Chapter 61

1.2K 67 3
                                    

Hibba

Mun gama shiri kenan da Faheema nasa mata kaya ya rage hijab dinta na tambayeta ina ta ajiye tace yana dakin daddynta, mikewa nayi nace ta jira naje na dauko mata, a hankali na fito na karasa hanyar zuwa dakinsa, na soma knocking amma shiru banji an ansa ba yasa na dan bude handle din kofar a hankali na leka ha'de da sallama, wani irin sanyayen kamshi mai dadi naji ya ziyarci hancina lokaci guda, a hankali naja dogon numfashi na fezar sa'anan na cigaba da leke leke, still shiru kamar da alamun babu kowa cikin dakin, hijab din Faheema da nake nema na hango kan gado, a hankali na saki handle din kofar na karaso cikin sauri wajen gadon na dauko hijab din, har na juya zan fita naji murya a bayana an dakatar dani " saurin me kikeyi haka?"

Cak na tsaya kirjina na harbawa da karfi, bansan ta daga ina ya bullo ba, a hankali na soma juyowa idanuna suka sauka kansa na ganshi tsaye daga shi sai iya towel daure bisa kugunsa, fatar jikinsa wet da alamun wanka ya fito, nan take naji wani irin abu ya tsargar mun nayi saurin kawar da kaina gefe ina nuna masa abunda na ruko a hannu "hijab din Faheema nazo dauka"

Bai ce komai ba, a hankali naji ya soma takowa har yazo ya tsaya dab dani, ina jin saukar numfashinsa a bayana, ina jin yanda bugun kirjina ke karuwa, unexpectedly from nowhere naji ya rungumoni ta baya ya manne ni da kirjinsa yana ajiyar numfashi a hankali yace "ya kike ji yanzu, are you okay now?"

Gyada masa kai kawai nayi ina jin yanda zuciyata ke bugawa, so many things were running through my head at that moment, naga yanayinsa ya danyi improving yanzu ba kamar na dazun ba, so nake na tambayeshi akan Maryam sai kuma na kasa naja bakina nayi shiru don ban san amsar da zan samu ba, Munfi minti biyar tsaye a hakan yana rungume dani ta baya yana ajiyar numfashi, A hankali naji saukar hannayensa duka biyu bisa waist dina ya kara matsoni jikinsa kamar zai shige jikina ya kaimun kiss a gefen wuya a hankali, wani iri sanyayen dadi ha'de da kasala naji ya tsagar mun lokaci guda tun daga tsakiyar kaina har zuwa tafukan kafana naji ya ratsani, ban san sanda nayi relax a jikinsa ba ina sauke ajiyar zuciya na lumshe ido, jin nayi relax a jikinsa ne yasa ya cigaba da abunda yake ya soma shafar waist dina through abayan dake sanye jikina da smooth hands dinsa har zuwa bayana, gabadaya cells din jikina sun dauka da abunda yake mun, tun da nake dashi ban ta'ba jin dadin abunda yake mun ba irin na yanzu, naji ina matukar son abunda yake mun gabadaya jikina yayi weak na kasa hanashi, a hankali yake bin duk sassar jikina yana matsewa yana shafa yana hura mun iskan bakinsa ta kunne babu abunda kakeji a dakin sai saukar numfashin mu, muna cikin haka ya juyo dani muna fuskantar juna, kyawawan idanunsa da suka canza launi tsabar jarabar dake cinsa ya zubesu kyam a kaina, a hankali yasa hannunsa ya soma bin fuskata dashi, yana shafa a hankali kamar yana kokarin memorising shape din fuskata, ya dau few seconds yana hakan sa'anan naji ya fada a hankali muryarsa kasa kasa "you're so beautiful"

A hankali na bude idanuna suka sauka kansa, naji nunfashina ya tsarku ganin irin kallon da yake bina dashi, kallona yake with so much care and affection in his beautiful eyes, and I felt it deep inside my soul, tunda nake babu wanda ya ta'ba dubana da irin wanan expression din cike da tausayawa tun rasuwar iyayenmu, wani abu ne naji ya taso ya tokare mun kirjina, naja numfashi na fezar da kyar, a hankali ya matso da fuskarshi dab da nawa ya ha'da fuskan mu wuri daya ya manna goshina da nashi, hancinmu na gogan juna ya ruko hannuna ya sakala da nashi yana ajiyar numfashi ya lumshe idanunsa a hankali sa'anan ya bude ya zubesu cikin nawa muna kallon juna still fuskokinmu a manne dana juna, a hankali na lumshe ido ina sauraronsa, ji nake kamar mu dawama a hakan nidashi.

Sai faman ajiyar numfashi muke can kuma kamar wani abu ya tsikareshi unexpectedly naji ya juyar dani ya daukeni cak, a kidime nayi saurin bude idanuna naga yayi hanyar gado dani, "Hassan... me zakayi?"

Murmushin dake kara masa kyau a duk sanda ya yita ya sakar mun ya ajiyeni a gefen gado yana shafar fuskata yace "me kike tunanin zanyi?"

Kara zaro ido nayi na girgiza masa kaina "kace zamuyi baki, kuma Faheema na jirana"

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now