Hibba
Sanyin da yake faman ratsa jikina ne ya farkar dani, na bude idanuna a hankali naga ni kadai ce a dakin, a hankali nakai hannu gefena ina shafawa har yanzu da dumi wajen kamar an kwanta, a hankali na motsa ina kokarin tattaro bargon zuwa jikina, wani irin sanyayen kamshi ne yake tashi daga jikin bargon, irin kamshin jikin Hassan. A hankali na lumshe idanuna na bude, ina tunanin kilan ya shigo kenan lokacin ina bacci, toh meyasa bai jira na farka ba? Rabona dana sashi a ido tun jiya, kuma nayi missing dinsa sosai, I miss everything about him, na tuno kalamansa gareni inda yake fa'da mun yana sona, har yanzu jin abun nake kamar a mafarki, wai ni Hassan yakeso, ni Hibba?
Wani irin murmushi ne ya kubuce mun ina jin wani irin sanyin dadi a raina, ban ta'ba jin farin ciki irin wanda nake ciki ba a yanzu daga jiya zuwa yau na tsinci kaina cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, yanda nake jin Hassan a raina, ji nake zan iya yin komai akansa, ina sonsa sosai har cikin raina bansan yanda zan missalta ba kuma ina kara godewa Allah daya ha'dani da mutum irinsa cikin rayuwa.
Ina cikin wanan tunanin aka turo kofa, wata sabuwar nurse ce ta shigo, sanye cikin farin uniform dinsu da baby hijab, bakar fata ce da dan murmushi a fuskarta ta karaso tana gaisheni tana tambayata ya jiki, nima murmushin na sakar mata nace da sauki, tace dani sunanta Fatima tazo a madadin nurse Priya, na tambayeta ina priya tace mun ta samu emergency call a gida amma zuwa anjima zatayi resuming duty nace da ita toh. Karasowa tayi wajen gadon tana duba temperature dina da abun gwaji, sa'anan ta soma dan rubuce rubucenta, ta tambayeni ya nakeji yanzu nace mata da sauki, tace ko zan iya cin abinci yanzu a kawo mun, nace da ita eh amma ba mai nauyi ba tace okay. Tana gama gwaje gwajenta da rubuce rubencta tace zuwa karfe tara Dr Munnir zai shigo yazo ya dubani, nace da ita toh. Blood pressure nane last abun data duba sa'anan ta fice taje ta ha'do mun shayi mai zafi ta kawo mun, godiya na mata har ta juya zata fita na kira sunanta nace "nurse Fatima..."
A hankali ta juyo tana dubana tace "na'am?"
"Dan Allah zan iya tambayarki wani abu?"
"Yes sure, go ahead"
"Uhmm... nace ko kinga wani mutumi fari, dogo mai kwantaciyar suma ya bar dakin nan?"
Dariya naga Fatima ta sake tace "kina nufin mijinki? Tabbas na ganshi ya fita da safen nan"
Sunkuyar da kaina kasa nayi ina tunanin yanda suke dangata Hassan da matsayin miji gareni, she's not the first person da take fa'din haka, har zan bude baki nace mata ba mijina bane naji tace "gaskiya kinada sa'a, samun miji kamarsa sai an bincika, ga kyau ga komai duk ya tara, uwa uba jibi yanda yake sonki yake nuna miki kulawa, he takes very good care of you, you're one luck girl wlh" ta karasa maganar tana kashe mun ido da'ya.
Murmushi na sake na kasa furta komai, don wani irin kunya ne naji ya lulubeni a wajen, dariya ta dan sake sa'anan tace mun nasha tea din kafun azo a mun allura a debi jinina nace da ita toh, nayi mata godiya ta fice.
Tana fita na sauko daga kan gadon na karasa bayi a hankali nake bi da komai, naje na gyara jikina sa'anan na fito, ba jima ba sai ga lab tech din ya shigo yazo ya debi jinina for routine testing, daman kusan kullum zai sunzo sun debi jinina, yana gamawa ya fice ni kuwa na jawo kofin shayin na soma kurba a hankali ina sha. Sosai nasha tea din na ajiye cup din a gefe.
Zuwa karfe tara na safiyan sai ga Dr Munnir din ya shigo, mutumin da ganisa yana late 40's dinsa ya karaso tare da wasu young doctors suna biye dashi, daga ganinsu kamar medical students ne, sosai Dr Munnir ya ba'ta lokacinsa wajen dubani, raunukan dake fuskata duk yabi yana examining dinsu sa'anan naga ya gangoro kasan marata nan ma sai daya duduba da kyau, yayi mun wasu yan tambayoyi, nidai kawai bashi ansa nake don bansan meyasa yake mun wanenan tambayoyin ba.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...