Hibba
Bayan kwana biyu dai na samu jikina ya warware, mutuwan jiki ne kawai nake fama dashi, amma duk wani ciwo da nakeji ya lafa mun yanzu, yau dai na tashi a bacci lati, don tunda na farka nayi sallah asuba na koma bacci ban sake farkawa ba sai yanzu, naga gari ya waye sosai, wayata na janyo na duba time naga karfe daya saura, azahar har yayi, a hankali na mike naje na fara watsa ruwa a jikina don na samu karfi sa'anan na dauro alwala na fito na tada sallah. Ina idarwa na kwanta kan sallayan nayi lamo, tun ran dana kwanta ciwo naji gabadaya hankalina ya kasa kwanciya, na kasa gane meke damuna, why I'm feeling this way, har yau ban san takamame abunda ya faru dani ba, I'm just confused. My body feels different kamar ba nawa ba. Hassan ne ya fara fado mun a rai, tunda na fara ciwon nan wani irin kulawa na musaman yake bani wanda bazan iya kwatantawa ba, sai faman riritani yakeyi kamar kwai, he's action towards me yanzu is just different, yau ma banji fitarsa ba don da alamu tun da sassafe ya fice, ajiyar zuciya na sauke na janyo wayata na soma dubawa naga ya barmun sako tun karfe takwas na safe, ga miss calls din Ammar baja baja a wayata ha'de da na Hafsah guda biyu, tunda nayi wanan zazabin ban samu nayi magana da kowa ba, jikina na ba'ri na fara bude sakon da Hassan ya barmun na soma karantawa kamar haka
"Na fita.. I won't be back sai zuwa anjima, if there's anything you need let me know, ga breakfast nan kan dining"
Ina gama karantawa na sauke ajiyar zuciya na zauna anan ina uwar tunani, Hassan....abubuwa da dama ne suke mun yawo akai, har yanzu na kasa gane kan abubuwan da suke faruwa dani, irin feelings din da nake ji a game da Hassan wanda kullum kara bunkasa yake cikin zuciyata, gashi har yanzu ban san makomar relationship dina dashi ba, dole nayi kokari na nesanta kaina gareshi don waenan feelings din da nakeji idan aka cigaba a hakan bansan me zai biyo baya ba saboda zuciyata ta gama accepting dinsa, ta bashi mazauni na musaman a cikinta, bata ji bata gani sai shi, a kullum kara dilmiya nake cikin kogin sonsa, kuma hakan ba karamin firgitani yakeyi ba, yanzu dai kawai zan samu na hanzarta kowata Maiduguri ne, that's the only way out for me, da wanan tunanin yazo mun wani irin nauyi naji zuciyata tamun, kamar batayi amana da wanan batun ba, but I have to do it, I have to go back, don ko adadin dana dauka wajen aiki yayi harma ya wuce, bansan me zanje na tarar a wajen madam dinmu ba idan na koma. So idan ya dawo dole mu zauna mu tattauna, na fahimtar dashi ya barni na koma, bansan ya zai dauki zancen ba amma zan mishi bayani ta yanda zai fahimta. Da wanan tunanin na mike jiki a sanyaye na fito parlour, kamar yanda ya fada ga breakfast nan an tanada mun yan jirana tun safe, nasan kilan yanzu abincin ma ya gama sanyi. A hankali na karasa na soma budewa naga chips ne da kwai da ketchup sai kuma kayan tea, tea din kawai na ha'da don yanda nakejin kaina yanzu bazan iya wani cin abinci ba. Ina cikin shan tea wayata ta soma ringing na duba naga shine ke kira, kirjina ya harba, ba tare da ba'ta lokaci ba na da'ga na kara a kunne.
"Sweetheart kin tashi?" Naji muryarsa ya doki kunena
"Eh" na bashi ansa muryata kasa kasa
"Kinci abinci?"
Shiru nayi ina tunani sai kuma nace masa eh kawai.
"Me kikeso na kawo miki?"
Shiru nayi bance masa komai ba,
"You're quite"
"Bakomai" na fada mishi cikin sanyin murya.
"Toh shikenan... na kusan dawowa kinji"
"Toh" kawai nace shi kuma ya katse kiran, ban gama ajiye wayar ba sai ga kiran Ammar, cikin sauri na da'ga daman so nake na kirashi sai ga kiranshi ya shigo.
"Hello Ya' Hibba... ya jikin naki?" Ya tambayeni muryarsa cike da damuwa.
"Da sauki Ammar"
"Mr Sooraj yake sanar dani baki ji dadi ba, jiya nazo na dubaki kina bacci, meya sameki Ya' Hibba?"
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...