Chapter 98

1.3K 85 1
                                    

Hibba

Weekend muka shirya komawa gida, Hassan yazo yayi picking dinmu, kamar kar mu tafi, Hajiya duk jikinta yayi sanyi tace ko zata bimu ne don already mun rigada mun gama sabawa da juna, su Anty Zaliha dai suna nan tukuna, ina jin sai bayan bikinsu Jamal zata wuce.

Tun kafun mu bar gidan Hassan duk ya kanainayeni, every slight opportunity ya samu sai yazo kusa dani ko kuma ya janyoni jikinsa, a raina nace daka daiana wanan rawar jikin, tunda already burinka ya cika, gida zamu koma, tun yana yi Hajiya na kau da kai har tazo tana ta'be baki. Kafun mu wuce gida sai da muka biya muka danyi siyayan gida da abubuwan da Faheema zata bukata na komawa school. Komai da komai muka siya bayan mun gama muka wuce gida.

Yau kwanan mu uku kenan da komawa gida, komai na tafiya normal. Faheema anyi resuming school, driver ke kaita yana dawowa da ita, harta islamiya, idan ta dawo tare muke homework da ita, kullum sai ta tuna mun maganar birthday dinta da kuma irin cake din da take so a mata, da party packs da zata bawa classmates dinta nace toh shikenan princess, duk abunda kikeso za'a miki zan sanar da daddy, bangaren mahaifinta kuma tunda na rigada na gano sirrin abincinsa nasa Baraka a gaba tayi mun bayani yanda tsarin girkin yake duk ta nuna mun, haka zamu shiga kitchen da ita muyita faman girke girke da ita tunda gidan kayan abinci birjik babu abunda zaka nema karasa, yauma kamar ko wace rana mun shiga kitchen mun dan' dafa abunda za'a ci a gida, Hassan na dafa mishi vegetable da pasta salad da kuma grilled chicken da coconut juice wanda purely kwakwa ne na markada banyi masa mix da komai ba, ko sugar bansa ba illa flavour, na jera akan table, muna gamawa na haura sama na yiwa Faheema wanka nayi serving dinta dinner taci, tana gama cin abincin ba jima ba ta gyangyada bacci. Ni kuma na karasa bayi naje nayi wanka na fito na shirya cikin doguwar riga blue mai hannu armless, na dauko hula nasa a kaina, turare na bida jikina ko wani lungu da saku sa'anan na debo turaren wutan da Hajiya ta bani na hura cikin burner, naje nasa a parlourn kasa, before you know it gidan ya bibiye da kamshi, sai dana tabbatar da ko ina a kasa ya dauka tukuna na haura sama da'kunan mu duk na bibiye da turaren, ina gama turarawa na hau gado gefen Faheema na kwanta na janyo wayata na kirashi yace mun gashi nan zai karaso gida, nace mishi toh. Sanyi AC na dan kara na janyo bargo na lulubemu sa'anan na fara buga game a wayata. Before you know it bacci nima yayi awon gaba dani.

Jin saukar hannu a gefen fuskata ana shafa a hankali ya farkar dani, na bude idanuna a hankali suka sauka kan kyakyawar fuskarsa, murmushi yake yana kallona, mikewa nayi ina kokarin matse baccin daga idona "ka dawo"

"Yes love..."

Na soma bin jikinsa da kallo naga har yayi wanka ya canza cikin farar riga tshirt da dogon wando dark blue.

"Yaushe ka shigo?"

"ban jima da shigowa ba, sorry I stayed late, ayuka ne suka rike ni"

"Ba komai Sannu da zuwa my love, nasan you must be tired and hungry muje na zuba maka abinci kaci" na fada ina mikewa, ban jira naji me zai ce ba na kamo hannunsa don nasan ina bari yanzun zai ce mun yaci abinci ni kuma gaskiya I won't take that, bai ce komai ba a hankali naga ya soma bin jikina da kallo, musamman kirjina don gown din dana sa yanada budaden gaba, ina rike da hannunsa na karasa na dauko gyale na zira a kaina sa'anan na juyo ina dubansa "Na kawo maka daki ko kuma zaka ci a dining?"

Shiru yayi yana dubana da murmushi a gefen bakinsa ganin yanda naci serious yace "toh shikenan bring it to my room"

Murmushi na sakar masa nace "alright tam ina zuwa"

Tare muka fito ina jin yanda idanunsa suke yawo akaina, dining na karasa naje na kwaso cooler abinci da plates, ganin kayan sunyi mun yawa a hannu yazo ya karbi cooler a hannuna muka karasa ciki tare, akan carpet na zuba plates din na sake fita naje na dauko jug din coconut juice dana ha'da da cups nazo na jera masa a gaba, a hankali na soma zuba mishi pasta salad da grilled chicken na zuba mishi coconut juice din, zan koma na zauna a gefe ya janyo hannuna ya zaunar dani bisa laps dinsa ha'de da janyo wata katuwar leda ya miko mun "this is for you"

❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI) Where stories live. Discover now