Chapter 11

1.2K 90 10
                                    

Hibba

Farkawa nayi ina mika ina sallati, tunda nayi sallahn asuba na koma bacci ban sake farkawa ba sai yanzu, hasken rana ne ya kara'de ko ina, na juya ina duban waje, daga inda nake kwance ina iya hango ko ina, gabadaya na tattara na mika hankalina ina kallon yanda gidajen suka bazu kota ina, abun yayi matukar mun kyau.

"Morning beautiful" naji murya ta daga can gefena ya furta

A firgice na waigo naga mutumin dana raba dare ina tunaninsa tsaye a bakin kofa ya rungume hannunsa bisa kirjinsa yana kare mun kallo, sanye yake cikin bakar suit da sukayi matukar amsar kyakywar surar jikinsa, fuskarsa smooth dashi, lalausar murmushi ya sakar mun muna ha'da ido naji zuciyata ta harba da karfin gaske nayi saurin sunkuyar da kaina "ina kwana" na gaisheshi. A hankali ya soma takowa har yazo ya tsaya gabana yana dubana yace "nazo tun dazun inata sallama but I guess you were fast asleep, I came to check up on you"

Da'ga masa kai kawai nayi, ina kara matsawa kan gadon na janyo bargo na rufe jikina, gabadaya wani irin kwarjini yake mun na kasa concentrating yana tsaye a kaina,

"Breakfast is ready, idan kin shirya ki sauko kasa sai mu karya"

kai kawaina sake da'ga masa, ya juya ya fice daga dakin. Yana fita na duro daga kan gadon na fa'da bayi nayi wanka nayi brush na kimtsa jikin, kayan dana cire suma na ninke na kimtsa su, ina gamawa  na zira hijab na sauko kasa.

A dining na sameshi yana zaune, ga plates na abinci an jera akan table, shayi ne da soyyayen kwai da irish pototoes an soya sai kuma toast bread, gabadaya wurin ya gauraye da kamshi, nan take naji miyau na ya tsinke ganin abincin dake zube a gabana.

"Bisimillah" ya sanar dani yana nuna mun wurin zama, godiya na masa naja kujera da'ya na zauna naga ya tura mun cup dauke da shayi da kwai da bread da dankali, kallon abincin nake with interest na da'go muka ha'da ido naga yana dubana murmushi a fuskarsa, share shi nayi na dauki cokali na soma cin dankali da kwan dake gabana, na janyo cup ina kur'ban shayi na, a raina sai faman santi makeyi, ina tunanin yanda masu kudi irinsa suke rayuwa, komai yi musu ake jibi abinci mai da'di irin wanan, na tuno gidansa na farko dana fara zuwa yanda yan aiki suketa faman kai kawo, sai abunda aka sasu suyi, kai talauci baiyi ba. Na fa'da can kasan raina ina cigaba da cin abincin.

Muryarsa ne ya katse mun tunani inda yake fadin "what's wrong?"

A hankali na hadiye abincin dake bakina nace "na me kenan?"

"Naga kin ba'ta fuska, ko abincin bai miki bane?"

Saurin girgiza masa kai nayi nace mishi bakomai kawai tunani daban nake. Bai sake ce dani komai ba muka cigaba da cin abincin, sai faman bina da kallo yake, duk loma da'ya biyun da zanyi sai naji idanunsa akaina, gabadaya naji na takura a wajen ina Allah Allah na gama ci na bar masa table din, ina gamawa na mike na soma tattara kwanukan, ai kuwa kafun na karasa unexpectedly naji ya fizgoni na fa'da jikinsa, a firgice nake binsa da kallo ina kokarin mikewa naji ya mayar dani ya zaunar kan cinyarsa, ya soma shafar hannuna, tsabar shock ma kasa motsi nayi ina jin yanda hannayensa ke yawo a sansar jikina har ya gangaro zuwa fuskata, gabadaya yanayinsa ya sauya, ga wani dadaden kamshin turaren jikinsa da'ya karade ko ina yana kawowa zuciyata farmaki, a hankali yakai fuskarsa daidai saitin wuyana ta hijab dana sanya yana lumshe kyawawan idanunsa yana cigaba da shafar fuskata daga bisani ya dago yana kallon cikin kwayar idanuna, munfi minti biyu a hakan muna kallon cikin kwayar idanun juna ina hango wani abu a kwayar idanunsa wanda bansan ma'anarsa ba, muna cikin haka unexpectedly naji ya matso da fuskata ya ha'de bakin mu wuri da'ya, ya soma kissing dina, freeze nayi hade da shock kamar an jona jikina da wutan lantarki ina jin yanda ya kamo lips dina na kasa ya soma tsotsa a hankali yana ajiyar numfashi, nan take na tsinci kaina cikin wani irin yanayi , gabadaya jikina ya dauki kyarma, cigaba da kissing dina yake yana tsotsan bakina kamar ya samu sweet, tsabar shock ma kasa motsi nayi, munfi minti uku a hakan yanata kissing lips dina, kamar an tsikareni na soma kokarin kwatar bakina daga nashi, baiyi forcing dina ba a hankali ya sako ni, yana ajiyar numfashi sai faman bin fuskata da kallo yake yana lumshe ido, ni kaina ajiyar numfashin nakeyi, kirjina na bugawa da karfin gaske cikin sauri na mike daga cinyarsa, kamar a mafarki nakeji wanan abun ya faru, tunda nake namiji bai ta'ba shan bakina ba, sai kawu Abu mijin Anty Lafi dayayi kokarin forcing kansa akan nida Ammar lokacin muna kanana.

