Chapter 70

1.1K 71 18
                                    

Hibba

Ina kwance a inda suka barni idanuna a rufe ina jin yanda jikina yake cigaba da mun radadi, so nake na daure na mike amma naji na kasa saboda duk jikina yayi weak sanadiyar dukan dana sha. Rintse idanuna nayi ina kokarin tattarowa kaina dauriya na mike, I have to take control of my weak body and move in har ina so na samu nayi escape daga wajen nan kafun dare yayi Kawu Abu yazo yayi gaba dani,

Yunkurawa na sake yi Cikin ikon Allah kuwa naji karfi ya dan dawo jikina na mike da kyar ina nishi, idanuna suka sauka kan window, dan hasken da yake shigowa ne ya bani alamun yamma ya gabato, gabana ya yanke ya fa'di don nasan I have only a few hours kafun garin yayi duhu gabadaya, dole nasan yanda zanyi nayi escape daga wajen nan kafun lokacin.

Dogon numfashi naja na fezar ina kokarin kwasowa kaina dauriya na mike daga kan gadon, dukda da irin azaba da radadi da nakeji yana ratsa duk ilahirin jikina hakan baisa na karaya ba na mike, kafafuna kamar laka sai faman rawa suke, nafi minti biyar tsaye ina kokarin saita kaina har na samu naji kaina ya dawo daidai, jirin ya dan' lafa mun, a hankali na soma motsawa ina jan kafa har na karasa wajen dana hango rigata a yashe a kasa naje na dauko na soma sanyawa a jikina, a hankali nakeyi don kar suji motsina don nasan basuyi nisa ba, maybe suna da'yan dakin dake kusa da inda nake. Nasan a tunaninsu yanzu a yanda suka tafi suka barni bazan iya motsa koda yatsuna bare har na iya mikewa da kaina.

Cigaba da kokarin sa kayan nayi ina Allah Allah na gama kafun wani cikin su ya sawo kai, ina gama sa rigata cikin sauri na karasa wajen kofar,  na dan girgiza cikin sa'a kuwa na jita a bude, wani irin farin ciki ne naji ya lulubeni na shiga mikawa Allah godiya, a hankali na bude kofar na leka, cikin gida ne mai fadi da sauran dakuna a zube a ciki, sai ciyawu kota ina, da Allamu cikin daji muke, wurin shiru babu motsin kowa don haka ba tare da ba'ta lokaci ba nasa kai na bude na fito a hankali ina san'da ina waige waige har na samu na karaso cikin gidan, wata kofa na hango ta baya, da alamu nanne kofar fita, ban tsaya ba'ta lokaci ba na karawa kafata wuta kafun wani cikinsu ya sawo kai ya ganni, ai kuwa ina isa kofar har nasa hannu zan bude sakatar sai ga Maryam nan kamar an jehota ta fito daga daya daga cikin dakunan tana ganina tayi freeze tana bina da kallo baki a sake, nima cak na tsaya kirjina na harbawa da karfin gaske "keh!!!" Ta fa'da a tsawace "Ya akayi kika.." bata gama karasa maganar ba sai ga Kawu Abu nan shima ya sawo kai, nan take naji abubuwa sun sake dagule mun duk na rikice na soma ja da baya ina girgiza kai, ba haka naso abubuwa su kasance ba, naso na samu nayi escaping kafun daya daga cikinsu ya fito ya tadda ni, shima Kawu Abu yana ganina shock yayi a wajen hade yana bina da kallo, nan take fuskarsa ta rikice da ha'de kamar hadari wani irin ashar ya  lailayo  ya hankade Maryam gefe yayo kaina gadan gadan, ban tsaya wata wata ba nayi saurin sa hannu na bude sakatar kafun ya karaso na fita a guje, shima yabi bayana yana zage zage, dukda pains din da nake ji a jikina hakan bai sa na tsya ba, a lokacin ma ji nayi na daina jin wanan zugin gabadaya hankalina nakan yanda zanyi nayi escaping daga hannun Kawu Abu daketa faman charji a bayana kamar wani mayunwacin zaki, ban tsaya ba inata faman gudu, gudu nakeyi irin wanda ban ta'ba yinta ba, gudun tsira gudun ceton rai, sai faman shiga cikin daji muke Kawu Abu yana biye dani yana kirarin zai kasheni, ban saurareshi ba na cigaba da gudu. Wani katon itace dake kwance kan gefe hanya ina kokarin tsalakewa naji ya ta'deni, kafun kace me naji kaina a kasa within 2 seconds sai ga Kawu Abu akaina, yasa hannu ya damki gashin kaina ya da'gani da iyakacin karfinsa sai dana saki kara don azaba, kokuwa dashi na soma yi ina fadin ya sakeni na sake zamewa na fa'di a kasa, mari ya kaimun a gefen fuska sai danaga wuta bai tsaya nan ba ya soma jana a kasa, ciyawan da kaya da duk abunda ke kwance a kasa ya dinga kuje mun fatar jiki, ihu na dinga ina kokarin kwatar kaina amma yaki ya kara damke ni yana cigaba da jana a kasa, wata karfe na hango a gefe, na sa hannu na dauko ba tare da ba'ta lokaci ba na daga karfen na soka masa a kafa, wani irin kara ya sake cike da tsananin jin azaba ya sakeni, ina jin kaina free na soma baya baya ina neman hanyar guduwa, ya sake yowa kaina gadan gadan, karfen na sake dagowa zan caka masa yasa hannu ya kwace daga hannuna ha'de da kaimun wasu maruka lafiyayu guda biyu a fuska yasa hannu ya shako mun wuya " ni kika jiwa rauni haka? Toh wlh yau na lahira sai ya fiki jin dadi, sai nayi fata fata dake yau, gobe bazaki kara ba "

