dataga ya shareta ya cigaba da abunda yakeyi ne yasa ta soma fadin " meyasa kasa aka kirani nazo nan idan kasan babu abunda zakayi dani?".

Hassan yayi pausing din abunda yakeyi ya dago yana dubanta da fararen idanunsa masu masifar kyau, sai daya dau minti biyu yana kallonta daga bisani ya taba gefen gadon muryarsa kasa kasa yace mata" come here".

Laurat ta mike a hankali tazo ta zauna a gefen gadon tana fuskantarshi. Hassan ya ajiye wayarsa gefe daya shima ya juyo yana fuskantar ta. Hannu yasa ya kwance head din data daure kanta dashi. Gashin attachment din dake bisa kanta suka zubo. Yasa hannu ya soma yawo dashi kan kyakyawar fuskarta, Laurat ta lumshe ido dan gabadaya wani irin feelings ne ta soma ji yana taso mata, ga daddaden kamshi turarensa daya mamaye ko ina.

Hassan ya cigaba da yawo da hannayensa bisa fuskarta, kamar daga sama taji ya birkito da ita ta fada bisa faffaden kirjinsa. Ya kwantar da ita bisa gadon. Soft lips dinsa yakai daidai bisa wuyanta ya soma kissing dinta a wajen daga bisani ya soma gangarowa bisa chest dinta.

Laurat gabadaya jikinta ya soma tsuma, gashi hanayensa basu tsaya wuri daya ba sai faman romancing din duk illahirin jikinta yakeyi.

Yunkurowa tayi tana kokarin ta hada bakinsu wuri daya amma bai bata dama ba ya cigaba da kissing din kirjinta yana shafa ko ina a jikinta. Hannu tasa itama tana kokarin ta cire rigan jikinsa ta samu damar romancing dinsa, yayi sauri ya cafke hanayenta ya hadesu wuri daya yaki bari ta tabashi. Duk yanda tayi kokarin ta taba shi taga abun ya gagara. Gashi yaki bata abunda takeso ita kuma yaki barinta tayi.

Abun ne ya soma bata haushi don Gabadaya ya gama tayar mata da hankali
"Allow me to touch you, ka barni na taba ka mana". Ta fada mishi.

Hassan ya girgiza masa kanta.

"Please". Ta sake fada

Bai sake cewa komai ba taga ya dago daga kanta ya zauna. Itama ta mike ta zauna tana kallonsa sai faman ajiyar numfashi takeyi. Shiru yayi yana kallonta daga bisani taga ya mike yaje can wurin drawers dake kusa da gadon ya bude ya ciro wasu files ya dawo ya zauna kusa da ita, ya bude file din ya ciro wata farar takarda dauke da wasu rubutu ya mika mata yace "read it and go through it carefully".

Cike da rashin fahimta ta karba takardan ta soma karantawa. Zaro ido tayi dataga abunda yake rubuce aciki ta dago tana dubansa cike da mamaki.

"You can't touch me. Bazaki iya taba ni ba, I won't have sex with you but you'll allow me touch you. So what do you think? Idan kin amince da duk abunda ke rubuce cikin takardan nan toh sai kiyi signing a kasa. Ni kuma i'll reward you handsomely" ya fada yana kallon cikin kwayar idanunta.

Shiru tayi tana kallonsa " wanan wani irin mutum ne yau ta hadu da?" Ta tambayi kanta. donta jima tana harkan karuwancin nan nata amma bata taba cin karo da irin wanan abun ba. Anya kuwa? Amma fa ga kudi nan makudai tana gani suna mata yawo a ido a rubuce a takardan idan ta amince.

"Kinyi shiru kina bina da kallo? Idan kinga bazaki iya ba. Babu dole ga hanya nan zaki iya tafiya amma idan kika kuskura kika fadawa wani abunda kikaga cikin littafin nan toh bazaki kai labari ba" ya karasa maganar yana mata warning.

Laurat shiru tayi tana jinsa
Cike da faduwar gaba ta bude baki tace " Na amince".

Hassan yace mata "Good, tashi ki saka kayanki ki biyoni". Ya fada mata yana mikewa.

Babu musu Laurat ta mike ta soma gyara kayan jikinta daga bisani suka fito tare. Straight penthouse dinsa suka nufa.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now