Hibba
Sai bayan sallah isha su Sadik suka wuce, Hassan yaje yayi dropping Faheema a gida saboda dare yayi gobe tanada makaranta, da kyar ta amince ya wuce da ita sai da yayi mata alkawarin gobe tana dawowa daga makaranta zai kawota tukuna ta yarda.
Suna tafiya ya rage daga ni sai Hafsah, na lura tunda ta shigo sai faman bina da kallo take kamar akwai abunda ke damunta cikin rai, na soma tambayarta ko akwai wani matsala ne? Shiru tayi kamar tana nazari sa'anan tace mun a'a, ta sake tambayata ya jikin nawa, ko sun fa'da mun a asibiti abunda ke damuna nace mata a'a, ni I don't think akwai abunda yake damuna bayan wanan ciwon danaji, besides I'm feeling much better yanzu, tace toh na lura kamar she's not satisfied da abunda na fa'di amma bata ja ta canza wani topic muka fara hirar sosai nake tambayarta ya suke ciki da ita da Lukman tace lafiya lau komai na tafiya normal tsakaninsu, ta fara bani labarin tafiya kasan waje da sukayi, da irin kulawar daya dinga nuna mata tace, duk abunda takeso yana mata kamar zai mayar da ita ciki, na nuna mata farin cikina akan hakan at least baya muzguna mata, a hankali naga ta sunkuyar da kanta ta akfa wani tunani daban na tambayeta meya faru, tace "wlh Hibba bana son yanda muke zama nidashi hakan, kullum ina rokon Allah ya yafemun ya yafemana don zaman sam bai dace ba, ina son Lukman Hibba, ina son ya aureni da akan zaman nan da mukeyi dashi"
Shiru nayi nace hakane, don I can relate to what she's saying, nima da zan so hakan nida Hassan dukda dai ya furta yace mun yana sona yanzu, hawaye naga sun taru cikin idanunta ta kamo hannuna cikin nata tana fa'din "Hibba tunda na hadu dake nakejin kamar na ha'du yar'uwata jini guda, kece kadai zan iya zama na gayawa abunda ke damuna kuma ki bani shawara haka zalika nima bazan so na ganki cikin halin nayi shiru na kyale ba"
Hankalina ne ya soma da'gawa na fuskanceta da kyau "menene Hafsa? akwai wani abu dake damunki ne? Ki fada mun please"
Shiru tayi sa'anan tace "ban sani ba.... I don't know if it's right to tell you this amma nima hakan ya faru dani so bana so kema hakan ta kasance dake ba"
"Dan Allah Hafsah ki gaya mun koma meye, please"
Shiru tayi tana hesitating sa'anan tace "kinsan kina dauke da ciki?"
Cak na tsyaa ina dubanta, zuciyata ta daina bugawa na huccin gadi sa'anan tazo ta cigaba da bugawa, kallonta nake cike da mamaki da al'ajabin abunda ta furta.
"Bawai na fa'da miki haka don na tayar miki da hankali bane, a'a don nasan halin irin mazajen da muke tare da, nima a lokacin da hakan ta sameni cewa yayi na zubar, I was so naive and stupid na biye mishi, nasha wahala sosai daga baya nazo ina regretting, na aikata zunubi biyu, I don't want you to go through that too, yau da rana da suka zo wajen mu naji suna discussing akan cikin dake jikinki, duk yanda za'ayi Hibba, karki amince a zubar miki da cikin nan......"
Ai tunda Hafsah ta bude baki ta soma mun magana akan wani ciki naji komai ya dauke mun, zaro ido nake ina binta da kallo kamar a lokacin na fara ganinta. "C...ciki? Ciki fa tace? Haba Hafsah, kinsan me kike fa'di kuwa? Taya zaki ce ina dauke da ciki, na soma girgiza mata kai, "no Hafsah, it's not possible babu ciki a tatare dani, ina zan samu ciki ana zaune kalau"
Shiru tayi tana dubana cike da damuwa a fuskarta. Zufa ne ya soma karyo mun daga inda nake zaune abubuwa da dama suka soma dawo mun, duk nabi na rude, na tuno maganganun Kawu Abu da Maryam inda suka nace cewa lallai ina dauke d ciki, yanzu kuma ga Hafsah. What's going on? Meke faruwa ne ko kuma ince meke shirin faruwa dani? Taya zasu sani a gaba suce ina dauke da ciki, ganin halin dana shiga ne yasa ta soma kokarin kamo hannuna don ta kwantar mun da hankali, muna cikin haka sai gasu Lukman sunyi sallama sun shigo tare da Hassan, jiki a sanyaye Hafsah ta mike tana dubana ta fake idanunsu tayi mun alamu da Hannunta danayi kokari na danne zuciyata, a firgice idanuna suka sauka kan Hassan daketa faman bina da kallo muna ha'da ido yaga yanda nake binsa da kallo ya fahimce babu lafiya, sallama mukayi dasu Hafsah tace mun sai da safe gobe zata zo ta ganni kafun su wuce, da kyar na ansa mata, Hassan yayi sallama da Lukman suka wuce.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...