Chapter 82

1.1K 77 6
                                    

Hassan

Four consecutive days kenan da Hibba ta dauki wanan dogon fushin dashi, 4 good days da baya samun koda sannu ballantana murmushi daga gareta, yaji duniyan ta tsaya masa, gabadaya ya rasa meke masa dadi. Ya bada hakurin yayi magiya amma still har yanzu tana kan fushinta, gabadaya ta tattara shida Ammar ta watsar.

Yauma yana zaune a gida a parlour yayi shiru yayi zurfi cikin tunani, shi kadai yasan yanda yake ji cikin zuciyarsa, damuwa ne suka taru suka addabi zuciyarsa, lamarin nan daya shiga ciki da Hibba yasa yaji komai ya sane masa a rai, ko abincin kirki baya samu yasa a cikinsa, ya kara ramewa sosai, he's now a shadow of himself, a cikin wanan yanayin AK ya shigo ya tadda shi yana faman mishi tsiya akan ina ya ajiye wayarsa tun dazun yanata faman kira bai da'ga ba, tsaki Hassan yaja yace oho shi bai masan inda ya jefar da wayar ba.

Yanda Hassan ya bashi ansa yasa AK ya karaso yazo ya zauna a gefensa yana fuskantarsa ya lura da yanayin da yake ciki "Sooraj wai ya ake ciki ne... kwana biyun nan naga you're not yourself, what's going on? Akwai abunda ke damunka ne?"

Shiru Hassan yayi yana duban wani gefe sa'anan ya sauke ajiyar zuciya "AK...Hibba ta gano tana dauke da juna biyu and she went ballistic yanzu haka ma maganar da nake maka ko magana bata mun, nayi iya kokarina na fahimtar da ita amma taki ji, tana ganin mun ha'da baki nida Ammar, I never meant to hurt her but she refused to see reason"

Shiru AK yayi sa'anan yace "her reaction is understandable, dole taji wani iri, you don't blame her for reacting this way ace ta waye gari ta tsinci kanta da ciki but ka sanar da ita auren dake tsakaninku?"

"She knows, ta sani"

"And how did she take it?"

"Ai ina jin sanar da ita auren shine ya kara hura wutan, I was hoping it'll calm her down but it was the opposite, har cewa take a cire mata cikin bata so, wlh AK I'm tired I don't know what to do, it's eating me up everyday I can't afford not to have her near me or talking to me, I crave her presence and everything around her, I wish things turned out differently, what if da gaske take bata so and she doesn't want to be with me? What do I do?"

Shiru AK yayi yana kallon abokinsa cike da mamaki yanda duk yabi yabi ya marairace ya shiga cikin damuwa akan wanan yarinyar, abunda bai ta'ba gani ba a tattare dashi, Sooraj din daya sani ada will never become like this over a woman, sai yanzu ya kara tabbatar wa kansa cewa his friend is far gone, yayi nisa baya jin kira akan soyayyar da yake mata, dafe kafadarsa yayi yace "I'm supposed to take a flight back to Abuja this evening amma zan da'ga, zanje na sameta muyi magana, i'll try and make her see reason, dazan ce kadan ba'ta lokaci har ta huce but I don't think only that will work, zanje na mata magana yanda zata fahimta kuma insha Allah nasan zata sauko, Hibba loves you, duk cikin harkokinmu da irin mata da suke shigo cikin rayuwarmu ban ta'ba ganin yarinya mai kamun kai da nutsuwa irinta ba, she's only hurt because she thinks you took her only virtue without her permission, saukin abun dai thank God you married her when it happened, so zaisa ta dan sassauta, don't worry Sooraj, you'll both be okay"

Ajiyar zuciya Hassan sa sauke yace "toh Alla yasa" da wanan suka shiga cikin wani chapter suka soma hiran abunda ya kawoshi.

*********************

Hibba

Ina kwance akan gado na kuna karatun Qur'ani surratul Nur recitation na Sudais ina sauraro, idanuna a lumshe ina bin karatun don ta hakan ne kadai zan samu na rage tunani tunanin da damuwa dake cina a zuci, ina cikin haka naji knocking aka turo kofar, a hankali na bude idanuna suka sauka kan Priya ta karaso tana murmushi tace nayi bako na tambayeta waye tace abokin mijina ne, maganar jinsa nayi bambara kwai a kunnena, ba yau Priya ta soma referring to Hassan a matsayin mijina ba amma yanzu data fada sai na jishi daban, tambayarta nayi ko waye tace AK, jimm nayi ina tunani sa'anan nace mata tace ya shigo. Tana fita na mike na gyara, bafi minti da'ya ba sai gashi nan yayi sallama ya shigo yana tafiyan nan nasa cike da kasaita da tsananin ji da kansa, tsakanin Lukman da AK bansan waye yafi wani daukan kai ba, ko aura dinsu idan sun shigo wuri daban yake, AK sanye yake cikin tsadaden suit as usual kamar yanda ya zame musu jiki shida Hassan, baka ta'ba ganinsu cikin wani shiga inba wanan ba, dama dama Hassan yana dan sa wasu kananan kayan amma sai in yana gida.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now