Hassan
Kamar yanda Jamal ya daukarwa yayansa alkawari suka je suka sami Hajiya shida Sadik, suka sata a gaba, da farko kin sauraronsu tayi tace su tashi su bata wuri, amma suka nace, barin ma Sadik daya like mata ya dinga mata magiya dole ta sauko ta dan' sauraresu, da farko dai nuna baccin ranta tayi sosai tace wato harda hadin bakinsu, suma sunsan da zancen suka ha'de kai sukayi shiru, rantsuwa suka shiga yi sukake ba ha'din baki bane, dan Allah tayi hakuri, ta dauka kawai haka Allah ya rubuto yayansu zai kara aure kuma ta kwantar da hankalinta wanan karon yayi zabi mai kyau, wanan ba anyhow yarinya bace karta ma ce zata ha'data da Afrah don wanan ta yiwa Afrah fintinkau, sosai suke zaqe sunata yaba Hibba a wajen Hajiya, abun ya bawa Hajiya mamaki sosai dole ta dan sauko, musamman ma yanda taga Sadik ya za'ke, Sadik da ko sama za'a hau a sauko bazai ta'ba bude baki yace zai yaba wata ba amma sai gashi yau da bakinsa yake yaba wanan matar da yayan nasa ya aura, gabadaya interest in Hajiya yayi picking sai taji tana so taga wanan yarinyar da Hassan ya zabi yabi ta bayan fa'ge yaje ya aura ba tara da ya sanar da ita ba, duk cikinsu harta wanda ta tsuguna ta haifa tana balai'n ji da Hassan saboda nutsuwarsa da hankali tun yana karami, tana son Hassan sosai, shiyasa abun yayi mugun kona mata rai. Bata dai ce komai ba har suka gama bayani da magiyan nasu suka tashi suka tafi, Jamal ya kirashi ya sanar dashi yace ta dai dan' sauko dukda dai bata wani bada fuska ba, Hassan yace okay insha Allah zai shigo anjima, toh dai hakan akayi da yamma Hassan ya shigo kai tsaye part dinta ya shiga, Nuratu ya fara gani, kanwar amaryar babbansu zaune a parlourn, yayi mamaki sosai don tunda akayi auren bai sake dora idanu akansu daga ita har yayar nata ba, koda yaushe suna part din da aka ajiyeta. Ko dayake ba abun mamaki bane ganin Nuratu a bangaren Hajiya ba don ita daman kowa nata ne, cike da girmamawa Nuratu tace "ina yini Ya'ya"
"Lfy lau" Hassan ya ansa fuskarsa babu yabo babu fallasa
"Hajiya na ciki?"
"Eh tana ciki"
Kafun ta gama rufe baki sai ga Sadik nan ya sauko, yana sanye cikin kananan kaya riga da wando da sukayi fitting dinsa, da key din mota a hannunsa allamun fita zai yi yana ganin Hassan yace "ah yaya ka shigo..."
"Yeah yanzu shigowa na kenan"
Nuratu na ganin saukowar Sadik ta mike Kirjinta na bugawa da sauri ta fice ta basu wuri, Sadik yabi bayanta da kallo ransa a ha'de "munafuka kawai"
"Kai meta maka da zaka kirata da wanan sunan, what's wrong with you?"
"Toh yaya idan ba munafunci ba meye ya kawota nan part din, suyi zamansu a can mana dole sai sun shigo wanan side din"
"Kaima kasan ko basu zo ba Hajiya zata gayacesu, she's open to everyone, so let the girl be please"
"Wlh na tsani gidan nan.. abunda akeyi ya isheni Alhaji na dawowa zanje na sameshi ya bani makulin gidana nayi gaba, idan bana nan suyi duk abunda zasuyi, na tsani na bude idona naga fuskokinsu"
Ajiya zuciya Hassan ya sauke ya nemi wuri ya zauna don ya gaji da mitar Sadik, idan yaga dama yabar kasar wanan shi ya sani, tsaki yaja yace "Dan Allah ka haura kacewa Hajiya na iso"
Sadik bai sake cewa komai ba ya koma ya haura sama ya isar da sakon zuwan dan'uwansa sa'anan ya sauko "gata nan zuwa yaya, ni zan fita akwai kayan data aikeni zan kai mata"
"Toh shikenan sai ka dawo"
Dawanan Sadik ya fice, bafi 10 mins ba sai ga Hajiya nan ta sauko, tazo ta samu wuri ta zauna, cike da girmamawa Hassan ya dawo kan carpet ya soma gaisheta, fuskarta babu yabo babu fallasa ta ansa, hakuri ya shiga badawa yana rokonta data yi hakuri ta yafe masa ta sauko daga wanan dogon fushin data dauka dashi, bazai iya jure fushinta a gareshi, amincewarta da yardarta yafi komai muhimanci a gareshi yanzu, bata dai ce dashi komai ba har ya gama magiyan ya tashi ya tafi, kwana uku Hassan ya jera yana bin kafa yana bada hakuri, a rana na ukun ne ma ya samu ta dan sauko sosai tayi mishi magana tace toh taji ya kawo mata Hibban rana Sunday ta ganta amma hakan bawai yana nufin tayi accepting bane bafa, kawai dai ya kawota gida ta ganta, ai kuwa murna a cikin Hassan kamar me ya shiga yi mata godiya na sauraronshi datayi yace Insha Allah zasu zo gabadayansu harda Faheema, tace toh sai sunzo, da farin ciki ya karasa gida a ranar.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...