Hassan
Tunda Hassan ya gama tabbatar wa kansa cewa eh da gaske ne Hibbansa ta ba'ta, ya dawo very calm and quite kamar bashi ba, magana ma bada kowa yake yi ba, ya dawo very dark and dangerous kallo daya zaka masa ka gano cewa wanan shurun da yayi bana lafiya bane.
Yanzu haka zaune yake ya kurawa surveillance camera ido, sosai ya zurfafa cikin tunanin da yake yana kallon camera din, damuwa ce ta taru tayi masa katutu cikin ransa shi kadai yasan yadda yake ji cikin zuciyarsa, su Jamal ne suke tare dashi a parlourn, don suma tunda suka samu labarin batan Hibba suka zo gida, gabadayansu babu wanda ya rintsa cikinsu musaman ganin halin da yayansu yake ciki. Jamal ne ya karasa inda Hassan yake zaune ya soma fadin " Ya'ya... Munyi assemble team din"
Sadik shima yasa baki yace "nasan it won't take them long, yanzu zasu iso"
Gyada musu kai Hassan yayi ya cigaba da kallon surveillance camera din yana kokarin dubawa ko Allah zaisa ya gano wani abu, Sadik da Jamal suma suka matso suna duba records da camera tayi capturing na gidan a ranar da Hibba ta ba'ta, da'ya bayan da'ya suka soma duba video clips din sai dai shiga da fitan mutane da kuma fitan da tayi a ranar kawai clip din ta nuna musu. Harta CCTV da akayi setting a perimeter na estate din babu wanda basu duba ba amma babu komai, gashi number Hibban a kashe take tun jiya babu halin yin tracing, anytime yayi trying sai ace masa switched off.
Wani irin wahalalen numfashi Hassan yaja ya fezar yana rike kansa, yanzu haka suspicions dinsa akan mutum daya ne tak kuma bai wuce kawu Abu ba, Allah kadai yasan halin da take ciki a hannun wanan kasurgumin dan iskan, kwakwalwarsa ce ta shiga hasko masa every possible thing da zai iya mata nan take hannunsa ya soma rawa, zuciyarsa ta soma masa wani irin ligudin bugu cikin kirjinsa don bazata iya juriyar tunanin wani na kokarin ta'ba masa ita ba, Hibba..Matarsa....daya tuno wanan sirrin cikin zuciyarsa, bai san sanda ya mike a fusace ba, yana busa numfashi daga cikin bakinsa, gabadaya he's confused babu composure a tattare dashi, Jamal ne ya matso ya dafa kafadarsa "kayi hakuri yaya nasan abun da ciwo, I understand how you feel but kada mu karaya da wuri, suna zuwa zansa su duba mana surveillance records na satin da suka wuce ko Allah zaisa mu samu wasu clue"
"you can go ahead but already I have my suspicions"
"Haba wa kake tunanin yakeda hannu cikin wanan ba'tan?" Sadik ya tambaya yana dubansa.
Ajiyar zuciya Hassan ya sauke yana yamutsa hannunsa cikin kwantaciyar sumarsa yace "kawunta daga Maiduguri"
"kawunta?" Suka maimaita a tare
Hassan ya gyada musu kai "abunda nake tunani kenan don tuntuni yake bibiyarta, but I never knew he'll go to this level har yace zaiyi kidnapping dinta"
"Ban gane ba yaya, kana nufin kawunta daga Maiduguri yake bibiyarta har Lagos? Ya akayi hakan ta faru? Ita Hibban ce ta gaya maka he's after her?"
"dan iska ne kuma tatace, tun isowarta nan ta soma bani labarinsa, so at that time nasa men dina su mun bincike akansa but I never knew he'll get to this length, duk sakacina ne wlh! I let my guard down, yayi striking when I least expected, He's a fucking sick bastard and I'm going to kill him when I lay my hands on him!"
Gabadayansu a wajen jikinsu yayi sanyi, Jamal yace "we need hardcore evidence to confirm this fact Yaya, Men din sun soma taruwa, at any moment sauran zasu iso, so we need to start planning our actions now, suna zuwa zansa su fara duba surveillance cameras na estate din gabadaya duk wani shiga da fitan mutum for the past weeks zai nuna mana"
Kamar yanda Jamal ya fa'da, bafi 20 minutes ba Men din suka iso, yanayinsu ma kadai abun firgitarwa ne don they were heavily armed and highly trained, su guda ashirin. Ndagi ne a gaba don shi ya riga dukaninsu isowa, yana gaba tare da sauran suna tsatsaye suna sauraron Hassan yana musu bayanin situation din da kuma yanda zasu bullowa lamarin. Bayan Hassan ya gama briefing dinsu, Ndagi ya karaso inda yake yana fa'din "kayi hakuri boss duk laifina ne, dana kamashi tun farko da duk wanan bai faru ba, I'm really sorry"
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...