Hassan
A 360 su Hassan suka bar cikin daji suka kama hanyar asibiti, Sadik ne ke driving Hassan na zaune a baya da Hibba kwance a hannunsa tana rike da cikinta tana rintse idanu cike da tsananin azaba, ga jini daketa faman zuba mata, duk jikinsu ya ba'ce daga ita har Hassan, Hassan duk ya rude gabadaya hankalinsa yakai kololuwar tashi, sai faman kokarin kwantar mata da hankali yake yana kara rungumeta jikinsa, ai basu karasa ko ina ba, suna shiga cikin garin Ogun state suka hango wata asibiti, Prime gold, Hassan yace da Sadik su shiga nan, ba tare da ba'ta lokaci ba Sadik ya karasa aka bude musu gate, tarban gagawa aka musu, aka fito da gado aka daura Hibba akai sai emergency room, doctors da nurses suka mata caa aka ana kokarin tsayar mata da jinin dake zuba mata, su Hassan kam sunga tashin hankali da basu ta'ba gani ba, don tun da aka shiga da Hibba suketa faman zarya suna addu'ar Allah yasa ta fito lafiya, Hassan daman tun da yaga jinin da take faman zubar mata zuciyarsa ta gama karaya, jikinsa yayi mugun mugun sanyi.
Su Ndagi sun wuce, daga Ammar, Sadik, Jamal sai AK suke asibitin suna zaune sunata faman jira, Hassan kuwa tun da aka shiga da Hibba yake tsaye yaki zama, sai bayan kusan hour biyu tukuna daya daga cikin doctors din ya fito daga emergency room, Hassan da Ammar suka karasa cikin sauri hankalinsu a tashe suna tambayarsa lafiya ya jikin nata, kallonsu Doctor din yayi bayan daya sa'anan ya tambayesu waye spouse dinta a cikinsu, Hassan yace shine, Doctor yace ya biyoshi, tare suka karasa office, suna shiga ciki yayi masa nuni daya zauna, Hassan yaki "Doctor ka gaya mun, how is she, ya jikin nata?"
"Ka zauna mana tukuna sai na maka bayani"
Ajiyar zuciya Hassan ya sauke sa'anan ya samu wuri ya zauna da kyar yana fuskantar doctor din, Doctor ya dauko wasu takardu ya danyi rubuce rubuce sa'anan ya da'ga yana duban Hassan yace "I know you are aware your wife is 6 weeks pregnant sir"
Cak Hassan ya tsaya yana dubansa, nan take wuta ta dauke masa, Wani irin sanyin goosebumps ne yaji ya ratsa jikinsa, daman yanada suspicions akan shigar cikinta but yanzu da akayi confirming yaji gabadaya hankalinsa ya kara tashi, yana ganin duk shi ya jawo mata shiga cikin wanan halin, she's facing all these because of him saboda sakacinsa, kokarin danne zuciyarsa yayi yana duban doctor yace "doctor I understand amma ya lafiyarta yake yanzu, how is she now? Please tell me she's okay"
Ajiyar zuciya doctor ya sauke sa'anan yace "gaskiya she lost so much blood sir, we tried all our possible best to stop the bleeding, but we could only save one, I'm sorry to say"
Kirjin Hassan na harbawa da karfi yace "ban gane ba, you could only save one?"
"She was pregnant with twins, as a result of the severe blows data samu a cikin da'yan ya zube, amma the other twin is doing okay, munyi mata single-nucleotide polymorphism–based noninvasive prenatal testing (NIPT), your wife needs a lot of proper medical care and attention, the other baby is at great risk too saboda her uteral lining is still weak and kuma jininta ya hau sosai, you need to...."
Ai tunda Doctor ya fara bayani Hassan yasa hannu ya dafe kansa yana furta kalmar innalillahi wa inna illahi raji'un, yana rintse idanunsa, zuciyarsa na masa wani irin mahaukacin lugudin bugu cikin kirjinsa, Hibba na dauke da twins...kuma an rasa baby da'ya? Dayan ma babu assurance zai iya surviving har ta haifeshi saboda health dinta? Wani irin gumi ne ya shiga tsatsafo masa bai san sanda ya mike ba yana fa'din"Doctor zan iya ganinta yanzu?"
