4 days 14 hours Sadik yayi spending a wanan unit din tukuna ya farfado, zuwa lokacin Alhaji ya gama shiryawa za'a fita dashi waje, hankali ya tashi sosai.Ko daya farka da wani irin azababen ciwon kai ya farka, ga bandage da aka zagaye mishi kanshi dashi, murna aka fara Yi ana Hamdallah, Hajiya kamar zata mayar dashi ciki, ta janyoshi jikinta sai faman masasannu takeyi, sai dai murna yazo ya koma ciki don Sadik kallonsu kawai yakeyi da'ya bayan da'ya kamar bai ta'ba ganinsu ba, aka je aka kira doctors suka zo suka soma dubashi nan sukayi confirming concussion dinne yayi masa causing amnesia abun yayi affecting some parts of his brain, but a hankali memories dinsa zasu dawo, kuka Hajiya ta fashe dashi tana tambayar yanzu Sadik dinta haka zai kasance baya gane kowa? Doctors suka ce tayi hakuri tunda Allah yasa ya farfado toh a hankali he'll start remembering, they should be patient and take it easy with him. Hassan couldn't bear it ganin halin da kaninsa yake ciki, zuciyarsa cike da bakin ciki da tsantsar nadama, ji yake dama shi yaje da Faheema a ranar bai aika Sadik ba. Gabadayansu hankalinsu a tashe yake, Hajiya ta mike sosai ta dage da rokon Allah akan dan'ta, Kullum safe rana da dare tana nan kan sallaya a asibiti, kotu Alhaji Sooraj ya maka mahaifin Afrah da ita Afrah din harda uwarta da duk wani nata daya san keda hannu cikin wanan aika aikan, akayi charging Afrah against attempted murder da kuma kidnap, Mahaifin Afrah da uwar aka sakosu, ita kuma Afrah aka yanke mata shekara hudu a prison, sunan family ya ba'ce sosai daman mahaifin nata yana shirin ya tsaya takarar zabe, haka ta ba'ta mishi political career dinsa, jininsa ya hau sosai ganin everything he has worked for is crumbling before his very eyes yana kara blaming matarsa akan duk ita ta jawo masa wanan matsalar batayi training yar'su ta bata tarbiyan daya dace ba, yace ko kwandala nashi bazai kashe akan Afrah ba taje can ta karata a prison din.
Watansu biyu a asibiti aka sallamo Sadik, zuwa lokacin alhamdulillah jikin nasa yayi sauki sosai, a hankali yake recovering yanzu dai yana gane yan'uwansa sosai, sai dai wasu abubuwan ne baya iya tunawa, suka dawo gida yana samun special treatment da kulawa, Nuratu kam duk wani abu daya danganci kula dashi tanayi, rai da rai tana tare da Hajiya harta girki ita takeyi ta kai masa, Jamal daya lura da hakan ta'be baki yayi ya kaiwa Hassan gulma, yace how the tables have turned never in a million years would he think something like this would have happened to Sadik. Murmushi kawai Hassan yayi yana girgiza kai shi dai fatansa bai wuce Allah ya karawa kanin nasa lafiya ba.
Yauma kamar ko wace rana, Nuratu na part din Hajiya suna kitchen sun gama ha'da abincin rana, Hajiya tace ta dauko cooler ta zubawa Sadik nashi da plates da magungunansa ta kai masa daki, Nuratu tace toh. Tana gama zuba abincin tayi arranging dinsu kan tray ta fito ta karasa part dinsa tayi knocking akan kofar ya bada izininin shigowa, sallama tayi ha'de da turo kofar ta shiga ciki, yana zaune kan kujera 3 seater, system ce kan cinyarsa yana operating yana sanye cikin kananan kaya na shan iska, tunda ta shigo ya zuba mata manyan idanunsa da suke firgitar mata da zuciya ko kyaftawa bayayi har tazo ta dire abincin a gabansa, "ga abinci nan Hajiya tace idan ka gama kasha magungunanka"
Bai ce da ita komai ba, harta mike ta juya zata fice ya dakatar da ita, a hankali ta juyo tana dubansa da kyawawan idanunta masu matukar kyau da haske, maganar daya fito daga bakinsa ne yasa tayi saurin ha'da ido dashi "ya sunanki?"
Batayi mamakin wanan tambayar nasa ba don kusan from time to time abun yana kwace masa sai dai abunda yafi bata mamaki shine maganar da yayi mata don tunda aka sallamosu suka dawo daga asibiti take kawo masa abinci bai ta'ba mata magana ba duk sanda zata kawo masa abinci sai dai tazo ta dire masa abincin yayita binta da kallo amma bazai ce da ita uffam ba, a hankali ta bashi ansa da "sunana Nuratu"
"Nuratu...." ya maimaita
"Toh baki zuba mun abincin ba zaki tafi"
Still cike da mamaki take kallonsa amma bata ja' ba a hankali ta karaso tana tafiyarta a nutse har tazo ta durkusa ta bude cooler ta soma zuba mishi abincin, komai nata a natse takeyi sam batada rawar kai, jollof rice ne da peppered turkey sauce da pasta Salad a gefe, abinci sai kamshi yake fiddawa, tana gamawa ta mika masa, godiya yayi mata ya karba daga hannunta, abun yayi mugun bata mamaki, wai Sadik ne yau yake mata magana harda godiya?
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...