"Have you decided yet?" Naji muryarsa ya fargar dani daga duniyar tunanin dana afka, a tsorace na waigo ina dubansa. Naga yana dubana yana jiran na bashi answer akan abunda na raba dare jiya ina tunani akai, nasan kona ki kona so dole nayi making decision, dole na ceci kanina koda ya kama na mikawa wanan attajirin kaina in exchange for 100million, daren jiya naci kukana har na godewa Allah, daga karshe na za'bi na mikawa Allah lamurana, don shi kadai zai iya fitar damu daga cikin wanan ukubar.

"Uhm ina jinki" naji ya sake fadi jin shirun danayi

Dagowa nayi ina dubansa muryata na rawa nace "idan na amince ga proposal dinka.... zaka sa ayi releasing Ammar?"

"Off course Hibba, I'm a businessman and a contract is a contract"

Gyada masa kai kawai nayi nace "toh shikenan... na amince, I'll sign the contract". Na karasa maganar ina jin yanda zuciyata take karaya. Shikenan na rigada na siyar da kaina, na siyar da mutuncina wanda har abada bazan taba dawo dashi ba, ubangiji Allah bazai taba yafe mun ba.

"Sit down" naji yace dani.

Jikina na rawa haka na samu wuri na zauna, Wasu takardu ya miko mun, yace "gashi ki karanta, I want you to read everything carefully"

"Ba sai na karanta komai ba, what difference does it make" na fa'da jikina a sanyaye

Murmushi ya sakar mun yana girgiza kai yace "no Hibba it doesn't work that way, you have to go through it and sign, ni bazan ta'ba saki kasancewa dani dole ba, bazan ta'ba saki kiyi abunda baki so ba but this is a business contract and anything can happen in the future, so now read it"

Karban takardan nayi na soma dubawa, naga sunana da sunansa rubuce karara akai kamar real business contract, abu guda uku ne suka dauke mun hankali "mistress....5years...100 million" sai wasu rubutu da ban fahimce me suke nufi ba, ganin kamar nayi confuse ban fahimta ba yasa ya karbi takardan daga hannuna ya soma mun bayani.

"Wanan rubutun da kike gani, yana nufin agreement tsakanina dake"

Na da'ga masa kai, shi kuwa ya cigaba "wanan kuma yana nufin idan har kika sa hannu kika amince zaki zama tawa har na tsawon shekara biyar toh bashin dake tsanina da kaninki za'a janye. The rest just clarifies our relationship, once you sign the contract, you're mine, you'll be under my protection dake da kaninki babu wanda ya isa ya ta'ba lafiyarku"

Na tsaya nayi shiru ina karewa rubutun kallo, dama aure yayi mun offering muyi har na tsawon shekara biyar ba wai na zama mistress dinsa ba, da'gowa nayi ina dubansa zuciyata ta raya mun wanan bazai ta'ba cewa na aureshi ba don banyi kallar matan da zai iya aura ba, sai dai ya mayar dani abar wasarsa idan ya gaji dani ya watsar. Ajiyar zuciya na sauke nace ko ba komai at least nida kanina zamu kasance cikin karkashin kulawarsa.

"Take your time and read through it, ina zuwa" ya fa'da sa'anan ya mike ya haura sama zuwa dakinsa. Yana fita na dawo da dubana ga takardan na cigaba da karantawa naga ta kasan an rubuta idan har na kuskura na gudu kafun shekara biyar toh bashin yana nan ba janye ba. Nayi shiru ina nazari, that means ban isa nace zan janye ba, dole na kasance tare dashi har na tsawon wanan lokacin. Sai bayan kusan 10 minutes sai gashi nan ya dawo, yana tambayata "are you ready?"

Ajiyar zuciya na sauke ina kallon takardan daga bisani na gyada masa kai zuciyata na mun wani irin nauyi, ya miko mun biro.

Kafun nayi signing wani tunani ya fa'do mun na da'go cikin sauri ina dubansa nace "kanina fa? Yaushe zan samu ganinshi? Zaka sa wanan AK din ya sako mun shi?" Na tambayashi muryarta na rawa cike da hope cikin kwayar idanuna

Murmushi ya sakar mun yace "well zaki ganshi gobe amma it's left to shi Ammar ko Ak suyi deciding last tambayarki".

Cike da rashin fahimta nace " ban gane su zasuyi deciding ba? Ai an rubuta ance ina signing babu wata sauran bashi kuma"

"Eh babu wata saurin bashi once you sign" ya fa'da mun kai tsaye ba tare da wata bayani ba, nayi shiru ina nazari, can naji yace "any more questions?"

Girgiza masa kai nayi na duki takardan jiki a sanyaye nafi minti biyar ina kallon takardan daga bisani nasa hannu inda aka rubuta sunana, haka ina ji ina gani nayi signing rayuwata da farin cikina game da wanan mutumin, zuciyata kamar zata tarwatse.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now