Hassan
Rintsa idanunsa yayi yana fitar da numfashi, zuciyarshi na bugawa da sauri sauri, gabadaya tunaninsa a hargitse yake, wani irin yawu ya hadiye kamar wanda aka ta'aba, ya shiga zarya a office din yana tambayar kansa meyasa ya bari ta shigo, yasan tun a hanya daya hadu da ita yaji yanda jikinsa yayi reacting yasan there'll be trouble. Bai ta'ba jin hakan ya sameshi ba, sai akanta.
Sake rintsa idanunsa yayi yana kokarin kawar da fuskarta da surar jikinta da'ga kwakwalwarsa, tabbass yarinyar tanada kyau babu karya but it's not as if she's the most beautiful girl daya ta'ba gani a rayuwarsa, yasha haduwa da mata iri iri daban daban, ko Afrah matarsa bata kamo ba, she's not this classic beauty, she's just Hibba Abdullahi, yarinyar da Allah kadai yasan inda ta fito, there's just something about her daya ji bazai iya hakura da ita ba har sai ya sameta, shiyasa yayi mata tayin wanan contract din, ta zama tashi sai yanda yaso yi da ita, amma as expected yasan da wuya ta yarda, yasan ba irin wanan matan bane, daga ganinta ma namiji ma bai ta'ba kusantarta ba, yarinya ce karama sosai, batada wayon da zata iya dashi.
Kokarin jan numfashi yayi ya fesar yana kokarin controlling mazankatarsa daya ya motsa, soft skin din fuskarta, da siraren lips dinta, kamar karya daina ta'bawa a lokacin, dabadin yace ta bar masa office ba da Allah kadai yasan mezai faru. Shi dai yasan bazai ta'ba mata komai ba tare da amincewarta ba, bazai ta'ba iya raping mace ba, amma yasan he wants her kuma he's going to have her, all to himself.
Fitowa yayi daga office, ya haura sama zuwa part dinsa yaje yayi wanka, yayi sallah ya canza kaya zuwa, casual jeans da bakr tshirt ya sauko zuwa parlourn kasa ya tadda Faheema da Maryam suna zaune sai faman daaga take da Faheema akan taci abinci taki,
"C'mon Faheema" yaji Maryam tana fa'din "ta tafi kuma ba dawowa zatayi ba, she's not your friend, now eat your food".
Banza Faheema tayi da ita, Hassan na ganin haka ya karaso cikin sauri yazo ya zaune a gefenta "what's the matter darling?"
A hankali Faheema ta da'go tana dubansa, idanunta cike da ruwan hawaye, nan take yaji zuciyarsa ta masa wani irin nauyi, sam baya san ya ganta cikin irin wanan yanayin.
"Daddy...Anty Hibba ta tafi, k..kuma ta mun alkawari zata zo muci abinci tare".
Saurin ja da baya yayi cike da mamaki yace "Hibba...kin ha'du da Hibba?"
gyada masa kai tayi "ta fa'di cikin garden ta ba'ta jikinta da ta'bo, shine na taimaka mata.
Nan take Hassan ya fahimta, yasan yar'sa Faheema da bala'in tausayi, kuma duk wanda ta gani cikin nema yana bukatan taimako zata taimaka masa, wala ga mutum ko dabba. Gaskiya mana ya gan Hibba ta fito hanyar guest bathroom, ashe Faheema ce ta kaita. Bai san sanda ya saki murmushi ba, yana yawo da hannunsa cikin lalausar sumar kansa daya tuno haduwarsu da kuma zaman da sukayi a office. Maryam ce ta ba'ta fuska ganin murmushin dayake, Faheema kuma ta cigaba da dubansa muryanta na rawa tace
"Daddy zata dawo? Meyasa ta gudu haka?"
Cak Hassan ya tsya yaji kirjinsa na harbawa, taya zai fara yiwa yar'sa bayanin abunda yasa Hibba ta gudu? Taya zai fara mata bayanin cewa mahaifinta is one of the most dangerous business men, and yana sha'awar wata yar mistila, kucakar yarinya irin ta?
Gyaran murya yayi yace "maybe tanada inda zata ne".
"Toh zata dawo daddy?" Ta tambaya tana ruko hannunsa cike da hope cikin kwayar idanunta, "Dan Allah daddy kaje kace ta dawo"
Hassan tsintar kansa yayi da kasa ce mata a'a don a rayuwarsa indai akan farin cikin Faheema ne zai iya yin komai don haka ya sakar mata murmushi ha'de da shafar kanta "toh shikenan, zanje na dubota, in fact I'm going to do that right now.
Saurin mikewa Faheema tayi ta rungumeshi ha'de da kai masa kiss a gefen kumatu "nagode Daddy". Fuskarta cike da Annuri, daga gefen idanunsa Hassan yana iya hango yanda Maryam tayi kicin kicin da fuska kamar batayi ammana da abunda ke faruwa ba, kasa hakura yayi ya juyo yana tambayarta
"What's the matter Maryam?"
Shiru tayi kmar tana nazari daga bisani tace "I see no reason why za'a bi bayanta, she left on her own"
Da'ga gira Hassan yayi da alamun tambaya a fuskarsa jin abunda tace, bata tsaya nan ba ta cigaba da fad'in" kuma fa babu wanda yasan inda ta fito, bansan ma meyasa John ya bude mata gate ta shigo ba".
"Ni nacewa John ya bude mata Maryam".
Mamaki ne ya cikata "kai kace? But why?"
Ba'ta fuska Hassan yayi ya fa'da cikin kakausar murya "because she's my business"
Faheema ce ta katse musu zancen da sukeyi tace "Dan Allah Daddy kaje ka nemota, she's my friend".
Dariya Hassan ya sake yace "harta zama kawarki kenan"
"she's not your friend Faheema! Yarinyar nan ba kawar ki bace! Bakiga yanda take ba? she's a mess..." Maryam ta fa'da tana kokarin kamo Faheema, Faheema taki ta kwace taje ta fa'da jikin mahaifinta tana fashewa da kuka, cikin sauri Hassn ya kamota nan take ransa ya ba'ce ganin yanda Maryam tasa yar'sa kuka "karki kuskura ki sake gaya mata irin wanan maganar, it's not in your place to tell her who to be friends with, remember that!" Ya fada cikin kakausan murya. Hakuri ta shiga bashi tana fa'din bazata sake ba
Faheema ta da'go cikin sheshekar kuka
tace "so...Anty Hibba zata iya zama kawata?""Of course sweetheart". ya fa'da yana share mata hawaye.
"Toh kaje ka nemota Daddy, inaso muci dinner tare kuma ina so na nuna mata books dina da kayan wasana, zamuyi wasa tare".
Dariya Hassan ya sake, cike da sha'awan yarsa, she's just too cute.
"Karki damu princess... yanzu zanje na taho miki da ita.
Hannu tasa ta soma share hawayenta cike da farin ciki, Hassan ya da'an lakuto kumatunta yace "now promise me you'll be a good girl".
Saurin gyada masa kai tayi tace "na dau maka alkawari Daddy"
"Toh shikenan sai na dawo" ya fada yana shafar kanta.
"Sai ka dawo daddy".
Haka ya shirya ya fita neman Hibba don ya dawo da ita gidansa.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomansaHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...