Hibba
Washe gari ma haka the same thing, haka na farka da hope din ganinsa ko during the day amma shiru, kusan every seconds sai na duba wayata ko zanga kiransa amma shiru, tun ban daga hankalina sosai har yazo ya kaiga I couldn't help it, abun ya nuna sosai a fuskata, gashi yau na tashi gabadaya ina jin jikina wani iri, wani irin zazzabi zazzabi Ke kokarin lulubeni, na kasa cin komai, maganin da aka kawo mun da abinci ma amayo su nayi, duk jikina yayi weak, hankalina ya tashi, a halin yanzu ji nake komai ya sane mun a rai, koda Doctor Munir yazo ya dubani, wasu sababin magunguna da allura ya sake rubuta mun, suma ina kaiwa baki duk na dawo da su, sai da aka mun alluran tsayar da amai tukuna na samu na dan' dawo hayacina, sunata faman mun sannu, suka ce zasu kira Hassan su shaida masa, hankalina a tashe na dubi doctor Munnir ina tambayarsa meke damuna kuma? don nasan lafiya lau tsakanin jiya da yau, har ina sa rai sallamata da za'ayi, murmushi ya sakar mun yace na kwantar da hankalina it's not something serious, jikina ne yake responding ga laulayin ciki amma karna damu zai lafa, jikina ya kara weak jin abunda ya fa'di, sai wajajen la'asar tukuna naji zazzabin ya dan lafa mun, Hafsah ta kirani tace gata nan zuwa zata zo muyi sallama yau zasu wuce Abuja, jiki a sanyaye nace mata toh sai tazo, bayan la'asar sai gata, ina kwance tayi sallama ta shigo, sanye take cikin wani expensive lace dinki da aka mata ya zauna carass a jikinta, tayi kyau sosai, na lura wajen sutura dai Lukman baya barin Hafsah haka, komai yana wadatata dashi, kamar yanda Hassan yake zaqewa yana spending akaina game da duk wani abun da nake bukata haka itama, hannunsu a sake yake dukaninsu.
Cike da farin ciki ta karaso gefen gadona tazo ta rungumeni tana mun sannu da jiki, nima na nuna farin cikin ganinta ina kokarin mikewa naji duk na kasa don jikina yayi weak sosai, hannu tasa ta janyo pillow ta jingina mun da kanta ta taimaka mun na zauna.
"Sannu Hibba..., ya jikin, badai zazzabin bane ya kuma tashi?"
"wlh Hafsah tun jiya nake jin jikina haka, na rasa gane kan al'amarin ciwon nan nawa"
"Oh Allah, to me Doctor suka ce?"
"Cewa sukayi it's nothing serious, laulayin cikin ne amma zai lafa mun"
Ajiyar zuciya Hafsah ta sauke tayi shiru tana dubana cike da tausayawa sa'anan tace "yanzu ya ake ciki game da wanan cikin naki Hibba, zaki bari ki haifesa? Me Hassan yace?"
Rintsa idanuna nayi ina jin wani irin kulutu cikin kirjina jin ta ambato mun Hassan, "Hafsah... har yanzu I don't really understand what's going on, abubuwa sun faru da dama da har Yanzu I'm still trying to place my head around it"
"Ban gane ba, me kike nufi? What's going on?"
"Hafsah kinsan da aure tsakanina da Hassan? all these while da nake tare dashi a matsayin matarsa nake?"
Kallona Hafsah take kamar bata fahimci abunda nake fad'in "wait hold on... ban gane ba, kina nufin kice da aure tsakaninki dashi all these while?How...taya?"
Ajiyar zuciyata na sauke, na kwashi komai na sanar da ita, har shaidu dana samu wajen Ammar da AK, duk maganar da nake gaya mata Hafsah bina take da kallo cike da mamaki, jikinta itama yayi mugun mugun sanyi,
"Hafsah kwana biyun nan na shiga cikin damuwa da tashin hankali irin wanda ban ta'ba jin irinsa ba, my heart and my mind is in chaos, na rasa yanda zanyi, ki bani shawara Hafsah, I need your advice please, ke kadai ce zaki iya fada mun abunda zaisa zuciyata rage zugin da take mun"
Ajiyar zuciya Hafsah ta sake ta kamo hannuna cikin nata tana kara matsowa kusa dani tace "kiyi hakuri Hibba... daga ni har ke hakuri zamuyi da irin kalubali da muke fuskanta cikin rayuwa, haka Allah yaso don haka ki nustu ki cigaba da kai masa kukanki, nima shi nake kaiwa kukana babu dare babu rana, shi kadai yasan dalilin dayasa abubuwa suke faruwa haka, kuma shi kadai zai magance mana"
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
Lãng mạnHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...