Hibba
Ina zaune a parlor tare da Faheema, muna kallon wani animation a tv, bamu jima da gama yin video call da Ammar ba wanda ya kasance yana Singapore, tun ran daya isa kasar mukayi waya ya sanar dani na dinga hamdallah ina godewa Allah daya sani naga wanan ranar wai yau Ammar ne a kasan waje, kuma ya bar kasan ne don yaje ya cimma burinsa ya samu ya gina future dinsa, abunda nida shi muka da'de muna addu'a akai, yace mun yana isa cikin satin immediately ya fara karatunsa tunda already AK ya rigada yasa anyi masa processing komai tun kafun ya isa,kuma duk abunda yake bukata a wadace yake, ai Hassan nasa a gaba nace ya kira mun AK don na kara masa godiya, haka ya kira mun shi muka gaisa na dinga masa godiya akan wanan dawainiya da dinbin kulawar da yake nunawa kanina, nayi mishi godiya kamar ba gobe, dariya kawai ya dinga yi yace babu komai ai an rigada an zama da'ya, yace shidai fatan shi na rike masa abokinsa amana kuma hannu bibiyu kuma na kula dashi kar na zuba musu kasa a ido, nace insha Allah, a raina ina fa'din har abada babu abunda zai shiga tsakanina da mijina ko ya rabani dashi, nida shi mutu ka raba, toh ya kasance haka kullum sai munyi waya da Ammar ta video call naji ya yake, kuma tunda ya fara it's either yace mun yana class ko kuma yana library yana karatu, yauma kamar kullum munata shan hira dashi harda Faheema, karshensa bar mata wayan nayi tanata surutu dashi shima yana biye mata, na lura Ammar yana son maganar Faheema sosai jininsu ya ha'du, ko waya mukayi dashi maganarsa daya biyu ina Faheema, ko dayake Faheeman ce tanada shiga rai, duk wanda ya kasance da ita kona second daya ne sai ya sake son kara kasancewa da ita, yanzu haka tana kwance kan cinyana mun gama cin abinci munyi sallah isha'i tare, lokaci na duba naga ana neman tara saura, na janyo wayata ina kokarin kiran layin daddynta amma naji number busy don haka na tura mishi text, ba jima ba yayi mun reply yace gashi nan yana hanya, nace okay Allah ya kawoshi lafiya. Jin Faheema shiru akan cinyana yasa na lekata naga ta soma gyangyadi alamun bacci ya soma awon gaba da ita, "Faheema...Faheema?" Na dan jijigata ina kiran sunanta a hankali
A hankali ta bude idanunta
"na'am....mommy"."Bacci kikeyi... bazaki jira daddy ya dawo ba?"
"Z..zan jirashi" ta bani ansa muryarta cike da bacci.
"Toh ki bude ido, daddy nanan zuwa ya kusan karasowa kinji?"
Gyda mun kai kawai tayi amma idanunta a lumshe, ajiyar zuciya na sauke don nasan tunda baccin nan ya riketa ba farkawa zatayi ba sai wani ikon Allah, ban sake yunkurin tashinta ba nabarta na cigaba da kallona, bafi 10mins ba sai gashi nan ya shigo, tunda naji karar shigowar motarsa naji zuciyata ta fara harbawa cike da shauki da dokin son ganinsa, ina jin sallamarsa na gyara Faheema na kwantar a gefe na mike jikina na ba'ri naje na fa'da kirjinsa ya rungumeni tsam yana ajiyar numfashi, nima ajiyar numfashin na sake cike da jin dadin ganninsa ina jin wani irin farin ciki har cikin raina "sannu da zuwa my heart"
A hankali ya da'go jin sunan dana kirashi dashi, ni daman tuntuni nayi saving sunansa da haka a wayata, saboda a yanzu shine zuciyata dama gangan jikina gabadaya idan babu shi babu ni, he's my everything. Murmushi ya sakar mun yace "yauwa my sweetheart, ya kike?"
"Lfy lau...ya kayi dare yau, ko aikin ne?"
Ajiyar zuciya ya sauke "kedai bari kawai"
"Sannu dear" na fa'da ha'de da karban jakan daya ruko, na kamo hannunsa muka karasa cikin parlourn, a hankali idanunsa suka sauka kan Faheema dake kwance kan 3 seater "gimbiya tayi bacci ne?"
"Eh wlh tayi bacci nayi nayi da ita ta jiraka amma baccin yaci karfinta, yanzu zata sani a gaba da safe tace na bari tayi bacci bata samu taga daddy ba"
Murmushi ya sauke ya karasa yana shafan gefen kumatunta, ni kuwa na karasa kitchen naje na debo masa ruwa mai sanyi na kawo masa ya karba yasha ina masa sannu, na lura kamar ya kwaso gajiya don kishingida ma yayi akan kujeran da yake zaune ya afka wani tunani, hannu na mika masa nace "muje kayi wanka sai na kawo maka abinci kaci"
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...