HibbaIna kwance akan gado, idanuna a lumshe ina sauraron Hassan wanda ya kira yaji ya nake, tun dazun yaketa faman jana da hira ni kuwa ina zuba masa shagwaba son raina, muna cikin hirar naji anyi sallama aka turo kofar aka shigo, ganin Anty Zaliha ce yasa nayi saurin ce masa zan kirasa ga Anty Zaliha nan yace toh ya katse kiran, hannunta dauke da cup ta karaso ciki tana murmushi "ashe idonki biyu na zata kina bacci ne"
"Idona biyu Anty, ban ma jima da kwanciya ba"
Wuri ta samu ta zauna tana fuskantata ta miko mun cup din dake hannunta "ga hadin garin gumba nan da madara Hajiya tace na deba na kawo miki, jiya aka kawo mata daga Chad, hadin maganin nada kyau sosai ki maida hankali kina sha, za kiji dadinsa sosai nima musaman take sa ana aiko mun a U.S"
Hannu nasa na karba kofin ina duba ciki, maganin a dame yake gashi yaji madara, wanan shine magani na uku da Anty Zaliha take kawo mun ina sha, godiya na mata ita kuma ta mike "babbu wani abun da kike bukata a kawo miki?"
Na girgiza mata kaina "a'a babu komai Anty, nagode "
"Toh shikenan bari naje nasa ido akan yaran nan"
"Toh Anty nagode, sai na sauko"
Tace yauwa, juyawa tayi ta fita ni kuwa na kurawa maganin ido ina tunanin shansa, cokalin dake ciki na soma stirring maganin sa'anan na kawo bakina nayi tasting, naji taste din babu laifi don haka na kafa kai nasha, ina gama sha na ajiye kofin na koma na kwanta, na janyo wayata na kirashi muka cigaba daga inda muka tsaya, ya sani a gaba yana fa'din yayi missing dina, abunda yakeyi ma a office ya kasa concentrating, tunanina ne kawai ya cika masa kai, dariya na dinga masa a waya cike da jin dadin kalamansa, yace wato ma dariya nake masa toh gashi nan zuwa na shirya tarbansa, nace mishi toh sai yazo nan muka cigaba da hiran mu har ya katse kiran.
*******************
HassanDa yamma ya shigo gidan, tun kafun ya karaso ciki yake jin hayaniyansu Faheema na tashi, yana sallama kuwa suka nufo shi a guje suna mishi oyoyo, daya bayan daya ya daga su tun daga kan Noulah yana juyi dasu sai faman kyalkyalewa da dariya suke, suka gaisa da Hajiya ya bata ledan daya ruko cike da ice-cream da chocolates yace a raba musu, ihu da tsalle yaran suka shiga yi suna masa godiya, Hajiya taji dadi sosai itama tayi masa godiya, suna cikin haka sai ga Hibba nan ta sauko kamar taji shigowarsa, sanye take cikin lace dinki riga da skirt six pieces, kayan ya zauna carass a jikinta, suna ha'da ido ta sakar masa lalausar murmushi wanda yasa zuciyarsa harbawa da karfin gaske, sosai ya shagala da kallonta, wani irin kyau na musamman yaga ta kara masa har wani glowing takeyi, a hankali ta karaso tana mishi sannu da zuwa, hajiya ta dubesu tace "kin sauko, daman yanzu nake shirin na kiraki, tunda kin zo ki gaishi sama ya huta ki bashi abinci yaci ko ba haka ba"
Hibba ta ansa da toh, a hankali ya mike daga inda yake zaune suka haura sama still idanunsa na kanta, tana gaba yana binta a baya, rigar data sa ya dan' matseta daga sama amma ba irin matsar nan da zai hana mutum numfashi ba, daurin dankwalin datayi ya zauna mata carass, a hankali iska yake buso masa kamshin jikinta, yana son kamshin jikinta sosai nan take yaji wani irin sha'awarta na taso masa yana bin sansar jikinsa har suka karasa hawa matakalan sai daya tabbatar sun ba'cewa idon Hajiya ya kamo hannunta cike da shaukin kaunarta ya juyo da ita tana fuskantarsa "kinyi kyau sosai sweetheart"
Cike da jin kunyarsa tace "Allah ko?"
"Sosai ma kuwa"
"Waya miki wanan daurin"
"Ni nayi da kaina"
"Da gaske?"
Ta gyda masa kanta
"Daga yau ki dinga yi, daurin yayi miki kyau sosai"
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...