Hibba
Yau ina zaune tare da Ammar a asibiti sai ga kiran Hafsah, tunda ta karba numberna ta kirani so daya muka gaisa bamu sake magana ba, na da'ga kiran na kara a kunne, ta soma gaisheni cikin dan karamin muryarta, na tambayeta ya jiki, tace da sauki alhamdulillah, itama ta tambayeni ya jikin Ammar har yanzu muna asibitin ne, nace eh muna asibiti amma yanzu jikin nasa da sauki alhamdulillah, tace idan bazan damu zata zo ta ganni a asibitin mu dan samu muyi hira mu kara sanin juna, nayi jimm don ina tsoron yanda Hassan ko Lukman zasu dauki zancen, tace kar in damu ita batada matsala, Lukman yana barinta taje ko ina amma tare da bodyguard. Nace Toh shikenan, tace zata zo washe gari nace da ita Allah ya kaimu, bayan mun gama waya Ammar ya soma tambayata wacece, na fa'da mishi gashi gashi, har yanda mukayi muka ha'du, nace mishi kamar fa tana tare da Lukman ne,kuma ina tsoro, Ammar yayi shiru nasan yana tunanin irin wanan rayuwar d muke ciki, amma don ya kwantar mun da hankal naji yace kar na damu, da Hassan da Lukman sun san yanda suke harkansu, tunda tace zata zo na kyaleta tazo kawai tunda da alamu kamar tana sona da kawace, ya karasa maganar da" Ya' Hiba tunda muke ma ban ta'ba ganinki da wata kawa bafa"
"Hmm Ammar a cikin wanan halin da muke ciki ba ta kawa nake ba, our life is a mess already"
Shiru dukanmu mukayi ina tunanin yanda abubuwa zasu kasance, daga gani dai Hafsah bazatayi matsala ba, she seems so lost and innocent almost similar da halin da nake ciki, yanda tayi mun magana kamar tana mugun bukatuwa da wani kusa da ita, shiyasa naji kawai bazan iya hanata zuwa ba, we might need each other.
Washe gari sai ga Hafsah nan, tazo har dakin da aka kwantar da Ammar muka gaisa, suka gaisa da Ammar tayi masa sannu da jiki harda miko mana leda ta da'an siya masa fruits da lemuka masu sanyi, na dinga mamaki don da alamu batada matsala sam da Lukman yana sakar mata, godiya sosai muka mata nida Ammar daga bisani nida ita muka ja gefe muka soma hira, hira muka dinga yi sosai kamar wanda muka jima da sanin juna, tana sanar dani abubuwa da dama dake damunta a rayuwa, na soma tambayarta zamanta da Lukman na nuna damuwata sosai don zuciyata sam bata kwanta dashi ba, a tunanina zata kawo mun wani aibinsa sai naga ma kamar tana jin dadin zamanta dashi a hakan, yanda take mun magana kamar ta rigada tayi zurfi cikin sonsa, tace daba din Lukman ba da yanzu bata ma san inda rayuwarta take ba, ta soma sanar dani batun matar babanta da irin wahalar ukubar data sha a hannunta, har cikin karuwanci data so ta sayar da ita, sanadiyar haka ta hadu da Lukman, tace tun daga lokacin rayuwarta ta dan samu sauki daya dauketa ya kawota gidanshi, tace baccin jarabarsa Lukman yana nuna mata kulawa sosai.
Shiru nayi ina sauraronta nace "yanzu bakida ranar komawa gida kenan ga iyayenki?"
Shiru tayi daga bisani tace ta gwamace zamanta anan, tunda mahaifinta ya rasu rayuwarta batada wata ma'ana, gwanda tayi zamanta tare da Lukman, ko meye zaiyi da ita ta gwamace ta karasa rayuwarta dashi a hakan data koma ga wacen mayar mata a Ilorin.
Jikina yayi mugun sanyi, ashe bamu kadai bane muke cikin wanan ukubar ba, wasu idan kaji nasu ma sai sai ka godewa Allah..Hassan har yanzu dai ban gane manufarsa dani ba, don ni ban ma san meye matsayina ba, meye banbancin karuwa da mistress da yake kirana, godiyata da'ya ga Allah dayasa bai wani nuna yunkurin keta mun mutuncina ba, sai dai yanda abubuwa suke tafiya yanzu ban san me zai iya faruwa tsakanina dashi ba nan gaba. Tsoro ya sake ziyartata ina wanan tunanin. A haka muka cigaba da hira da Hafsah, har zuwa rana tukuna tace zata wuce mukayi sallama, nayi mata rakiya hade da godiya sosai bodyguard dinta yaja mota suka tafi.
Bayan kwana biyu da zuwan Hafsah, aka sallami Ammar daga asibiti, sosai nida Ammar muka ji dadin haka don ba karamin jinya mukayi ba, Hassan dai bai zo ba, don da alamun ma tafiya yayi baya nan, AK ya turo akayi settling komai na asibitin muka dawo gida.
Washe gari da safe na koma asibiti don na karbi sauran abubuwan da muka bari daga nan na samu na karbawa Ammar sauran drugs dinsa da suka rage, Habib ne ya kaini ya jira har na gama na fito, ina tafiya sai faman tunani tunani nakeyi, yanzu mun gama da asibiti mun dawo, ya rayuwar mu zata kasance? Ya Ammar fa? Hassan zaice mu koma Lagos ne mu cigaba da aikin contract ne ko yaya? Anya zan iya tafiya na bar Ammar a hannun waenan mutanen kuwa? Ga batun komawata Maiduguri da nakeso nayi, ban ma sanar dashi batun son komawata ba, gabadaya tunani a hargitse take.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...