Hassan
By the time daya dawo washe gari da yamma ya shigo dakin ya sameta tana bacci hankalinta kwance, ya karaso ya tsaye a gefen gadonta yana kare mata kallo, sosai ya kura mata ido yana binta da kallo da yanda raunukan nan suka ba'ta mata kyawawar fuskarta, wani irin bakin ciki yakeji ya ratsa shi, sam bai kaunar ya bude idanu yaga waenan ciwon a fuskarta, he wants those marks gone as soon as possible don anytime ya gani yana tuna masa da abunda ya faru da kuma abunda wanan dan iskan yayi mata, wani irin tafarfasa yaji zuciyarsa ya soma masa nan take a wajen ya sake daukan wa kansa alkawarin insha Allah bazai sake barin wani abu makamancin haka ya faru da Hibbansa ba, bazai sake irin wanan sakacin ba, zai tsaya mata, he'll stand by her, he's going to protect and cherish her at all cost.
A yanzu haka da take kwance tayi zurfi cikin baccinta yasan it won't be long kafun ta fara waenan mafarke mafarken, tunda aka kwantar da ita kusan kullum sai tayi, har yanzu trauma din abunda ya faru da ita yana tare da ita, ta dinga kuka tana ihu cikin baccinta kenan tana rokon Kawu Abu daya rabu da ita, abun ba karamin konawa Hassan zuciya yake ba, his heart breaks anytime ya ganta cikin wanan yanayin, da da hali da zai sa ta daina yin irin waenan munanan nightmares da sai yayi, ko doctors ma da sukayi magana sunce zata daina she just needs constant rest and peace of mind, anything da zai sa hankalinta ya da'ga, they should avoid it, for the sake of her and her baby.
A hankali ya matso da Kujeran dake gefen gadon ya zauna dab da ita yana fuskantarta, yakai hannunsa bisa fuskarta ya soma shafar ta'bon ciwon dake fuskarta a hankali yana murmushi yana tuno zancensu na jiya, ya tuno kalamansa gareta da irin tsantsan farin cikin data nuna, bai ta'ba ganinta cikin farin ciki kamar na jiya, ya tuno kalamanta itama garesa yanda ta fada masa itama tana sonsa, wani irin farin ciki ne yaji ya lulubeshi kamar a lokacin ta furta, a hankali ya sunkuya yakai lips dinsa bisa goshinta ya mana mata kiss ha'de da fa'din "I love you"
Kamar ta jishi a hankali yaga ta motsa cikin baccin nata tana dan juyi sa'anan ta cigaba da baccin, murmushi ya sakar yana cigaba da kallonta yana jin wani irin sanyi a ransa. An wuce stage din farko, yanzu yana jiran sai ta gama samun lafiya tukuna sun koma gida zai fara mata bayanin yanda abubuwa suke ciki a tsakaninsu, don yasan eventually he has to open up, sai dai bai san yanda zai bullo mata ba, bai san yanda zata dauki maganar ba, he's scared of her reaction shiyasa ya sanar da nurses din koda wasa karsu sanar da ita tana dauke da ciki, sai komai ya lafa tukuna. Ba jima ba ya mike ya koma kan sofa dake can gefe ya mike ha'de da ciro wayarsa ya soma dadanwa yana replying wasu emails da aka turo masa, sai zuwa sha biyun dare tukuna ya ajiye wayar, zuwa lokacin ya gaji sosai, ga stress daya masa katutu a jiki, tsawon kwana ukun nan sam baya samun isashen bacci, in fact rabonsa daya samu bacci tun ba'tanta, har ya soma kokarin rufe idanunsa kenan yaji ta fara motsi kan gadon, kafun ma ya motsa yaji ta sake wani ihu a guje ya mike ya karasa wajen gadon ya sameta tana birgima kan gadon, hawaye na zuba mata still idanunta a lumshe tana bacci sai faman sumbatu take tana fa'din
"Wayyo Allahna... Hassan...Ammar...kuzo ku ceceni, Kawu Abu zai kasheni, kuzo ku taimakeni...zai kasheni.."
Kuka take sosai tana mitsika bedsheets din tana birgima, hankalinsa a mugun mugun tashe ya karasa ya tattarota zuwa jikinsa ya rungumeta tsam a jikinsa ya shiga ba'ta hakuri, yana rarashinta akan ta daina kuka gashi nan tare da ita, sosai take kukan nata shi kuwa yanata aikin rarashi, zuciyarsa kamar zata buga ta fito tsabar tashin hankalin daya tsinci kansa cikin daren nan, sun kasance a hakan har kusan karfe ukun dare tukuna ya samu kukan nata ya lafa, ta kwanta lamo a jikinsa tana ajiyar numfashi, duk motsin da zaiyi sai tayi kamar zata farka, da kyar ya samu ya gyara musu kwanciya akan gadon still tana makale a jikinsa, Hassan yayi shiru ya afka duniyar tunani yana jin yanda zuciyarsa ke masa wani irin nauyi, he can't bear to see her in such pains, it breaks his heart all the time. Bai rintsa ba idanunsa na kanta har asuba, aka kira sallah ya soma kokarin mikewa, ya kura mata ido yana kallon yanda take baccinta hankalinta kwance kamar ba ita ba, wani irin tausayinta ne yake ratsa duk ilahirin jikinsa ya kai mata kiss a goshi ya kwantar da ita a gefensa sa'anan ya soma kokarin saukowa a hankali ta yanda bazata farka ba, yana cikin haka yaji anyi knocking an turo kofar an shigo, Priya ce ta shigo hannunta dauke da tray din magunguna da drip, tana ganinsa ta rinsina ta gaisheshi cike da girmamawa, a hankali ya mike daga kan gadon yana gyara zaman kayan jikinsa da suke mitsike tsabar cakumar da Hibba tayi masa ya juyo yana duban Priya ya ansa gaisuwarta yace "morning"
YOU ARE READING
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)
RomanceHassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi n...