Bangarensu Sadik kuwa yana isa gida Hajiya ta soma tambayarshi dalilin daya sa ya jima, nan ya kwashi komai ya gaya mata, sallati Hajiya tasa tana fad'in "Afrah din?""Wlh Hajiya ina gaya miki, kawai kwatsam na shiga gidan nan na ganta, ban san ya akayi ta samu damar shigowa ba, daba din na shiga tsakani kinsan shiri takeyi tayi fada da Hibba, wai zata fitar da ita daga gidan"
"What?! Toh Karyanta tasha karya shegiya yar iska la'ananiya, ina wayata, miko mun wayata yanzun nan suga cika aiki, wato har tanada karfin hali da zata sa kafa ta shiga wanan gidan bayan duk wahalar data sa da'ana ya fuskanta da irin bakin ciki da mawuyacin halin data jefa shi bai isheta ba ta sake dawowa, toh ubanta zata ci, miko mun wayata Sadik!"
Tashi yayi yaje ya dauko mata wayarta ya kawo mata "me zakiyi Hajiya?"
"Kiran uwarta da ubanta zanyi don sune suke daure mata gindi, idan bana dau' kwakwaren mataki akansu bazasu shafawa wanan familyn lafiya ba"
Karban wayar tayi daga hannun Sadik ta soma dialling number maman Afrah, tana dagawa bata ma bari ta numfasa ba to soma attacking dinta
"Mallama kina jina ko, na kira ne akan ki jawa yarki kunne tafita daga harkan da'na da family dinsa, idan ma kece kike zugata kike daure mata gindi tayi duk abunda taga dama toh ki garga'deta don ni bazanyi tolerating wanan haukan kusa da familyna ba, tayi na farko kuma tayi na karshe kenan"
"Haba Hajiya ya za'ayi daga kira baki ma bari mun gaisa ba zaki hau mun bambami a waya"
"Gaisuwarki na banza da wofi me zanyi da gaisuwarki, nidai na gaya miki kija mata kunne, da'na ba saran yinta bane, ha'da iri da irinku ko masifa da bala'i, har yau bazan daina bakin cikin ha'da zuria da irinku, mutanen banza kawai mutanen wofi"
Bata ma jira taji me zata ce ba ta katse ta soma kiran Hassan shima ta soma mishi bala'i a waya, tana tambayarsa dalilin da zai sa yana biyewa Afrah har ta samu daman shigowa gidansa, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, hakuri ya shiga bata yace wlh shima bada saninshi ta shigo ba amma he's going to handle it insha Allah hakan bazata kara faruwa ba. cigaba da mishi fa'dan tayi daga karshe tace ya bawa Hibba waya, nan ta shiga bata baki akan tayi hakuri karta sa komai a ranta, insha Allah duk wani mugun nufi data zo dashi akanta zai kife.
Mahaifiyar Afrah Hajiya Rabi, suna gama waya da Hajiya ta mike ranta a ba'ce ta haura sama zuwa dakin Afrah ta soma kwankwsawa kofa sai faman balai take tana zage zage, ai kuwa bugun duniya Afrah taki budewa, karshenta spare key din dakin taje ta dauko tasa ta bude, nan ta ta'da yar nata jagap, sallati tasa cikin sauri ta karaso ta hau gadon ta soma jijigata amma inaa, a hankali idanunta suka sauka kan abubuwan shaye shayen dake gefen gado, hankalinta yayi bala'in tashi, duk tabi ta rude, jikinta ne ya hau rawa, gashi Alhaji ya kusan dawowa, idan ya dawo ya tadda Afrah cikin wanan yanayin kashinsu ya bushe a gidan, cikin sauri ta sauko daga gadon taje ta dauko waya tasoma dialing number Family doctor dinsu, tace yazo gida yanzu yanzun nan tana son ganinshi Afrah babu lafiya, within 10 mins sai gashi nan ya karaso, tana hawaye tace yaje ya duba state din da yar'ta ke ciki, karasawa yayi ya soma duba Afrah nan take ya gano drugs ne, cikin hikima ya soma kokarin resuscitating dinta, blood presssure dinta yayi low sosai, hankalinsa shima ya tashi sosai ya fara tambayar Hajiya tana ina ta bari Afrah ta yiwa jikinta wanan aika aikan? Kuka Hajiya ta fashe dashi tana fa'din bata san ya akayi hakan ta faru ba, kulle kanta a daki tayi itama da kyar tazo ta bu'de, dan Allah ya taimaka ta farfado kafun Alhaji ya dawo, doctor ya girgiza kai yace ai yanzu halin da take ciki it will hard for her to wake up, sai dai yayi mata allura da zaisa drugs din suyi wearing off a hankali daga bloodstream dinta. Hajiya tana kuka tace yayi duk abunda zaiyi ya ceto mata yar'ta, ita kenan ta rage mata.
Doctor dai ya samu yayi duk abunda zaiyi amma har zuwa lokacin bata farfado ba, yace a barta ta huta she'll be awake zuwa gobe, Hajiya tace toh tayi mishi godiya sosai tace dan Allah koda wasa karya bari Alhaji yasan halin da Afrah take ciki, yace karta damu bazai sanar dashi ba amma itama dan Allah tasa ido sosai akanta, at the rate da take taking waenan drugs din, her immune system is already weak komai zai iya faruwa, tace insha Allah.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...