Kafun kwakwalwata ta gama processing abunda yake fa'di naji ya daukeni cak ya sa'pa a kafadarsa ya karasa dani cikin gidan, Maryam na tsaye ta bude masa kofar bai tsaya ko ina ba sai dakin da suka killaceni, muna shiga cikin dakin ya jubgeni a kasa kamar kayan wanki, cikina ya bugu da simintin kasa, wani irin kara na sake na rike cikina cike da tsananin azaba na kudundune a wajen na rintsa idanuna hawayena zuba mun, wani irin azabar radadi nakeji tun daga marata har zuwa tafin kafata kamar ana zare mun rai, karan saukan zip din wando dana ji ne ya farga dani na bude idanuna naga ya yo kaina gadan gadan yana jan wando na zaro ido, nasan abunda yake kokarin yi, na soma kokarin jan kafa don babu yanda za'ayi na bari Kawu Abu yayi raping dina, sai inda karfina ya kare.

Sai faman ja da baya nake ina zaro ido ya cigaba da dingisawa yana jan kafar dana caka masa karfe, ina kaiwa daidai jikin bango naji saukar hannunsa a kaina, na sake wani irin razananen kara na kamo fuskarsa da iyakacin karfina na kai bakina kunnensa na damke da hakorina ina ja, wani irin ihu ya sake yana kokarin kwatar kunnensa daga bakina naki sakewa har sai dana ji jini ya fito, sai faman ihu yakeyi duk yabi ya rikice yana kokarin kwatar kansa ni kuwa na kara kankameshi ina rike da kunnen, da kyar ya samu ya kwaci kansa naji ya hadeni da jikin bango, kaina ya bugu da ginin na sake zubewa a kasa nan take sai ga jini ya ba'lle mun yana gangaro mun bisa kafafuna, kara na sake naji dakin ya soma juya mun ina ganin dishi dishi, shi kuwa sai faman tangal tangal yake yana rike da kumnensa yana ihu, ya karasa gefen dakin yaje ya dauko wata katako daga yashe a kasa ya nufoni dashi da niyar zai raga mun, ina kwance a wajen cikin jini na kasa motsi, lumshe idanuna nayi ina jiran naji saukan katakon akaina don na rigada na sadakar.

Not edited please.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now