Hassan
Driving yakeyi amma gabadaya tunaninsa baya jikinsa yana kan gimbiyarsa, yau kwana kusan biyar kenan bai samu ya daura idanunsa akanta ba, ayuka sun masa yawa yana so ya samu ya kamala kafun ya koma Lagos, don ko can dinma ayuka ne ke jiransa. Ko na second da'ya bata ta'ba barin kwakwalwarsa ba, da zuciyarsa dama gangan jikinsa gabadaya kara dilmiya yake da tunaninta da kewarta, yanzu yayi realising Hibba daban ce, he has come across so many ladies amma bai ta'ba haduwa da macen daya ji faral daya ta tafi da imaninsa haka ba,
ga sha'awarta da kullum kara bunkasa yake a sansar jikinsa, idan ya rintse idanunsa ita yake gani, har cikin mafarkinsa kwo masa farmaki takeyi, da farko bai taba tunanin zaiyi zurfi haka ba amma yanzu he's already in, a yanzu halin da yake ciki bai ji kuma bai gani sai ita, bai jin zai iya rike kansa when next ya ganta, ji yayi zai iya yin komai don ya sameta, zai iya yin komai don yaga ya sadata cikin farin ciki, ya yanke hukuncin zaiyi wanan auren sirrin da ita, ya samu ya kashe wanan wutan sha'awar da yake cinsa akanta, sai ya rabu da ita a sirrincen bayan adadin da aka dauka ya isa, yasan idan ya sameta sau daya ma ya isheshi, komai zai warware masa, ko AK ma bai gaya masa plans dinsa, yanata faman tunanin yana sake saken yanda zai bullo wa lamarin.Yana isa straight office dinsa ya wuce, ba tare da ba'ta lokaci ba ya kira Iman Sani tun a waya ya soma shaida masa bukatarsa, Imam Sani yace bamu matsala zai zo tare da Saleh wani mallami ne shima an unguwarsu dake Kubuwa, Imam Sani ya kasance datijon mallami wanda Hassan yake mutuntawa sosai, yayi aikin gardener a gidansu Hassan tun yana karami, gabadayansu yan gidan sun taso sunga Imam Sani yana aiki a gidan, kuma duk cikinsu yafi shakuwa da Hassan, rai da rai zakaga suna tare, har tsufa yazowa Imam Sani mahaifinsu Hassan ya sallameshi yace yaje gida ya huta, ya bashi kudi masu tsoka, toh abu dai na mai iyali dayawa kuma babu wani abun da aka dogara dashi yasa Hassan yayi mishi tayin gidan gonakinsa ya rike masa, Hassan yana mugun tausayawa Iman Sani, ya dauki mutumin tamkar dan'uwansa, shima Imam Sani yana son Hassan sosai don duk cikin yaran Alhaji yafi shakuwa dashi saboda saukin kansa, ga taimako da sanin ya kamata, abun hannunsa bai rufe masa ido sam yanada kyauta sosai, yaran Imam Sani takwas a duniya yanada yara samari duk babu wanda ya karasa karatunsa shiyasa Hassan ya dauki nauyin uku ya sasu a Jami'a, guda biyu kuma ya daurasu kan aikin da mahaifin nasu keyi suna taimaka masa, kuma dayake yaran masu kwazon nema ne, komai na tafiya daidai ciki har suke samu suna kula da mahaifin nasu, Imam Sani cike da barin jiki yazo ya sami Hassan a office, Hassan ya soma shaida masa gashi gashi yanda yakeson abubuwa su kasance, Imam sani yace babu matsala, ba tare da ba'ta lokaci Hassan yasa aka kira masa Ammar,Ammar yazo ya tadda su, Hassan ya shaida masa, ai sai da gaban Ammar ya fadi, dukda dai shine yayi suggesting amma hakan bai hana zuciyarsa harbawa ba, hankalinsa yakai kololuwar tashi, me yake shirin aikatawa game da yayarsa? anya he's doing the right thing kuwa? Kirjinsa sai faman harbawa yake amma daya tuno halin da yayar nasa zata shiga dakuma irin rayuwar da zata dinga yi a hannunsa yaga gwanda kawai ayi hakan, ita ce kadai mafita ta hanyar kare mata mutuncinta.
A gabansa yana ji yana gani Imam Sani ya daura auren yayarsa da Hassan bisa sadaki dubu dari biyu aka shafa Fatiha, sai da kwalla suka zubowa Ammar don daga Allah sai shi sai Hassan suka san me auren nan yake nufi, can kasan ransa yana addu'ar yafiya daga wurin ubangiji da kuma addu'ar Allah yasa Hibba ta samu wuri cikin zuciyarta ta yafe masa wanan aika aika da yayi game da rayuwarta ba tare da saninta ba.
Bayan Hassan ya sallami Imam Sani, Ammar yace sam bazai iya karban wanan kudin a matsayin sadakin yayarsa ba, bayan ga bashin da yake binsu a kasa, Hassan bai saurarshi ba yace ya dauki wanan kudin ya sawa Hibba a account nan gaba zai musu amfani koda sun koma Maiduguri, kuma karya kuskura ya sanar da ita komai. Cike da sanyin jiki Ammar yace toh shikenan, yace da Hassan ga amanar yayarsa nan, ita kadai ta rage masa dan Allah ya kula da ita har zuwa lokacin da iya adadin zai cika su rabu, yana magana yana zubda hawaye, Hassan ya tsinta kanshi da tausaya musu, bai ce dashi komai ba ya sallameshi yace ya tafi sai ya sake nemansa, haka Ammar ya juya ya tafi cike da sanyin jiki, bayan sun watse tukuna Hassan ya soma tunanin kala kala, sai yanzu yake realising abubuwa, ya auri Hibba ba tare da saninta ba, yanzu ya zai bullo mata don yasan bazata ta'ba yarda ba tunda gashi nan a rubuce no sex a contract dinsu, kuma idan yace zai sadu da ita ta dole yasan zata tsaneshi, tsanar ma dayafi wanda take yiwa Kawunsu Abu, kuma yasan zuciyarsa bazata iya juriyar Hibba ta tsaneshi ko ta juya masa baya ba, ya soma tunani yana sa'ke sake yanda zaiyi ya bullo mata.
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...