Chapter 2

1.7K 99 1
                                    

Hassan

Hassan yana zaune tare da yayansa Bashar, sai kuma kanansa Jamal da Sadik, sunzo taron welcome home party na yar' abokin mahaifinsu, Senator Isa Matawalle.

Mahaifinsu Hassan, Alhaji Sooraj Marafa d'an Taraba ne and is one of the most succesful business men a kasar dama Africa gabadaya, ko wani states yanada companies din da ake sarrafa mai, yanada hotels hotels da estates dinsa sunfi a kirga, tsayawa fadin kudinsa ma ba'ta lokaci ne don babu wanda bai sanshi ba, mutane ma da dama suna zarginsa shi da'an mafia ne, well they are not far from the truth saboda sunada nasu kungiya da suka kafa na billionaire elites kuma sunsa yaransu akai suna musu running. Tun suna kanana Alhaji Sooraj ya daurasu kan business dinsa, Ya shigo dasu duniiyarsu ta ruthless businesmen wanda only the fittest can survive, kuma ko wanansu nada kungiyan sun raraba. kungiyansu Hassan na da'ya daga cikin the richest billionaire elites da aka ta'ba samu. Dashi da Bashar yayansu, Alhaji Sooraj baya wasa dasu don sune in and out dinsa, kuma duk aikin da suka sa kansu cikin sai sunyi nasara. Opponents dinsu ta harkan business suna mugun shakkansu. Su maza shida ne a wajen mahaifinsu baida mace ko da'ya. Kuma a maza shidan, ko wane da mahaifiyarsa, Alhaji yaje kasashe daban daban yari aure aure kuma kowace haka zata haifar masa da'ya ko biyu ta kara gaba, daman yawancinsu saboda kudinsa suke aurensa, suna yagan abunda zasu yaga sai suyi gaba. A cikin matan daya aura, uwar gidansa Hajiya Bahija ita kadai ce yar kasa kuma yar Zamfara, yara maza biyu ta haifar masa da Bashar da Aliyu, Hassan shine na uku, kuma shi kadai mahaifiyarsa ta haifa a gidan, asalinta balarabiyar Misra ce, Hassan baiyi wayo ya ganta ba don tun yana karami ta tafi, daga Hassan sai Hamdan da Jamal su kuma mahaifiyarsu Yar America ce, auren mahaifinsu yasa ta musulunta, suna rabuwa ta koma ruwa abunta, na karshen ne Sadik shi kuma mahaifiyarsa daga can Vietnam aka aurota, kuma Muslimah ce, Sadik ne kadai mai fuskar yan china a cikinsu, kuma mahaifiyarsa kadai ce ta zauna a cikin matan, mahaifinsu ya sota sosai don tunda ya aureta bai sake roro wani auren ba, sai data rasu last year, ciwon cancer ya kasheta. Shine yanzu suka samu labari zai kara aure, wanan karan bai je waje ba anan Nigeria ya samu wata yar bafulatana daga Jalingo, abun daya fi basu Hassan haushi da takaici karamar yarinya ce bazata wuce 18 years ba, ko autansu Sadik ya girmeta, yarinya ce karama sosai. Shiyasa Sadik yafi kowa jin haushin abun, ya zata daga mahaifiyarsa Alhaji bazaiyi tunanin kara wani aure ba.

Suna zaune suna shakatawa a VIP section da aka ware musu ga kwalaban wine da drinks iri iri a gabansu, Jamal ne yaketa faman zukar sandar tabarsa yana fesarwa sai faman lumshe ido yake kamar mai bacci, suna cikin haka sai ga Afrah nan ta shigo tare da wani, Hassan na ganinta yaji wuta ya dauke masa nan take zuciyarsa ta fara masa wani irin tafarfasa, yaji kamar ya mike ya bar hall din.

"Meya kawota nan?"Sadiq dake zaune a gefe ya tambaya, na zata tana London tana masters dinta, yaushe ta dawo?" Ya karasa maganar yana bin Afrah da kallo wace taci uwar kwaliya sai faman daukan ido takeyi duk inda ta shiga.

"Taya zan sani? Ai bamu tare kuma". Hassan ya bashi ansa yana kallon wani gefe daban.

"Kai Afrah batada kunya, dubi karamin yaron da take yawo dashi yanzu, bashida maraba fa da wanan yaron Ammar.

A hankali Hassan ya soma bin yaron da kallo ya gasgata maganar sadik, bashida maraba da wanan wawan, naive Ammar daya bari aka damfare shi million da'ri, yaron daya so ya gina, yasa akan hanya saboda yaga kwazonshi amma dare da'ya yayi masa wanan uban asaran.

Bashar dake zaune a gefe ne ya katsesu da "Yauwa speaking of Ammar, ya kuke ciki dashi? Yana ina yanzu?"

"Yana wajen AK" Hassan ya bashi ansa kai tsaye

"What?" Sadik ya fada yana zaro ido, ya za'ayi ka bawa AK Ammar? so kake ya kashe shi?"

Gyada kai kawai Hasan yayi don yasan Sadik nada gaskiya, Ak mahaukacine, duk cikin abokanansa yafisu zafin kai, he's one of his best business partners da suke dashi kuma basu wasa dashi. Shiyasa da abunan ya faru ya dauki Ammar ya damka mishi.

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now