Hibba
Zuwan yan'uwan Hassan was nothing like I expected. Tun kafun su iso zuciyata keta faman harbawa, ina tunanin yanda haduwarmu zata kasance, da wani ido zasu kalleni nasan bazasu ta'ba mun kallon mutunci ba, kallon watsatsiya zasu mun wace takeso ta kasance da dan'uwansu akan abun duniya, hankalina yayi maseefar tashi, koda suka iso kin fitowa nayi ina zaune a daki har sai da Faheema tazo ta soma jan hannuna tace daddy na kirana, jiki a sanyaye na mike na dauko gyalen abayan dana sanya na yafa a kaina sa'anan muka fito muka karasa da ita parlourn da suka sauka, tun daga bakin kofar nakejin maganarsu da dariyarsu na tashi, cikina ya kulle na kasa karasawa ina tsaye a bakin kofa, "muje Anty Hibba, muje kiga su uncle Sadik" Faheema ta fada cike da doki tana faman jan hannuna.
Dogon numfashi naja na fezar, sa'anan na kawowa zuciyata dakiya na bari ta jani muka karasa ciki bakina dauke da sallama, a tare suka juyo suna ansa sallamar ban da'go na kallesu ba kaina a sunkuye muka karasa da Faheema, ta gefen idona ina iya hango Hassan zaune ta kujeran dama, ina jin yanda idanunsa ke yawo akaina, zuciyata nata faman dokawa, kamar kasa ta bude ciki na shige nakeji don wani irin kwarjini ne na musamman ke tashi a parlourn ina jin idanun kowa a kaina, Faheema ce ta karasa a guje inda suke zaune tana fad'in "Uncle Jamal ga Anty Hibba"
A hankali na durkusa ina fa'din "Sannunku da zuwa, Ina kwana?"
"Lfy lau Anty Hibba, mun sameku lfy" uncle Jamal dake zaune a gefen Hassan ya ansa cike da fara'a a muryarsa
"Lfy lau" na ansa still kaina a sunkuye ina kokarin kare fuskata da gyalena
"Dago mana muga fuskar, anata bamu labarin Anty Hibba AntyHibba, yau munce bari muzo muga wanan Anty namu data daukewa yayanmu hankali, dan Allah ki sake jikinki kinji ko? Ni sunana Jamal, wanan kuma kanina ne sunansa Sadik"
Yanda yayi mun maganar cikin sigar kwantar da hankali yasa na danji karfi a raina tsoron da nakeji cikin zuciyata ta ragu, a hankali na dan da'go idanuna suka kansu, numfashina ne ya kusan daukewa. Bansan me nake expecting ba, but this wasn't it. Dukaninsu Sanye suke cikin kaftan, Yanayinsu daya da Hassan da hasken fatan da kwantaciyar sumar iri daya sai dai fuskokinsu ne yasha babban, ta yanda Hassan yafi kama da jinsin larabawa, shi Jamal yafi kama da turarawa, ko yanayin gashin kansa yasha banban danasu Hassan, amma kyakyawan gaske ne, yanada daradaran idanuna masu matukar haske da kyau hancinsa siriri kamar an zana masa shi, yanada fara'a sosai don tunda na shigo yaketa faman bina da murmushi, a hankali na dawo da dubana kan karamin cikinsu wanda Jamal yakira da Sadik, tunda na shigo banji ya furta wani abu bayan sallamar daya ansa, daga gani bashida hayaniya ko son magana, kallo na cigaba da binsa dashi cike da mamaki, Yanzu wanan shima kanin Hassan ne? Allahu akbar na fada a raina, ina kare masa kallo, shima farin fata ne irinsu amma fuskarsa da yanyinsa abun kallo ne, sak kamar chinese da idanun da hancin da komai, daba din shigar dake jikinsa ba sai ka rantse ba bahaushe bane, ko kadan baiyi kamada akwai digon jinin bakin fata a tattare dashi ba, kai bama shi kadai ba dukaninsu dake zaune a wajen idan ba'an fada maka ba bazaka ta'ba tunanin suna jin hausa ba. Ina cikin wanan sake saken a raina naga Faheema ta karasa wajen Sadik shi kuma ya dauketa ya dorata kan cinyarsa, nan take ta soma masa surutu tana nuna masa kayan wasan data rike a hannu, murmushi ya sakar mata ya soma biye mata nan take ta soma kyalkyalewa da dariya. Da alamu akwai kyakyawan bond tsakanin Faheema da kawunanta.
Muryar Hassan ne ya katse mun tunani inda yake fa'din "Hibba taso kizo ki zauna" ya karasa maganar yana nuna gefensa.
A hankali na soma kokarin mikewa naji wani irin juwa ya debeni nayi saurin rike kaina, kamar walkiya naga Hassan a gefena ya rukoni hankalinsa a tashe, nan take naji wani iri, "subhanallah batada lfy ne?" Naji Jamal ya tambaya daga inda yake zaune
"Meke damunki?" Hassan ya tambayeni cike da tashin hankali.
Na girgiza masa kaina nace mishi ba komai na gaji ne zan koma daki na kwanta
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...