Hassan
Tun a office yake jin gabadaya jikinsa wani iri, ya kasa sukuni, gabadaya mind dinsa nakan Hibba, yana gama meeting daya rage masa bai tsyaa ba'ta lokaci ba ya bar office ya kama hanyar gida, ya duba lokaci yaga karfe shida saura, da yayi niyan ya kira doctor Fuad wata zuciyar tace dashi ya bari ya karasa gida tukuna yaga yanayin jikinta. Within 15 minutes ya karasa gida aka bude masa gate ya shiga yayi parking. Sama ya fara haurawa ko dakinsa bai leka ba, ya tsaya bakin kofar Hibba yayi knocking ba ansa ba, a tunaninsa ko tana bayi ne yasa ya karasa dakinsa yaje ya dan watsa ruwa a jikinsa ya canza kaya ya fito ya sake komwa dakin nata, yayita knocking ba'a bude ba, wanan karon bai tsaya ba'ta lokaci ba ya murda handle din kofar ya jita a bude ya tura ya shiga ciki hade da sallama nan ma yaji shiru, babu alamunta, ya karasa bayi ya leka nan ma babu, nan take yaji hankalinsa ya soma tashi ya soma kwada mata kira amma shiru kake ji cikin sauri ya sauko kasa ya tadda madam Laide yana tambayarta Hibba tace bata sama a dakinta? Don dazun ta sauko ta samesu a kitchen, hankalin Hassan ya kara tashi yace bata nan bai ganta ba, Baraka ce ta karaso take fa'din dazun ta ganta ta fita wajen gate tana tsaye da Mr John, bata sani ba ko fita tayi ba, haba Baraka ba'ta gama rufe baki ba Hassan ya karasa a guje zuwa gate yaje ya samu Mr John, cike da masifa ya soma tambayarsa ina Hibba?
Tsuru tsuru Mr John yayi da ido ya rasa mezai ce cikin i'ina ya soma fadin "erm sir.. she went out to buy something earlier tace bazata jima ba"
"Shit!!" Hassan ya fada, gabadayansu a wajen sai da cikinsu ya duru ruwa.
"Uban wa yace ku barta ta fita ita kadai?? Orders din dana baku kenan? Bance duk sanda zata fita asa wani security ya rakata ba?"
"Yess sir..but"
"Shut up!!! banso naji komai Stupid kawai !!"
Wayarsa ya ciro ya soma kokarin dialing number Hibba ya jita a kashe, "shit!!" Ya kuma fadi yana dafe kai, gabadaya tunaninsa a dagule yake, hankalinsa yakai kololuwar tashi,
"Ina takamame tace muku zata?"
"Wlh oga bamu sani ba, kawai dai tace zata siyo abu ne ta dawo, bata gaya mana inda zata ba" cike da tsananin tashin hankali Hassan ya koma ciki yaje ya dauko makulin motarsa bai tsaya sauraronsu ba at 360 ya bar gidan, tuki yakeyi kamar zai tashi sama, hankalinsa baya jikinsa, bai ma san ta inda zai fara nemanta ba, har bakin titin shiga estate dinsu yaje ya soma dube dube ko zaiga alamunta amma babu, kamar zaice wayo Allah, kusan zaucewa yayi a wajen yana nemanta amma ko mai kamata da ita bai gani ba, Ya lalubo number Ndagi ya soma dialing, ringing daya ya dauka, "Ndagi where are you, ina so kai da men dinka ku bazama garin Lagos duk inda Hibba take ku nemota!! she's missing!!!"
"Oh shit!!" Ndagi ya fa'da hankalinsa a tashe "kana tunanin wanan kawun nata yanada hannu ciki?"
"I'm not sure but we're not taking chances!! We need to look for her starting now!"
"Okay toh shikenan oga, we're on it, insha Allah zamu nemota duk inda take"
Yana gama waya da Ndagi ya soma kiran Jamal ya sanar dasi abunda ke tafe, shima hankalinsa yakai kololuwar tashi, Hibban da suka gani da safen nan ne ta ba'ta? Hakuri Jamal ya dinga ba yayan nasa yace gashinan zuwa shida Sadik. Hassan ya rasa inda zaisa kanshi, yafi 3 hours yanata faman nemanta yaje nan yaje can amma babu alamunta, haka ya hakura ya koma gida zuciyarsa kamar zata raba kirjinsa ta fito tsabar tashin hankalin da yake ciki, addu'arsa daya Allah yasa duk inda take tana cikin koshin lafiya babu abunda ya sameta kuma duk wanda yakeda hannu cikin batarta ya kuka da kanshi, don Allah kadai yasan mezaiyi idan ya daura hannunsa akan duk wanda yakeda hannu cikin batarta.
***********************
Hibba
Sanda na dawo cikin hayacina, ban san inda kaina yake ba, wani irin tsoro da fargaba ne ya ziyarceni lokaci guda, naji kaina yayi mun wani irin sara kaman an zube mun ginin block, sallati na soma yi ina jin wani irin jiri na debata, da kyar nake iya fidda numfashi.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...