"No sir, you can't see her now, har yanzu she's still undergoing some ultrasounds, we've stabilized her but she's still unconscious, so you have to wait"
Hassan ya sake dafe kai yana fidda numfashi kamar wani mai ciwon asthma
Ganin halin da Hassan ya shiga ne yasa Doctor din ya soma kokarin kwantar masa da hankali yace karya damu, they have it under control, she's going to be okay, he should count himself lucky sun kawota da wuri"Da kyar ya samu Hassan ya danyi calming, at that time wani irin zafi yakeji cikin kirjinsa, wani irin bakin ciki ne ke cinsa ya rasa wani emotion zai dafa a wanan lokacin, he lost a baby with her...dana sani mara iyaka ya somayi a wanan lokacin yana jin yanda zuciyarsa ke kara masa hurting. Doctor ya kawo mishi wasu takardu akan ya cika, sa'anan ya shiga masa bayani dallah dallah yanda za'ayi a shawo kan health dinta, Da kyar Hassan ya samu ya fito daga office din jikinsa a sanyaye.
Ammar ya fara zuwa ya tareshi yana tambayarsa me doctor yace akan lafiyar yayarsa, Hassan yayi shiru ya rasa me zai ce masa a wanan lokacin, da kyar ya iya bude baki yace masa tana lafiya, Doctor yace she's going to be alright, nan ne hankalin Ammar ya dan kwanta, su AK ma suka karaso suna tambayarsa same thing ya fa'da musu, sai dai bai sanar dasu batun cikin nata da kuma ba'rin datayi ba.
Zuwa yamma Hassan ya kira private hospital dinsu dake cikin Ikoyi island, yasa akayi musu transfer zuwa can, babu ba'ta lokaci aka turo motocci aka zo akayi picking Hibba akayi transferring dinta zuwa can inda zata samu cikakken kulawa, sai dai har zuwa lokacin bata farfado ba. Special unit na Lagoon hospital akayi admitting dinta, musamman Hassan yasa special doctors da nurses suna attending to her, every 30 minutes suna zuwa suyi checking dinta.
Hassan yana zaune a special lounge na asibitin dashi dasu Jamal yayi zurfi cikin tunani, Sadik ya tafi gida shida Ammar don su kwaso wasu abubuwan da za'a bukata, ya rage daga shi sai AK da Jamal, har zuwa wanan lokacin zuciyarsa bata daina masa zugi da radadin da take masa ba, shi kadai yasan yanda yake ji cikin zuciyarsa, damuwa ne suka bi suka adabi cikin zuciyarsa, kuma damuwarsa akan Hibba, yanzu addu'arsa bata wuce tana cikin koshin lafiya ba, yana cikin wanan tunanin nurse ta karaso tace dashi zai iya shiga ya dubata, cikin sauri ya mike ya karasa cikin dakin, kwance take kan special gado, ga nau'rori sun zagayeta suna monitoring dinta, idanunta a lumshe, kyawawar fuskarta a kumbure, sosai ta sauya kamani kamar ba ita ba, a hankali ya karaso ya zauna a gefen gadon sa'anan ya kamo hannunta zuwa lips dinsa ya sumbata, wani irin hurting zuciyarsa ke masa ha'de da tsantsan tausayinta, ji yake dama shine a kwance a wurin ba ita, hannunsa ya kai ya daura bisa cikinta ya soma shafa a hankali yana jin wani irin burning feeling aransa, zallar sonta da son babyn da zata haifar masa yaji ya ratsa shi lokaci guda, bai ta'ba jin yaso abu kamar yanda yakesonta ba, ji yake zai iya yin komai don ya kareta da kuma abunda ke cikinta, duk wani tsoro da fargaba da yake ji tun farko game da cikin yaji ya gushe ya dawo masa zallan farin ciki, a hankali ya cigaba da shafarta yana addu'a Allah ya kara mata lafiya kuma ya da'ga kafadarta.
"Yanzu idan ta farfado ya zaka mata bayani game da wanan cikin dake jikinta? Me zaka ce mata?" Wata zuciyar ta tambayesa, sai a lokacin ya sake jin wani irin fargaba ya ziyarce shi, tsigar jikinsa suka mimike, tabbas yasan zasuyi daru da ita idan cikin ya gama fitowa, don yasan he can't keep hiding it from her, dole ya fito filli ya sanar da ita wanan sirrin da ba kowa bane yasan da ita ba. Saboda a halin da yake ciki yanzu yafi bukatarta a kusa dashi fiye ga komai, he can't imagine not being with her for the rest of his life, kwana biyun nan daya rasata it has been hell for him, Yana cikin wanan tunanin nurse tayi knocking ta shigo hannunta dauke da tray tace zata dubata, a hankali Hassan ya mike jiki a sanyaye ya juya ya fita don ya bawa nurse wuri tayi aikinta.
Yana fita wayarsa ta soma ringing, Ndagi ne ya kirashi ya sanar dashi cewa sun kilace Kawu Abu suna jiran order daga wajensa, Hassan yace su fara dealing dashi gashi nan zuwa, hatred da bakin cikin abunda kawu Abu ya masa yaji bazai iya hakura yabar wanan azalumin yaga wayewar gari ba don haka yace Jamal ya jira zasu je su dawo da AK.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...